← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 269

Sashe 28

Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

   Tayi taku biyu ta ji hannun falmatan ya sarƙe a cikin nata ,"
        ", Yakaka dan Allah kar ki ɗaɗe kuma ki lura da kyau da wurin da kuka ajiye ni kar ku manta wurin , sannan kuma kema ki kula da kan ki , Allah ya baku sa'a kije ki dawo ina jiran ki anan yakaka ,"

           Daga haka ta zame hannun ta daga cikin hannun yakaka ta buɗe zazzaƙar muryar ta tare da ware hannuwan ta biyu ,ta fara rero kalmomin bara ,"

       Alaro sadakah fisabilillah
       Alaro sadakha fisabilillah

Gurbin fararen idanun ta cike taf da hawayen da suke sheƙi a cikin hasken ranar , zuciyar ta kuwa ta jima tana kwararar da hawayen maraici da wata irin kewa maɗaukakiya ,"

     Juyawa yakaka tayi cikin sassarfa tana mai bin bayan su kolo waɗanda har sun riga sun soma tafiya ," lokaci guda tana mai share ambaliyar hawayen da suke shatata akan farar fuskar ta , "zuciyar ta kuwa wani irin raɗaɗi da zogi suke yi mata tana jin kamar baza ta iya tafiya ta bar ƙanwar ta anan ba , tana jin kamar idan ta bar ta wani abu zai taɓa ta , " tana jin kamar ta kasa bata kariyar da ta kamata ,"  sai dai sashi guda na zuciyar ta yana mai karfafa ta da cewa ta tafi ai ZATA DAWO TA SAME TA ,' kuma a yanzu wannan hanyar ce kaɗai mafitar su domin tallafawa kan su .," da haka suka tsallaka babban titin da ya raba su da sashin kasuwa ,"

     Dai-dai zasu gangara gangaren (kwarin) unguwar da zasu neman aikin ta sake waiwayawa a karo na barkatai tana me sake kallon bigiren da ta ajiye ƙanwar ta ta , chan ta hango wata mata ta miƙa mata wani abu da take kyautata zaton sadakha ce aka fara bata ," nan take fuskar ta ta yalwatu da kyakyawan murmushi har haƙoran ta suna masu bayyana cikin ran ta tana me yin hamdala ,

,"lokaci guda ta sanya kafafun ta tare da tattare zanin ta suna masu sauka cikin kwarin unguwar da ake kiran ta da ,"BULABURIN",  unguwar da tayi ƙaurin suna a birnin na maiduguri gurin tara lalattun mutane , kama tun daga kan ƴan shaye shaye , karuwai da ƴan daba ," .

    

   Assalamu Alaikum ina miƙa sakon gaisuwa ta ga masoyan rubutuna a duk inda kuke , tare kuma da baku hakurin jinkirin cigaban labarin da ake samu wanda a zahiri ba a son raina bane,  face hali irin na rayuwar ɗan adam wacce take tafe da cuta da lafiya ," duk tsawon lokutan da kuka ji ni shiru , shirun ya faru ne a sakamakon rashin lafiyar da nayi fama da ita , amma a halin yanzu Alhamdulillah da sauki .,
Nagode

#vote
#comments
#share
#fikrh[6/24, 9:59 AM] +234 701 013 7848: Fikrah writers association

*MAFARI........*
( _Hargitsin Rayuwa )_

*umm'muaz*

11

Fuskar ta ɗauke da murmushin da ya zarce zuwa dariyar da ta bayyana ƴan gajerun jerarrun haƙoran ta ,take shafa tare da sunsuna tarin kuɗaɗen da ta samu ta hanyar barar da ta shafe awanni fiye da uku tana zaune tana yi , wanda bata kai ga sanin yawan adadin kuɗaɗen ba ,"

Sake runtse kuÉ—aÉ—en tayi cikin tafukan hannayen ta ,lokaci guda kuma ta fara lalubar leÉ—ar da ta saya awara taci É—azu domin ta kulle kuÉ—aÉ—en nata a ciki ganin cewa kuÉ—aÉ—en sun taru a hannunta ,

zuciyar ta kuwa ƙwal kuma cike da farin ciki a rayuwar ta yau ne karo na farko da ta riƙe kuɗaɗen da suka kai haka yawa nata na kan ta , nan take taji ta sake gamsuwa tare da samun karfin gwaiwar cigaba da yin bara har sai yadda hali yayi , "

Gefe guda kuma tana Allah-Allah su yakaka su dawo ta nuna mata irin É—inbin alherin da ta samo musu ,"

