Sashe 200
Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da gudu Maimounatou ta tsallake shi tana lalubar wayar ta , jikinta na rawa ta shiga ƙiran wata number ,
  Ana ɗaga ƙiran bata jira ance kome ba tace
   " ka tahou yanzou aiki ya cika sauran ka ƙarasa naka , ni nagama nawa .
 Daga ɗayan ɓangaren Mammadou zuruf ya miƙe tsaye tare da kewaye matar sa ya fita ,
   A harabar gidan sa ya tsaya , cikin yin ƙasa da murya yace
  " kina nufin yau kin yi nasarar kashe Youssoufa ?
 Jin jina kai tayi kafin tace "ƙwarai yau na cimma manufata ta amren sa .
 Â
Â
Â
 Â
 Â
Â
  Â
Assalamu Alaikum masu karatu da fatan kun wayi gari lafiya ?
Alherin Allah ya sadu da mu baki É—aya .
Nagode
 Â
[12/25/2019, 9:11 AM] +234 706 503 6187: MAFARI
( Hargitsin Rayuwa)
Umm'muaz
46
" Yakaka tana nan zuwa ita ma ,
Ita ce amsar da Falmata ta bawa Maman su , daga nan hira ce ta sarƙe a tsakanin su mai cike da labarin yadda rayuwa ta kasance musu bayan rabuwar su da juna .
****
Tiryan-tiryan Falmata ta basu labarin duk wasu bala'o'in da suka afku ga rayuwar su bata ɓoye kome ba illa mummunar rayuwar da Yakaka tayi da har ta kai ga haihuwar Mama da take jin har abada laɓɓan bakin ta baza su taɓa iya bayyana wannan mummunan labarin ga kowa ba .
  Ta cigaba da bata labarin ɓacewar Yakaka bayan haihuwar Mama ba tare da ta faɗi ainahin silar barin su da tayi ba har zuwa kan auren su ita da Youssouf yadda kome ya wakana , da rashin lafiyar Mama har zuwa tafiyar su USA da samuwar lafiyar idanun ta , komawar su Niger da kuma dawowar Yakaka , zuwa kan Mutuwar Mama .
 Shiru su duka ukun suka yi bayan gama sauraron ta , zuciyar Khaalty Rahima ta girgiza da jin yadda rayuwa tayi walagigi da 'ya'yan ta mata , tsakanin ƙarya da gaskiya , rayuwar rashin gata ta tsantsar wahala abu ɗaya ne mafi ciwo a gareta yadda duk su biyun suka auri Miji guda a wannan ƙarancin shekarun nasu , lalle wannan ƙaddara ce mai girma .
 Babu wanda ya fita sanin halayyar 'ya'yan ta duk kuwa da cewa sun jima da rabuwa daga yin rayuwa guri guda , amma ai ita ta haife su dan haka ta san halin kowaccen su tun kafin su mallaki hankalin da zasu iya boye abu a ran su .
 Daga zaman Falmata a gabanta kawo yanzu ta fahimci lalle akwai wata damuwa mai girma da take cinta a rai , wanda farin-cikin haɗuwar su bai sa ta manta da damuwar ta ba , ji tayi hankalin yana neman tashi , tana jin kamar akwai wani abu da Falmata take ɓoye mata da tafi danganta shi da Yakaka , dan haka ta muskuɗa tana kallon fuskar ta cike da nazari tace ,
 " Falmata kin samu labarin bayyana ta ne kika zo ? Ko kuma kawai dai kin zo ne ?
Murmushin yaƙe tayi kafin tace
  " Maman mu ban san kin zo ba , ban San kina nan ba, ta cigaba da cewa Mama ina Yaana da Bulama suke ? nayi kuka nayi kuka na damu akan sanin ina kike ko kina raye ko kin mutu ? shekaru suka yi ta tafiya ba tare da mun san halin da kike ciki ba , har na fitar da rai da sake haɗuwar mu a duniya , na koma yi miki addu'a iri ɗaya da wacce nake yiwa Baban mu , kan Allah ya jiƙan ku .
  Ƙwallar tausayin ta ya taru a idanun Khaalty Rahima , kafin tace
  " Yaana ta rasu a kan hanyar mu ta shigowa maiduguri , Bulama kuma yana nan ya girma , anjima kaɗan ma za ki gan shi ya dawo daga islamiya ,
  Ta cigaba da cewa ,
" Falmata ni na wanke gawar Mahaifin ku a cikin gonar na binne shi , ban yarda gawar mutumin kirki irin sa ta walaƙanta a hannun dabbobin daji ba , bayan na koma neman ku ban same ku ba , na dawo wajen ƙabarin sa mun rayu kwana biyu ni da Yaana da Bulama ina yi ma sa addu'a , kafin mu bar gurin , Allah sarki Mutumin ƙwarai mai tawali'u Allah ya masa Rahama ,
  " Amin Mama Amin ,
  Falmata ta amsa tana share hawayen da suke zubo mata ,
 Amnee ita ta katse musu hirar ganin duk fiye da rabin ta koke-koke suke yi da jimamin rayuwar su da ta wuce .
  " Ukhtee Rahima ku bar koke-koken nan haka , Fatima mu tafi ɗaki kiyi wanka ki shirya kafin a kawo miki abinci , "me zaki ci 'ya ta ?
