Sashe 5
Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
cikin farin ciki da karamci da aka nuna masa Sarki youssoufa ya tsayar da ranar É—aurin auren Abdoul azizou da saratu ranar ishirin da biyar ga watan sha biyu shekara ta alif dubu daya da É—ari tara da tamanin da biyar 25-Dec-1985 .
A daren ranar ya aika aka kira masa yarima abdoul azizou , in da ya sanar da shi hukuncin da ya yanke tare da bashi umarnin ya shirya gobe da Maraice ya je su ga juna shi da saratu É—iyar liman domin kwanaki ishirin da É—aya kachal suka rage a É—aura musu aure ,
Ba tare da yarima Abdoul azizou yana fahimtar sauran kalaman bakin mai martaba ba ya amsa masa gami da yi masa godiya da sallama ya fito daga turakar mai martaban zuciyar sa cike da zogi da raÉ—aÉ—in bacin ran tashin hankalin da yake iya hango samuwar sa tsakanin sa da abar son sa "safiyyah "
Tabbas shi yasan yadda safiyyah take tsananin kaunar sa da kishin sa , yasan duk lokacin da ya je mata da labarin auren da aka riga aka nema masa ya kuma zama dole a gareshi ya amsa hannu bibbiyu , kasantuwar bai taɓa musantawa mahaifin sa ba akan duk wani hukunci da ya yanke a rayuwar sa domin shi mutum ne me ilmin addini sosai , yayi karatu sosai arabi da boko ya san irin haƙoƙin da iyaye suke da shi akan ƴa ƴan su hakan ya sa ya kasance ɗa mai tsananin biyayyah ga iyayen sa .
Dan haka a yanzu ma yayi aniyar karban auren da za'a yi masa da hannun aminci duk da cewa shi ba son auren yake ba asalima bai taba kawowa ransa sake yin aure nan kurkusa ba kamar yadda tun da yake bai taɓa son wata ɗiya mace irin son da yake yi wa safiyar sa ba kuma baya jin zai sake son wata ƴa mace irin son da yake yi mata " ya ajiye auren da za'a yi masa a karo na biyu a mizanin kaddara "
Sai dai babbar matsalar sa a yanzu tunanin hanyar da zai bi ya tunkari saffiyah da batun karin auren sa ,"a daren yau din domin baya son ma lamarin ya kwana ba tare da ya fitar mata da hakkin ta ya sanar mata ba a matsayin ta na matar sa da suke zaman aminci , kaunar juna da fahimtar juna " sai dai ya san mata idan aka zo batun kishiya ba dama ne '
Haka dai ya shiga gidan nasa baya sun natsa ya fuskance ta da maganar auren , sai dai ga mamakin sa ,' bata tayar da hankalin ta irin yadda yake zato ba hakan kuwa yana da nasaba da zancen ya riga shi isowa zuwa kunnuwan ta "
Abun nufi ta ji zance a cikin gida " abun ka da gidan sarauta da kuma yadda ya kasance hajiya uwa tana ta yamiÉ—iÉ—i da zance tana yada magana tare da fiffikar ta ta zata shigo gidan " da farko bata fahimci zancen ba sai da ta tambayi jakadiyar sarki ta wancen zamanin ita ce ta warware mata zare da abawa ta kuma kwantar mata da hankali tare da bata shawarwarin alkhairi da za su taimaka mata.
Amma duk da haka bayan dawowar ta sashin ta yini tayi tana kuka tare da tunanin ƙalubalen da yake fuskanto ta "abu ɗaya ne ya rage mata jin zafi ji da tayi matar da za'a aurawa mijin nata ba ƴar wani babban sarki bace ko kuwa wani hamshaƙin attajirin da kasa ta san da shi ba "
Ƴar Limamin Maraɗi ce hakan sosai ya rage mata zafi kasancewar safiyyah irin ƴaƴan sarautan nan ce masu ji da kan su da nuna isa sosai jinin sarauta na ƙasaita , da iko suke yawo a jikin ta ta yadda take ganin duk wani wanda ba ɗan sarautar da ya kai ya kawo ba a matsayin kasasshe a wurin ta,
safiyyah tana son sarauta tana alfahari da sarauta tana kuma ƙaunar masu sarauta , bata daukar mutanen da basu da sarauta da wani muhimmanci a rayuwar ta .
Dan haka koh lokacin da ranar da aka yanke na ɗaurin auren Abdoul-azizou da saratu ya zo , aka kuma ɗaura auren cikin kwanciyar hankali tare da bakukuwa kamar yadda yake a al'adar su , sam safiyyah bata bayyana matsanancin tashin hankalin ta ba duk kuwa da cewar abun yana nuƙurkusar ta a karkashin rai !Saboda yadda take kaunar mijin ta sai ga shi a yanzu ya zama nasu ita da wacce take ganin bata kai matsayin ta haɗa kafaɗa da ita akan abun da take so ba .
