Sashe 97
Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
shiru hajiya umma tayi tana nisawa cikin tunanin meke faruwa ga yarima youssouf haka mai girma da yasa take jin damuwa har a cikin amon muryar sa , ?? Jikin ta yana bata wani abu ya faru ko yana shirin faruwa gare ta ita kan ta kyakkyawa ko kuma akasin sa , koma menene tasan yana da alaƙa da youssouf ɗin ta domin akan sa kaɗai wannan soyayya mai girma take bayyana tasirin ta a kaf cikin ƴaƴan ta !
   Cikin satin kamar yadda tafeeda yace ya gama shirinsa tsaf , yayiwa nigeria tsinke ,
Bai wani sha wahala ba yayi wa kan sa jagora zuwa garin maiduguri bayan da jirgi ya sauke shi a garin abuja , " sai da ya samarwa kan sa masauki international hotel ya huta , washegari ya bada kuɗi aka sayo masa layin nigeria ya cire layukan sa na niger ya sanya ns Nigeria , hajiya umma ya fara ƙira ya sanar mata da samuwar sabon layin nasa da zasu dunga magana ta hanyar sa sannan , ya kashe ya fara laluben number biyamuradi youssouf wanda bai kai ga sanin isowar Tafeeda nigeria ba rabon da suyi waya ma sun tasamma kwanaki goma abun da kusan hakan bai taɓa faruwa ba a tsakanin su sai fa yanzu da biyamuradin yake cikin wani hali na tsantsar damuwa tare da ƙarin zafafawa kan sa aiki da yayi ta hanyar rashin hutu ba dare ba rana yana zabarin rundunar dake ƙarƙashin sa suna matsa ƙaimi wurin farautar ƴan tawayen Boko haram ," duk a ƙoƙarin sa na son yakice tunanin damuwar sa daga cikin ran sa da kuma kusantowar lokacin da aka ɗibar ma su na kammala aikin su da nigeria yana gaf da ƙarewa tsakanin kwanaki arba'in masu zuwa nan gaba zasu cika shekara da aka ɗibar musu za kuma su koma ƙasar su ta haihuwa ,"......!
Assalamu Alaykum kowa da kowa !
ina miƙa sakon gaisuwa ta ga masu karatu ,tare da fatan Alheri !
ku sani naji daɗi na kuma yaba muku a kan yadda kuka bayyana ra'ayoyin ku kan shafin da ya gabata ," ƙwarai ƙwarai na gode muku ," Zan kuma yi ƙoƙari ganin nayi amfani da wasu daga cikin shawarwarin ku/ƙorafin da kuka yi , da fatan nima zaku bani dama ku cigaba da bibiya ta ba tare da kun yi saurin yanke hukunci ba har ku ga inda na cimma matsaya da kuma manufa ta da inda labarin ya dosa ,
Da fatan zaku samu wasu ƴan dakiƙai daga cikin lokutan ku kuyi addu'a ga ƴan gudun hijira da igiyar rayuwa ta chukurkuɗe musu take kuma jaan su tana haɗa su da manyan ƙaddarori duk a sanadin rabo su da bigiren su mahaifar , su garuruwan su da annabor boko haram tayi , suka tsinci kawunan su a cikin matsananciyar rayuwar da ta zarce ta su yakaka da falmata a tasku tare da wahalarwa , Annobar boko haram gaskiya ne kamar yadda wani sashi na daga cikin labarin nan yake gaskiya !
Ina matan da suke makancewa cikin so , ? tare da sarkarwa soyayya ragamar rayuwar su , har ta kai su ga aikata mummunan kuskuren da zasu wanzu suna danasani tare da nadama cikin rayuwa , Yakaka tace ahir kuma kul ! Ba kome da kake so kake samu ba ba kuma kowanne abunda kake so bane yake zama Alheri , Rayuwar da duk aka ɗaukaka soyayyar fiye da kome a cikin ta ba'a cika yin ƙarƙo tare da samun farin cikin rayuwa ba ,! Hannun ka mai sanda ne kuma Nasiha ce !
  Nagode !
 Af na manta
  Yakaka tace I Love y'all ta gutsuro muku kaɗan daga cikin irin son da take yiwa bature kam silum, " Ah to meye So ne fa ??? 😂
  [7/9, 4:42 PM] +234 803 559 8589: Fikra writers association .
MAFARI
( Hargitsin Rayuwa )
umm'muaz
28
Biyamuradi youssouf bai samu damar shigowa cikin garin maiduguri ba sai da Tafeedah ya samu kwanaki biyu a cikin garin yana dakon jiran sa ,"saboda yanayin aikin sa ,"
Kai tsaye hotel ɗin da tafeeda yayi masauƙi ya nufa , kasantuwa tsawon watannin da ya samu yana ɗan shigowa garin ya fara gane hanyar guraren da kafafun sa ke yawan zuwa ,"
Bayan sun gaisa cikin raha sosai irin ta aminan junan da suka shaƙu da juna , Tafeeda ya nisa yana kallon Youssouf ɗin tare da nazartar sa , ƙwarai ya fahimci har yanzu bai shirya sanar da shi damuwar sa ba , duba da yadda yayi ƙoƙari ya boye damuwar ta sa fiye da wancen haɗuwar tasu , cikin rashin sanin damuwar ɓaro-ɓaro ta bayyana kan ta a cikin ƙwarar idanun sa ,"
Kai tsaye Tafeeda ya doshi Youssouf da maganar da ta taso shi takanas daga ƙasar su ƙarƙashin umarnin hajiya umma , inda yake cewa
 Ban san ba ko rabuwar mu ta ƴan watanni ta sauya alaƙar mu da kai ba ɗan ouwa , ta yadda har ta kai ka shiga boye min wani babban lamari da ya shafi rayuwar ka wanda ya kai ga tsunduma ka cikin damuwar da hatta Hajiya umma ta shina ,
ita ma kuma damuwar ta shafe ta ta kuma sanya ta a firgici , ka riga ka san kome na daga yanayin gidan da munka taso cikin sa , ka san kou kai wanene , kasan yadda hajiya umma ke takatsantsan da du wani lamari naka ,
hakan ya sa hajiya umma ta titsiye ni tana son san sani game da abunda yake faruwa gare ka , na shaida mata ko ɗaya bani da sani game da halin da kake ciki nan , sai tayi gaugawar turo ni domun naji shin menene damuwar ka Yarima Youssouf ?