 Ɗan murmushi Falmata tayi "kome ma zan ci , amma da zan samu tuwo miyar kuka da man shanu ,
  Dariya Amnee tayi tana kama hannun ta " muje kiyi wanka ki shirya , abinda kike so shi zaki ci .
 Bayan tayi wanka ta shirya cikin riga da zanen da Amne ta zaɓo mata daga cikin kayan Rahima , tsumu tayi zaune a kujerar gaban madubi ,
  " wani irin yanayi take ciki marar kan gado , ga dai ta a gida ta dawo kamar yadda ta zaɓarwa kan ta , take kuma ganin hakan shine zai raba ta da ɓacin-ran da take ciki , daɗin-daɗawa ma ta dawo ta tarar da farin-ciki mafi ɗaukakuwa a wajenta watau haɗuwar ta da Mama ,
Amma sai farin-cikin nata ya gaza kaiwa ga matakin da take so , baki ɗaya a hagunce take jin zuciya da ƙwaƙwalwar ta sun gaza tsayuwa gu ɗaya bare su taya ta samun gamsasshen farin-cikin da zai wanke mata rai .
  Ƙiran sallar La'asar da aka yi , yayi dai-dai da gilmawar tunanin da take ta yunƙurin danne sa tuntuni , wani sashi na zuciyar ta ya tunbuƙo da tambayar ta ƙarfi da yaji ,
  " a wanne hali Yakaka da Youssouf suke ciki ? Wataƙila sunyi ta neman ta sun gaji , wataƙila kuma ba su ma wani neme ta ba , dama ce suka samu ta tsara yadda rayuwa zata musu a gaba , ƙila ma ya saki auren ta zuwa yanzu ,
 Nan take ta runtse ido Zuciyar ta na tsananta bugu ,
  Da sauri ta miƙe ta shiga banɗaki gami da ɗauro Alwalar La'asar ,
Har ƙarfe huɗu tana kan Sallaya tana addu'o'i domin yaƙi da tunane-tunane , sai da Amnee ta matsa mata ta zo ta ci abinci sannan ta tashi suka koma falon tare , inda suka tarar da Khaalty Rahima ita ma ta idar da sallar ta nan bisa darduma ,
idanun ta kan falmatan tana duban ta da murmushi irin na zallar farin-ciki ,da ƙauna , ita ma falmatan da murmushi ta tafi a hankali ta zauna a gefen ta ,
Farantin da aka jera abinci akai amnee ta tura mata gaban ta , " ki cinye duk kin ji ko ?
Sama-sama take chakalar abincin duk kuwa da an girka shi yadda take so , miyar ta sha haɗin kayan ƙamshi na gargajiya , ga kuma man shanu gangariya ,
Sallamar Yakaka da ta sauka a kunnen ta daga bakin ƙofar falon shi yasa ta mayar da lomar da ta ɗauka da nufin kaiwa bakin ta ,
A hankali ta É—ago kan ta tana ganin shigowar ta ,da kai tsaye Yakaka ita ta doso bata kai ganin ta kan kowa da yake wajen ba ,
Ganin yadda ta taho yasa Falmata ta tsorata , dan haka ta janye kwanon abincin gaban ta , zuciyar ta na bugawa bata taɓa ganin Yakaka a fusace ya irin haka ba .
  Yakaka tana ƙarasowa ta riƙo kafaɗun Falmata da karfi ta jijjigata , muryarta a tsaurare tace ,
   " Falmata me yasa kika min haka ? Meyasa kika tafi ki ka barni ? Ashe kinyi girman da za ki iya yin gaban kan ki a rayuwa ? Ashe ni matsayina a wajen ki daman bai wuce na ƴar jagora ba da yanzu kuma lafiya ta samu wajen ki shine kika sanya kan ki a hatsari wajen yin gaban kan ki ? Wallahi da wani abu mummuna ya same ki bazan yafe miki ba Falmata .
  Kukan da take riƙewa ya taho mata , sakin kafaɗun ta tayi ta zauna daɓas akan kujerar gefen ta , muryar ta cikin kuka ta cigaba da cewa ,
   " Falmata kin manta ne da kusancin dake tsakanin mu ? Ashe har akwai wani laifin da ni zan miki ki kasa yafe min ?
  Zuwa lokacin ita ma falmatan hawaye ke sauƙa a idanun ta , ganin kukan Yakaka ya karya mata zuciya , a hankali ta zauna a gefen Yakaka , muryar ta na ɗan rawa tace " Yakaka , kiyi haƙuri ba yadda zan yi ne , kin san... Kawai bazan iya zama bane .
 Da wani irin yanayi Yakaka ta ɗago tana kallon ta , baza ki iya zama a gidan auren ki ba saboda ni ko Falmata ? Saboda mummunan kuskuren da na aikata ko ? Saboda...
  Da sauri Falmata ta katse ta tana nuno mata inda Khaalty Rahima da Amnee har da Hajja duk suna tsaye suna bin su da kallo ,
  "Yakaka kin ga fa Maman mu a tsaye , ga ta nan tana kallon ki , bata mutu ba ,ga Maman mu Yakaka .
  A hankali Yakaka ta bi inda take nuna mata da kallo cikin ran ta da ɗarsuwar tunanin ko dai Falmata ta samu jirkituwar tunani ne ?