← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 147 OF 269

Sashe 147

Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gudu take tamkar wacce aka ɗaurawa tayoyi a ƙafa , bata san gabas ba bare yamma , karen wanda haushin sa ya jawo ƴan uwan sa karnai na bakin titi suka zama su uku , su ma bin ta suke da iyakar gudun su .

Ruwan saman da ya tsinke kamar da bakin ƙwarya shi ya sake gigita yakaka ,  har numfashin ta na barazanar ɗaukewa duhu na fara mamaye ganin ta .

Hakan shi ya hana ta fahimci karnukan sun koma baya sun daina bin ta tunda ruwan saman ya fara sauƙa .

Duk da cewa dare ne kuma titin babu kowa , amma shi ka'idar tukin sa ne haka baya cika gudu , sannu-sannu yake tuƙin sa cikin nutsuwa ƙira'ar Sheik Sudais cikin Suratul Al-Araf  tana tashi ta cikin sifiƙun motar , fitowar sa kenan daga asibiti inda ya yini yana wasu muhimman aiyuka ( shigar da bayanai akan marasa lafiyan da yake ɗauke da alhakin duba su )  saboda hutu da yake son rubutawa na sati shidda ya je gida ya gaida iyayen sa , sannan yayi amfani da damar wajen sasantan tsakanin iyayen sa ,

lokaci yayi da yakamata ace an kawo ƙarshen koma menene ya jawo rabuwar ta su tsawon waɗannan shekarun , ga su suna zaune babu abokan rayuwa wanda hakan ko kusa ba martabar su bane , duba da cewa shekarun su sun fara jaa ,

À son ransa a maida auren iyayen nasu kafin bikin Rahima wanda za'a yi a farkon sabuwar shekara me kamawa nan da watanni bakwai masu zuwa ,

Bai yi aune ba ta ɓullo daga kwanar gaban sa da gudun gaske ,  da ba domin a hankali yake tafiyar ba da babu abunda zai hana ya yi ciki da ita da mota.

Da ƙarfin gaske ya jaa burki ganin yadda ta bugu da jikin motar ta sa , ruwan saman bai hana shi ɓalle murfin motar ya fito ba , ya zagayo da sauri ta sashin da take dai-dai lokacin da ta miƙe tsaye daga faɗuwar da tayi ,

Da gudun ta tayi bayan sa ta ɓuya bayan ta riƙe jikin rigar sa ƙam da dukkanin hannuwan ta biyu , jikin ta ko'ina rawa yake .

Tsai yayi yana jin yadda wani nisasshen yanayi a wani shuÉ—aÉ—É—en lokaci makamancin wannan yana bijiro masa ,

KARE , KARNUKA su na bina dan Allah ka taimaka min , zasu kashe ni .

Muryar ta tayi amsa kuwwa a kunnuwan sa ta tafi ta tado Æ´ar uwar ta da take binne cikin ran sa me É—auke da salo da kalmomi iri É—aya da suka fito a jere cikin yanayi me kama sak da wannan , dan haka sai ya jiyo baki É—ayan sa yana fuskantar ta bayan ya fizge jikin sa ,

Hasken walkiya da na fitilun gefen hanya sun gaza wajen fiddo masa da ainahin kamannin fuskar ta da take rufe da niƙabi illa idanun ta da suka jirkita da zallar tsoro , da ya gaza jurar kallon su .

A hankali ya janye ganin sa daga kan ta ya dubi gefen titi inda ta ɓullo , ko alamun karnai babu , dan haka ya juya da sassarfa yana nufar ƙofar motar sa , cikin ran sa yana aiyanawa wannan wani sabon salo ne na matan banza .

Ki koma gida dare yayi .

Yace da ita .

Halin ruÉ—anin da take ciki bai isa jirkita mata tunanin da zai sa ta gaza gane shi ba , zuban ruwan sama akan kamilallar fuskar sa ba zai taimaka ba wajen hana ta shaida kamannin sa duk kuwa da rabuwa da yin tozali da tayi da shi na tsawon wasu shekaru , shi É—in ne dai mutumin da Allah yake kawo mata shi a duk lokacin da take tsaka da neman agaji me girma a cikin rayuwarta ,

Wani irin yanayi ta tsinci kan ta a ciki me nawi , da ya sanya ta sauƙe ganin ta ƙasa ,

A hankali ya tada motar sa ya gifta ta tana me cigaba da tsayuwa a wajen ruwan sama na sauƙa kan ta cikin yanayi na rashin madafa ,

Tsaki yayi a karo na biyu lokacin da yake sake kai ganin sa jikin É—an madubin saman motar sa yana hango ta , cikin nutsuwa ya murÉ—a kan motar sa ya taka ta yayi baya tare da dawowa inda ya bar ta ,

Shigo na kai ki gida .

yace ga ita ba tare da ya dubi sashin da take tsaye ba .

A hankali ta buɗe gidan baya na motar ta shiga ta rufe ƙofar tare da takurewa da jikin murfin motar tayi ƙasa da idanunta , wata irin kunya da nawin sa take ji ., girman laifin ta ninƙaya yake cikin tunanin ta yana ƙara girmama a idanun ta , zuciyar ta na raɗa mata ai ita ɗin bata cancanta da sake samun wani taimako kome ƙanƙantar sa daga gare sa ba .

ko motsi ta gaza yi , gani take cikin duk wani motsi da zata yi zai iya gane ta , zai fahimci ko ita wacece , da zuwa yanzu ta tabbatar bai shaida ta ba .

me zai faru idan ya gane ta ? Wataƙila ya wurgata kan titi .

