← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 170 OF 269

Sashe 170

Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hannuwanta biyu ta sanya ta É—ago Mama , da wani irin yanayi ta matso da fuskar Mama daf da tata bayan ta É—aura ta a cinyar ta ,

Ƙure mata kallo take yi , cike da son ganin ta fiye da yadda take iya hango ta dusu-dusu a yanzu ,

Runtse ido tayi ta buÉ—e a hankali

'Mama
   Ta ƙira sunan ta, 

Dariya Mama tayi tana É—ora 'yan hannuwanta akan hannun Falmata da take tallafe da kumatun ta ,

Ta ga hasken haƙoran Mama da fuskar ta , a yanzu ta yadda da cewa ta samu waraka , irin ganin da take yi dusu-dusu shine ganin da ta haƙiƙance kowanne ɗan adam yana yi ,

Irin haske marar ƙarfin da take gani shi ta aminta da cewa shine hasken duniya , ita kuwa mai zata yi da ya wuce godiya ga Allah da ya nufe ta da samun waraka ?

rungume Mama tayi tana faɗin kalmar Alhamdulillah , Alhamdulillah babu ƙaƙƙautawa ,

Raf-Raf-Raf likitocin da suke wajen suka É—au tafi , cike da bayyana farin cikin su na samun nasara kan aiki ,

Youssouf wanda farin cikin sa bazai misaltu ba ya tako zuwa gaban gadon Falmata ,

" Fatima
Ya ƙira sunan ta , da amon muryar da take cike da shauƙi da zumuɗi ,

cike da ƙwaɗayin son ganin Fuskar wannan ma'abocin Alheri a gare ta ta ɗago kan ta daga fuskar Mama da take ta son sake gani tamkar mai son haddace kamannin ta a ɗan tsakanin lokacin ,

Dariyar haƙoran sa ta fara cin karo da su , kafin hasken farar fuskar sa irin na Mama da ta fahimci basu kai sauran mutanen wajen haske ba , ta bayyana mata , 

Kafe shi tayi da ido tana burin ganin kamannin sa ko da kuwa ace shine abu na ƙarshe da zata iya samun nasarar gani kafin hasken da ta samu ya koma duhu da har yanzu ta gaza yadda a zahiri ne ba mafarki ba cewa idanun ta suna ganin duniyar da ta rayu tsawon lokaci a cikin ta ,

Irin riƙon da ta yiwa fuskar Mama shi ta masa , ta kai hannun ta kan sajen fuskar sa ta tallafo fuskar tana kallon sa da irin ganin da ya sawwaƙa a gare ta  ,

Dariya Youssouf ɗin ya cigaba da yi da haƙoran sa ganin yadda ta riƙe masa fuska ƙam-ƙam , kamar wanda zai ƙwace ya gudu , ko kuwa ya ɓace mata ,

Da ƴar dariyar mai tafe da amon da  ke bayyana tsantsar farin-cikin ta , ta kai goshin ta ta haɗa da nashi , tsinin hancin su na gugar na juna ,

"Baban Mama nagode , nagode nago...

  "Fatima ki godewa Allah da ya baki lafiya , ni ma shi nake godewa , da ya nufa aka cimma nasarar aiki ,

Zama yayi daga gefen ta a bakin gadon ,

Mama tana tsakiyar su ya sanya hannu sa ya kewaye su da shi ya rungumo su jikin sa , yana jin matsanancin farin-ciki na zagaya ruhin sa ,

Tamkar a ire-iren shuÉ—aÉ—É—un lokutan da suka wuce cikin rayuwar ta da Yakaka , sautin ta ya bijiro cikin tunanin ta tamkar a lokacin take furta mata ,

" Falmata na ina ji a jikina watarana za ki warke , za ki ganni kamar yadda nake ganin ki .

Hawaye masu ɗumi suka silmiyo ta ƙarƙashin gilashin idanun ta , kewa tare da ƙaunar ahalin ta suka bijiro mata , a sarari ta furta

" Allah ya jiƙan ku Baba , Mama , Yakaka,  Bakura da Baana ,

'Amin 

Youssouf ya amsa mata .

*****

Cike da tarin sabbin dokoki da sharaÉ—in ziyartar likita a duk bayan mako guda na tsawon watanni biyu ,

Suka samu sallama daga asibitin , tafiyar ƙafa suka yi zuwa gidan su , inda Falmata ta dunga bin titi da ganin ta marar ƙarfi ,

Murna fal cike da zuciyoyin su ita da Youssouf , kome ta hango shatin sa sai ta tambaye shi wannan abun menene shi ? Meye sunan sa ?

Shi kuma babu gajiyawa cikin jin daÉ—in tambayoyin da take masa yake bata amsa tare da faÉ—a mata sunayen abubuwan .

Ƙofar gidan Musa suka tsaya , farin cikin da zukatan su ke ciki ya tunbatsa so suke su yi ɗaukanin sa da wani , alhalin babu wani nasu makusanci tare da su , dan haka gidan Musa suka yada zango ,

Musa da Ramlat sun taya su murna sosai inda a ƙarshe har 'yar walima suka shirya musu nan cikin falon su,

Yana riƙe da hannunta suka shigo gida ,

Suna shiga tun kafin su zauna ta ce  shi ,

"Baban Mama ka ƙira Hajja a waya na faɗa mata na warke nima yanzu ina gani ,

Yana murmushi ya zaro wayar sa daga Aljihun sa ya shiga lalubar layin Hajja ,

Ya san dole tana neman wani makusanci nata wanda zata raba farin-cikin ta da shi ,

Nigeria

Tsawon satikan da suka biyo bayan Rayuwar Yakaka tayi su ne wajen ganin ta cigaba da ƙokarin wanke laifin ta daga idanun jama'ar gidan Prof ,

Babu inda take zuwa kullum tana gida ita ke yin mafiya yawan aiyukan gidan ,

A hankali Hajja ta fara fahimtar kyawawan É—abi'un Yakaka , na kawaici da gudun tashin hankali , sannan kuma me sakakkiyar fuska ce ma'abociyar murmushi ,uwa uba yawan ibadar da ya zauna mata .

