Sashe 60
Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ran ta ƙwal ta dawo cikin gidan kai tsaye ta wuce cikin ɗakin su falmata , a zaune ta tarar da ita , ta ajiye kayan hannun ta gami da ficewa taje ta wanko kofuna biyu da faranti ɗaya ta zo ta juye musu ,
   Falmata matso muci!
Lomar yakaka ta É—aya ta biyu ta zare hannun ta daga cikin abincin sakamakon ji da tayi zuciyar ta ta wani hautsina ta yamutsa kamar zata fito ta baki , nan take tsinkakken miyau ya taru a bakin ta ," ta matsa gefe tana jan numfashi .
Jikin ta har rawa yake ta balle murfin pepsi da haƙorin ta ta kafa kai tana kwankwaɗa , ba dire ba sai da ta shanye ,"
Sai dai me wani irin ƙugi da cikin ta yayi falmata da kan ta ta jiyo , kafin ta ankara wani kakkarfan amai ya taho mata , nan ta dunga kwarara shi a ɗakin daga bakin kofa , kaf abincin da ta ci tun daga na jiya da dare da bai kai ga narkewa ba har zuwa ƴar indomi ɗin yanzu sai da ta amayo su , amai har ta hanci , ga hawaye da yake ta tsiyaya a idanun ta , yunƙurin aman ta har kofar rumfar su ana jiyo sautin sa ,' har ta koma sai kakaru bata amayo komai sai koren yawu ,"
Falmata ta gigice da ya sa ta fatali da kofunan shayin nasu tare da bi ta cikin farantin indomi ta ɓarar da sauran , cewa take
  Yakaka yakaka yakaka , meye ya same ki ? Meye ne ? Baki da lafiya ne daman ? Me kika ci kike amai ? Da lalube ta ruƙo yakakar zuwa jikin ta bayan tayi zaune dirshan cikin aman da yakakar tayi ,
  Rashin amsa mata da yakaka tayi wacce take ta yunkurin amai har muryar ta ta shige ciki ya sa falmata fashewa da kuka tare da fara kwala ƙiran neman agaji ,' ihu take tana neman taimako
  Daga bakin maƙwarari inda hema da larki suke wankin dawa suna jin su duk yunƙurin aman da yakaka take sun ji sarai sun kuma riga sun yi hasashen abun da ka iya sanya ta aman dan haka suka yi biris , ! Yo ina ruwan su ? Sun ga ire iren ta yafi sau shurin masaƙi , '
 Â
Rabu da shegiyar yarinya , ba dai ita tace bariki zata yi wa shigar sojan badaskare ba ? Sama ta ka ba tare da ta ɗau darasi ba , ai kuwa zata ɗanɗani kuɗar ta , wannan somin taɓi ne daga cikin illolin faɗawa bariki ba tare da an nemi ilmin sa ba ," cewar hema
  ihun da ya yawaita ya farkar da madam saly daga baccin tofon girar da take shaƙa a gigice ta bazamo kan ta babu ko ɗan kwali guiguyayyar ƙeyar ta da sanƙon ta sai ɗaukar ido suke a hasken ranar da ta fara ɗagowa , " cewa take
    Wace masifar ce ta faru da farar safiyar ne ? Waye ya mutu ? Waye ya sha azaba ? Ake faman kururuwa haka ?
  Kai tsaye ta nufi ɗakin su hema inda take jiyo tashin ihun falmata ,"
Turus ta jaa ta tsaya ," yawata idanun ta tayi cikin ɗakin tana ƙanƙan da ido kafin ta lailayo wata ƙazamtatciyar ashariya ta watso ," ta ɗora da
    Na shiga uku na lalace ni salaha dan uban uban ku yakS me nake gani haka ? Gasar amai kuke koh me ?wace iriyar shegiyar ƙazamta ce wannan irin taku ta ƴaƴan ƙauye kuke gwada min haka a cikin gida ? Tab toh da sakel wallahi baza ku korar min kostomomi ba , yo wannan ai idan ɗaya daga cikin kostomomi na suka ga wannan iskancin ƙazantar da kuke babu ni babu ƙara ganin wani ya zo sayan ruwa ," dan babu mai yadda ya ci abun da kazamtattu irin ku suka taɓa ,!
  Wata irin damuƙa tayi wa kafaɗar yakaka ba tare da ta kula da halin galabaita da take ciki ba , ta hankaɗo su waje tare da falmata wacce ta maƙalƙale jikin yakakar ," suka tafi suka faɗi tare nan yakaka ta ƙarasa bajewa a ƙasa cikin halin rashin sanin inda take ,
Shegiya tsinanna yo wani ɗan iskan ya aike ki kije ki maƙalo ɗan tayi a mahaifar ki ? Ai ni daman kallon ki kawai nake ina jiran ranar da cikin zai baiyana kan sa , ko ta arziƙi ko ta tsiya , amma tun tuni na farga da shi , shegiya marar sa'a daga fara bariki har kin ɗauko ciki , to kar ki ji da wai ni bana rainon ƴaƴan shegu a cikin gidana dan haka ku san inda dare yayi muku , arziƙi nake nema ba tsiya ba baza ki raɓe ni da shegen abun da yake cikin ki ku maƙalamin asara da rashin sa'a ba ," yo ƴaƴan halas ɗin ma wasun su amfanin me suke tsinanawa kan su da iyayen su idan ban da masifa ? Haure kafafun yakakar tayi , idan kin gama watangaririyar ki a ƙasa sai ki tashi ku hau shiri , ban ji zan iya ba rainon ɗan shege ! ki bar ni naji da kaina !