Tana son tace wani abu ko da kalmomi biyu ne ,

ina Falmata ?  A wanne hali take ciki ?

A sama ta tsinkayi muryar sa ,

Wacce unguwa kike

Muryar ta a dushe ƙasan maƙoshin ta ta sanar da shi ,

Babu wanda ya sake magana a tsakanin su har zuwa lokacin da suka kawo unguwar , ƙofar gidan malama maryam ta nemi ya dakata zata sauƙa , baice ƙala ba ya tsayar da motar ,

Na-nagode

ta furta tana barin motar kai tsaye ta isa jikin ƙofar gidan malama maryam ta shiga ƙwanƙwasawa sannu kan hankali .

Jaan motar sa yayi yana barin unguwar lokacin da zuciyar sa ke nace masa wajen son bijiro masa da tunanin waccen tana haÉ—a su da yanayin wannan , amma bai bari tunanin yayi tasiri ba ya kunna karatun Al'qur'ani yana cigaba da saurara .

bai son tuno wani abu da ya shafe ta , ita ɗin ai bata cancanta da kutsowa cikin tunanin sa ba ko kaɗan  .

A hankali ta zame ta zauna a jikin ƙofar bayan shuɗewar ƙugin tayoyin motar sa bisa kan kwalta, ruwan saman na cigaba da sauƙa a jikin ta , kukan da take riƙewa tun shigarta motar ta saki da ƙarfi , kukan ha'incin da samy baby ta yi mata , kukan nadamar kuskuren da ta aikata a rayuwar ta, babu abunda take so a dai-dai lokacin irin ta buɗi ido ta ga falmata da mama a tare da ita , ta haƙiƙance sune kaɗai jinin ta a duniya sune baza su taɓa cutar da ita ba ,

Takurewa tayi a wajen tana karkarwar sanyin iskar É—aukewar ruwan sama da yake busa ta .

Washegari

Samy baby tana tsakiyar baccin ta na tofon gira misalin ƙarfe goma na safe ta tsinkayo bugun ƙofar gidan ta tamkar a tsakiyar kan ta ,

Mummunan tsaki ta jaa , bayan ta miƙe tana haɗa maballan gaban rigar baccin ta , kan ta ko ɗan kwali babu ta fito , dai-dai lokacin da aka kaiwa ƙofar wani mugun bugu tamkar za'a ɓalla ta ,

Kai wai wanne ɗan^ yake ƙoƙarin ɓalla min kofa , tamkar na ci bashin sa ban biya ba ?

Ta furta hakan a tsawace  tana ƙoƙarin zare sakatar ƙofar , bata gama zarewa ba ta ji anyi ciki da ita da ƙofar , tayi baya taga-taga ƙiris ya rage ta faɗi ,

A fusace ta ɗago kan ta hannun ta dafe da goshin ta , da ƙofar ta buga

Kutumelesi ,....

Kar ki yadda ki zage ni tsohuwar ƴar damfara , kuɗaɗena na zo ki mayar min da su account , saboda ƙaramar ƴar iskar da kuka haɗa baki kuka damfare ni tun daren jiya ta gudu , dan haka ko naira ɗaya ban yadda a samu giɓin su ba a cikin kuɗina ki dawo min da su yanzu-yanzu .

Wani irin fargaba ne ya dirarwa Samy baby , me Kamal yake cewa ? Yakaka ta gudu ?

Da kÆ´ar ta tattaro guntuwar nutsuwar ta ,

Ta juÆ´a ta fara taku tana cigaba da murza goshin ta ,

  Kamal ka shigo muyi magana a ciki , zancen ba na tsaye bane ,

Ke duba Samira ba inda zan shiga kawai kuɗaɗen nan zaki dawo min da su domin ko hannun ta bata yadda na taɓa ba tayi tafiyar ta tun jiya , bayan wahalar neman ta da ta saka ni cikin ruwan sama ƴar^ ke daman kin san yarinyar nan wata gara ce irin haka har zaki karɓi kuɗina akan ta ? Yi sauri dallah ki dawo min da su , da akwai inda zan tafi daga nan bani da lokacin ɓatawa .

Kallon ba yadda zan yi Samy baby take bin Kamal da shi , ta fahimci a bugen sa yake tatil kamar koyaushe , idan har ta nemi yin gardama kan zancen kuÉ—in nan kome zai iya faruwa da ita ,

  Bani account number

Ta ce masa tana shigewa ɗaki ɗauko wayar ta , daga ƙasan ran ta take jin mummunan ɓacin rai na taso mata akan abunda Yakaka tayi mata , ashe rashin mutumcin Yaks har ya kai haka ? Ta gudu ta jawo mata irin wannan babbar asara ? Allah ya so bata riga ta kacan-chala kuɗin nan ba da yanzu yaya zata yi da tijarar Kamal ? Tabɗi dole ne ta ɗau mataki akan Yaks , ta nuna mata kuskuren ta saboda gaba kar ta sake gwada mata irin wannan mugun wasan .

Cikin mintoci biyar Samy baby ta ɗibga asarar Naira miliyan biyun da suke mallakinta daga jiya zuwa yau , har gumi ne ke tsattsafo mata ,  lokacin da ta koma falo ta zauna bayan tafiyar Kamal da bai bar gidan ba sai da miliyan ɗin sa biyu ta koma account ɗin sa .

Ina Yakaka ta kwana ? Shine tambayar da Samy baby take yiwa kanta ,

Zumbur ! ta miƙe tsaye lokacin da ta ayyana inda Yakaka ta kwana , gidan Malama Maryam .
Chapter 147 · 0% Book details