Shiru ne ya É—auki É—akin ,
A haƙiƙanin gaskiya Youssouf yana kunyar buɗe baki ya sanar da wani mahaluki laifin da ya aikata tsakanin sa da ubangijin sa , laifi mai girma kuma irin wannan , to amma hajiya umma ita wata halitta ce mai girma gare shi bazai so ba ko kusa shi ya zamto silar samar da damuwa ga ruhin ta , abun zai masa yawa ,"
To amma wanne hali zata shiga idan ta ji dalilin shiga damuwar sa ? Wane alfanu sanar da ita damuwar sa zai samar ? Idan ta ji laifin da ya aikata da har ta kai shi ga shiga halin da yake ciki ƙara mata damuwa zai yi daɗi da ciwon zuci ko kuwa ma hawan jini ," ! Kai anya ma kuwa zata yafe masa ??
Tunanin halin da zata iya shiga ciki kawai ya sanya gumi tsatsafo masa a goshi , hannun sa ya kai ya rufe fuskar sa da tafukan sa , ya goge gumin ,
Ɗan ouwa , nayi kuskure mai girma cikin rayuwa wanda giya ta zam sanadi , na haiƙewa ƴar mutane , nayi tarayya da ita har ta samu juna biyu , a yanzu haka mariƙiyar yarinyar ta kore ta ta shiga duniya .
ɗan ouwa ka faɗa min ya zan yi ina zan tahi na same ta ? Yaya zan yi na gyara kuskuren da na aikata , ɗiyar mutane zata zama kilaki sanadi na , yaya rayuwar ni nawa ɗiya mata zasu ƙarƙe ?? Yaya nawa ƙanne zasu samu kariya , tayaya zan katange iyalina ? ....
Kallon sa kawai Tafeeda yake idanun sa sun kaɗa jazir da ɗai bai taɓa jin zance mai munin wannan ba , ashe yarima bayan shan barasa har fyaɗe yake yiwa mata ? Har zina yake yi ? Har ɗa ya samar ta hanyar haram ? Anya anya Yarima Youssouf ya chanchanta ??
Miƙewa yayi ya soma haɗa kayan sa ," baya so ya cigaba da kallon sa , ganin sa a halin yanzu zai ɗarsa masa tsanar sa , zai rushe amincin da suka faro tun ƙuruciyar su ," yana so ya tafi , yana so yaje ya lallashi hajiya umma da tausasan kalamai domin ita ɗin a yanzu abar a tausayawa ce , da ɗai bazai yadda kunnuwan ta su ji waɗannan munanan laifukan da ɗan da ta ƙwallafawa rai ya aikata ba , ɗan da hatta shi da kan sa yaci albarkacin samun tsaftatatciyar tarbiya daga gareta sanadin raɓar Youssouf da yayi amma sai ga shi , ! Kai kaicho
Da sauri Youssouf ɗin ya miƙe yana riƙe hannun Tafeeda da yake harhaɗa ƴan abubuwan buƙatun sa cikin jaka ,
Warce hannun sa yayi da wani irin zafin nama
  Kar ka taɓa ni Youssouf , babu wata sauran Alaƙa a tsakanin mu , manzon Allah yace mu guji munanan abokai, mu mu'amalanci mutanen kirki ," kai baka chanchanta ba Youssouf
   Ƙwallar da ya kamata ta zubo tun watanni da suka gabata amma rashin samun damar kukan ya hana ta zubowa tare da taurin rai irin na soja gami da jin kai na jinin sarauta ita ce yau ta silalo ,
   A hankali ya zauna a bakin gadon , bai yi aune ba ya fara kuka shaɓe-shaɓe da hawaye kukan nadama kukan tsanar kai kukan neman mafita ,"
 Share shi Tafeeda yayi tare da cigaba da haɗa kayan sa tsaf ya ɗaura agogon sa gami da ɗaukar ƴar jakar sa na matafiya,
 Â
 Kallon Youssouf ɗin yayi ,
Zuciyar sa ta raunana , ganin hawayen sa abune da tun zamanin ƙuruciya rabon sa da gani , kai zai iya ƙirga yaushe da yaushe ya ga kukan Yarima Youssouf tun a ƙuruciyar su , to ɗan sarki ne , ɗan gata yarima , da kowa tattalin sa yake , a yau ya san cewa zuciyar sa ta luguiguita matuƙa da har ya kawo zubar hawayen sa a karon farko cikin shekarun girman su ,
  Ƙauna ta haƙiƙa irin ta shaƙiƙan aminai ta taso , ji yayi bazai iya tafiya ya bar shi ba ya zama dole ya tsaya su samar da mafita , kamar yadda suka saba tallafar junan su idan wata maysala ta riski ɗayan su kome girman ta ko ƙanƙanta,