Hakan ya sa bayan tarewar Saratu "a sashin ta da aka gina mata daura da sashin Safiyyah ta hannun hagu "Sam safiyyar bata shiga harkar Saratu "A ganin ta saratu bata isa tayi gogayya da ita ba " "iyakaci idan sun haÉ—u a cikin gida 'idan sun je gaishe da hajiya uwa da sauran matan mai martaba biyu "Hajiya mai karamin É—aki da umma Amarya " " su gaisa da juna sama-sama, sosai ita saratu take jin zafin yadda safiyyah ta tattara ta tare da shirgin ta ta watsar a gefe take nuna kamar bata san ma da zaman ta a cikin gidan ba , "
Hakan yana kona ran ta , domin ita ta shigo gidan ne da nufin ta dunga bi ta ƙasa-ƙasa irin yadda ta saba ( a gidan mahaifin ta) tana tunzura safiyyah tana tada bala'i a tsakanin ta da Abdoul-azizu har dai tayi nasarar dusashe karfin soyayyar da ta lura Abdoul-azizu na yi wa safiyyah ,ta yadda ya kasance idan suna tare koyaushe bakin sa cikin ambaton Alkhairin safiyyah da kyawawan halayenta tare da yabawa safiyyar yake ,"
Sai dai bata samu damar hakan ba domin duk wata kafar da zata bata damar aiwatar da mummunan nufin ta safiyyah ta toshe "ta hana ta fuska "
A cikin hakan ta fara laulayin ciki bayan watanni biyu da auren su "wanda kuma kusan tare suka É—au cikin da safiyyah " domin ita ma tana É—auke da É—an tayin cikin ta na wata É—aya " .
Nan fa Saratu ta samu abun yin lanɓo ,kitifiri da feleƙe , ita a dole ga mai juna biyu " cikin yana wata uku su ka fasa Sanarwar ai Malamar jinya a asibitin da take zuwa awo a wancen zamanin ta tabbatar mata da cewa "Ɗa" namiji zata haifa '
Sanarwar ta fito ne ta bakin "Ɗan Zagii" a karkashin jagorancin "Hajiya uwa "wacce ita ma saratu ce ta yi mata Albishir tare da tabbatar mata da abun da malamar jinyan ta faɗi gaskiya ne "cikin rashin sanin Hajiya uwa cewa zancen ƙarya ce tsagoronta wacce ita Saratu ita ta haɗa zancen ta sakamakon jin wata matar babban likita da suka haɗu da ita wurin awu tana bada labarin injin awun da yake bayyana jinsin jariri tun yana cikin mahaifiyar sa " ( Asalima a wancen zamanin injin yin awun da ke gano jinsin halitar da yake ciki bai riga ya bazu a kasashen africa ba )
Nan take zance ya kewaya fada har ya isa kunne mai martaba ta bakin jakadiya " sosai mai martaba yayi farin ciki tare da bada goron Albishir me yawan gaske"
A bangaren Yarima Abdoul azizu shima yayi matuƙar farin ciki da wannan albishir har ma ya gaza boyewa ya bayyana farin cikin sa a sarari gaban idanun safiyyah tare da nuna ɗokin sa akan samun ɗa namiji da zai yi nan ba da daɗewa ba "wanda hakan ya tashi hankalin safiyyah a karon farko tun bayan auren sa da saratu "Amma sai ta share ta taya shi murna a sarari "duk da cewa cikin ran ta taso a ce ita ta haifo magajin maraɗi saboda kaunar ta da sarauta ",
Sai dai kasancewar ta ƴar sarauta ta kasance me iya boye hakiƙanin cikin ta, ya sa ba wanda ya fahimci halin da zuciyar ta ke ciki , hatta Saratu wacce take yin duk wani kilbibin ta da biyu 'dan ta turawa safiyyah haushi " ta gaza ganin bacin ran safiyyar .
cikin watannin girman cikin kafin zuwan ranar haihuwar sa kaf an gama tanadin kayan jarirai na É—a namiji wanda wasu ma mai martaba da kan sa ya sayo su a tafiyar sa Umrah , tarairaya da kulawa kuwa babu irin wacce Saratu bata samu tun daga kan surukan ta hajiya uwa da sauran matan mai martaba "da kusan suke karkashin ikon hajiya uwa "har zuwa kan shi kan sa mai martaba, da uban gayya yarima Abdoul-azizu wanda shima zuwa lokacin zuciyar sa sosai ta rinjaya ga son haihuwar É—a namiji sakamakon "janye hankalin sa ta siyasa da hajiya uwa da saratu suke yi "
Wanda har hakan ya soma taɓa amintaccen zaman su na fahimtar juna da su ke shi da safiyyah.
Ranar biyu ga watan ɗaya na shekarar alif dubu ɗaya da dari tara da tamanin da bakwai ,2-jan-1987 Saratu ta wuni tana naƙuda taci wahala sosai , kafin zuwa maraice ta haifo Santaleliyar ɗiyar ta mai kama da ita sak "
An É—auki tsawon mintoci uku a É—akin haihuwar da yake cikin baban asibitin maraÉ—i bayan bayyanuwar kukan jaririyar da likitocin da suka karbi haihuwar suka tabbatar wa hajiya uwa wacce take tsaye a dai-dai kan saratu tana ta faman jera mata sannu , cewar Saratu É—iya mace ta haifa har ma suka É—ago Santaleliyar jaririyar da ba'a ce yanzu aka haife ta ba saboda girman ta suka nuna wa hajiya uwa da saratu, shiru ne ya ratsa tsakani kafin Muryar hajiya uwa ta bayyana Cikin cewa".
Saratu kika ce Malamin jinya ya tabbatar miki Ɗa namiji ne a cikin ki ? watau ashe zancen ba haka bane ? ashe dai zance Altine "yayar saratun da suke uba ɗaya " zancen ta gaskiya ne da take cewa ke Saratu ba ƙaramar maƙaryaciyar yarinya bace " ,