Wani irin bugu zuciyar falmata take da kalaman madam saly suke sauƙa a kunnuwan ta , wai me take cewa ?waye yake da cikin shege ? Ɗan shege waye zai haife shi ? ta san ɗan shege sarai domin kuwa akwai wata ƴar makotan su da ta taɓa yi , iyayen ta suka kore ta , kowa a unguwar su ya tsane ta , jama'ah suka ta yin Allah wadarai da ita , mamar ta ta dunga kuka har ta daina fita layi , bata san ma'anar cikin shegen ba sai da ranar ta nacewa maman su da tambayar ma'anar kalmar,"a taƙaice ta bata amsa haihuwar yaro ba tare da anyi aure ba shine cikin shege," har garin su ya watse ba'a san inda wannan yarinyar take ba , tabbas cikin shege abu ne marar kyau matuƙa , madam saly tana nufin irin shi yakaka tayi ?
Tunanin ta ya katse lokacin da ta ji yakaka ta jaa wani numfashi tare da sake yin wani yunƙurin aman ,"
  Wani sabon ihu ta sake saki ,"
  Dan Allah ku taimaka min kar yaya ta ta mutu dan Allah ku taimaka mana ," yakaka ki min magana dan Allah ki daina shiru , ki tashi yakaka ki tashi ,
   Larki ce ta bar abun da take gami da nufar bakin fanfo ta taro ruwa a wani kwanon silver gami da sanya wani bokitin a bakin fanfon , a kaikaice ta ɗago yakaka wacce take ta sakin numfashi'ita ba sumammiya ba ita kuma bata motsin kirki ," ta kafa mata kwanan a baki ,
   Bata wani shaa na kirki ba ta cigaba da yunƙurin aman,"
  Aifa lalle kin gamu da wahala , gwara ma idan zaki tashi ki ta shi domin a gidan nan babu wanda zai damu ko mutuwa zaki yi a nan a yashe sai dai a tsallake ki a wuce , masu mutuncin ciki sune zasu jaa ki gefe a samo mai miki salla a je a turbuɗe ki , dan haka ma gwara ki bar lamɓo ciki ba kan ki aka fara ba , laulayi kuma dole ne tun da har kika iya zuwa kika kai kan ki aka maƙala miki maƙalalliya, kin dai ji abun da ,"saly fara," tace ki fara shirin bar mata gida ,"
   Juye mata ruwan bokitin da ta ɗauko tayi akan ta baki ɗaya ta jiƙa su sharkaf har da falmata wacce take ƙwaƙume da yakakar , daga ita har yakaka ba sauraran bayanin bakin larki suke ba ,"
wacce ita ce É—aya da ta kula su , ta zo kan su duk da cikin walakanci take musu Abun da ita a wurin ta taimako ne !
  Nan ta dangwarar da bokitin gefen su ta wuce bakin aikin ta tana cewa ,"
  Sai ke kuma ki tashi ki je ki wanke ɗakin da kuka gama chaƙuɗa shi da kazantar , sakarkarun yara ƙyauyawa !
Sanyin ruwan ya taimaka wurin farfaɗo da yakaka daga halin gigitar da ta shiga ," da taimakon falmata ta miƙe zaune ," yadda kan ta yake juyawa tare da wani irin bala'in ciwo ya sa ta kama kan nata da hannu biyu,"
 Falmata kaina zai fashe ,'!
Sannu yakaka ki tashi na kai ki É—aki ki kwanta ,'
 A wajen kwanciyar ta, ta taimakawa yakaka ta kwanta , fita tayi ta lalubi bokitin da larki ta ajiye ta ɗauka taje ta taro ruwa a cikin sa ta komo ɗakin ,"ita bata san inda tsintsiya yake ba a gidan , dan haka ta laluba ta tattara kofunan da farantin ta haɗa su wuri ɗaya , kasancewar ɗakin daman Ledar sa ta riga ta ratattake ta zama gutsirarra ,ta wurin da suke kwanciyar , daga tsakiyar sa zuwa bakin kofar dandaryar siminti ne , sai kawai ta kwarar da ruwan ta wuraren da take jin lema-lema , ta sa takalman ta biyu ta kwarfe ruwan ta tura shi wajen kofar ,'
Duk abun da take yakaka wacce idanun ta suke lumshe tana jin ta , karfin tashin ne bata da shi , wata iriyar mummunar kasala take ji tana bin duk gabobin jikin ta , ga juyawa da kan ta yake yi É—akin kan sa juya mata yake ,"
Gefen yakaka ta dawo ta zauna , cikin ran ta tana fatan lafiya ga yakakar wacce take zaton bacci take ,"