Hakan ya sa ta fara sakar mata fuska har takan É—an ja ta da hira a wasu lokutan ,

A yau ma zaune suke , suna 'yar hira Yakaka tana taya Hajja tsinke ganyen zogalen da zata yiwa Prof girki da shi

Wayar Hajja da take ajiye a gefe ta ɗau ƙara ,

Da sauri Yakaka ta ɗau wayar ta miƙa mata ,

"Ni hauwa'u waye ke ƙirana da wannan sanyin la'asar ɗin ? Allah jishe mu Alheri ,

ɗaga ƙiran tayi dai-dai da ƙwanƙwasa ƙofar falon da aka yi , Yakaka ta miƙe da saurin ta tana cewa

" Oyoyo Rahima .

Ta nufi ƙofar ,

"Assalamu Alaikum Hajja ni ce Falmata ,

Muryar Falmata ta karaÉ—e kunnen Hajja ta cikin wayar ta mai maÉ—aukakin sauti ,

Yunƙurawa tayi ta miƙe tsaye ɗingis-ɗingis ta nufi ɗakin ta da yake gefe ,

"Lale Lale Marhabin da uwarÉ—akina Fatima mutan turai ,

Ta furta hakan lokacin da take ƙarasa shigewa ɗaki cike da son kar Yakaka ta san da wacce take waya ,

" UwarÉ—akina ince dai duk kuna lafiya ? Ya Babban soja tare da 'yar rigima Mama , dafatan an samu nasara wajen neman magani ?

"Hajja Alhamdulillahi ki taya ni murna , na warke Hajja na samu lafiyar idona ,

"Da gaske Fatima kai Alhamdulillah nayi murna , nayi murna Allah Abun godiya kin warke Fatima ,? Buwayi gagara misali ,

Murnar Yakaka ta rikiɗe zuwa Fargaba lokacin da idanun ta suka sarƙe cikin na Sofi matar Yaya Dakta ,

Kallon-kallo na daƙiƙoƙi suka yiwa juna kafin ta tsinkayo muryar Doctor Hamza wanda yake tsaye daga bayan sofi ,

  "Malama kauce ki bada guri mutane su wuce kin yi wani sanƙanƙam a tsaye kina zarewa mutane ido ,

Da sauri Yakaka tayi baya tana komawa falon ƙarƙashin rakiyar mummunan tsakin da sofi ta bita da shi .

Ɗan diri-diri tayi a falon rashin ganin Hajja yasa sum-sum ta nemi mafakar ta a can ƙarƙashin kafar benen da yake falon ta samu guri ta zauna ran ta duk a dagule .

"Me ya sake dawo da shi yau kuma ? har ma da matar sa ?

Daga inda take tana iya jiyo tashin Muryar su ,

Da Sallamar da Docto Hamza ya yi ,

Basu ko zauna ba Sofi ta fara faÉ—in

"Wannan kuma wacce jemammiyar 'yar aiki aka samu haka a gidan nan ? Sai tashin ƙarnin man masu bleaching take ,  Doctor ba dai ita take yin wanke-wanke ba , ? Dan bana jin zan iya riƙe ko chokalin da ta wanke ,

A kaikaice Doctor hamza ya dube ta yana samarwa kan sa mazauni akan kujerar falon mai cin mutum guda ,

Motsa laɓɓan sa yayi kamar zai ce wani abu sai kuma yayi biris da ita yana zaro wayar sa daga Aljihu ,

Hannun kujerar da ya zauna ,Sofi tayi matsuguni a É—osane tana cigaba da cewa ,

"Ni kamar ma nasan Fuskar ta a wani waje ?

A hankali ya ɗago kai yana duban ta da ita ma ta karkato gare shi , fuskar ta ɗauke da wani irin yanayi na tsantsar ɓacin rai da bai kai ga sanin dalilin samuwar sa ba ,

" akan wa kike magana ne ?

" wannan yarinyar mai kama da farar kura , "

Ta furta hakan lokacin da tunanin ta ya gama tuno mata da inda ta taɓa ganin Yakaka a gidan Samy baby ,

Dariya ce ta so kama Doctor Hamza jin an kwatanta Yakaka da farar kura ,

     " ko ina sofin sa ta san wannan gantalalliyar yarinyar ?
       Ya tambayi kansa a zuci .

" okay ,

Yace a taƙaice yana mayar da hankalin sa ga fuskar wayar sa ,

"irin karuwan nan ce masu tsayawa a bakin hanya suna ne...

Fitowar Hajja cikin Murna ya katse mata zance da ta É—auko yi ,

" a a' ah Babban likita kaine tafe iwar haka ? Sannu da zuwa sannu da zuwa ka sha hanya tun daga birnin tarayya,

Da 'yar fara'a Doctor Hamza yake amsawa Hajja gaisuwar da take masa ,

Hajja ta ɗora ganin ta kan Sofi wacce ta jirkita sosai kan kafaɗun Doctor Hamza kirjin ta daf da fuskar sa , fiye da rabin cinyar ta na kan jikinsa ,  kan ta a ɗage sai shan ƙamshi take , ko ƙala bata cewa Hajja ba , "ah to wacece ita 'yar aikin zata gaisar ?

Ƙanƙan da ido Hajja tayi ,
Chapter 170 · 0% Book details