Soke kuɗin tayi a cikin zanen ta bayan ta ƙulle su a cikin leɗar , ɗan saurarawa tayi tana mai jin yadda rugugin hadari yake bada amo bisa ga dukkan alamu garin gangame yake da hadari ,duba da yadda ta ji rangwamen zafin rana da yake nuni da cewa hadari ya kare ranar ," ,

Ji tayi hankalin ta yaÉ—an soma tashi sanin cewa a sararin Allah take ba cikin rumfa ba ,ita kuma bata shiri da dukan ruwan sama mummunan zazzabi da ciwon kai gami da tari yake samar mata ,"

ÆŠan matsawa tayi ta gurin da take jin muryar dattijon nan wanda tun da ta zauna a wurin take jin sa yana hada-hadar saye da sayarwar sa ,"

Baba dan Allah ince koh hadari ne sosai haka a garin naji sai cida garin yake ?

Ƙwarai kuwa ƴata hadari ne gashi nan ya shata bakikkirin a sama ," ya kamata ma kiyi haramar komawa gida ,'domin duk jama'a ma shirin tafiya suke ga la'asar ta riga ta gabato ,"

Tsugudi falmata tayi cikin fargaba tare da taraddadin rashin dawowar su yakaka har yanzu ,"

Tunanin ta ya katse ne lokacin da taji wata mummunar ƙara da tafi karfin a kira ta da rugugin hadari domin gabadaya sai da ta ɗimauce ,"lokaci guda ta miƙe a zabure gami da tsayuwa akan kafafun ta da take jin ƙasa na girgiza ,"

Waige waige ta fara yi lokacin da ta tsinkayo hayaniyar muryoyin mutane sun ƙaru tare da takun kafafun su da alama guje-guje aka fara ,"

Cikin tashin hankali ta sake matsawa wurin dattijon nan da take jin muryar sa sama-sama da alamun tashin hankali ,sai dai rashin jin isashiyar hausa da kuma yadda ta firgice ya sanya ta kasa tsintar koh da kalma guda daga cikin kalmomin da take ji a bakunan al'ummar wajen bare ta fahimta,"
Ba-Baba dan Allah meke faruwa ne ƙarar menene haka naji ?

Ƴata bom ne ya tashi yanzu yanzu a post-office , maza maza ki kama hanyar gida domin kuwa kasuwar ma yanzu za'a rufe ta sojoji zasu zo ,ai yau gari sai yadda hali yayi bom a post-office matattarar mutane ? Kai Allah dai ya kawo mana karshen wannan masifa ,"

Kalmar bom da ta sojoji ita kaɗai falmata ta fahimta cikin dogon jawabin da dattijon nan yake mata ," a take wasu hawayen da bata san lokacin da suka samar da kan su ba suka fara sintiri akan fuskarta ," dai-dai lokacin da taji an kai mata wata bangazar da tayi sanadiyar zubewar ta a ƙasa da bata raba ɗaya biyu ƙaton da ya bangajeta gudu yake yi domin ya samu isa ga mafakar sa kafin zuwan sojoji koh kuma tashin wani bom ɗin ,"

Ji tayi dattijon nan ya sanya hannu ya ɗago ta lokaci guda yana me fada akan rashin imani na wasu mutanen ta yadda har wannan garjejen ƙaton ya bangaje ƴar ƙanƙanuwar yarinya kuma miskiniya amma bai koh juyo ba ,"

Ƴata ina abokan tafiyar ki da suka ajiye ki anan suke ?? Koh kuma ina ne unguwar ku ? Kiyi maza fa ki samu ki bar wajejen kasuwar nan dan nan da mintoci ƙaɗan kowa zai watse ,"

Yakaka , yakaka , itace kawai kalmar da bakin falmata ya furta ba tare da ta jira jin ƙarshen zancen dattijon nan ba , lokaci guda kuma ta fara jefa kafafun ta ba tare da ta san inda take sanya kai ba koh kuwa inda ta nufa ," ita dai burin ta ta sadu da yayar ta ,"

AWANNI UKU BAYA

Tun da suka gangara gangaren unguwar yakaka da yagana suka ware idanun su sosai suna masu kallon tun daga kan tsarin gine-ginen unguwar har zuwa kan mutanen da suke cikin unguwar da mafi akasarin su kallo ɗaya za'a musu a fahimci ƙarancin tarbiyyar da take tare da su ,"

Unguwa ce irin ta yaku-bayi talakawa mafi yawan gine-ginen unguwar sun shiga ƙasa kana iya ganin kan ƙwanukan ,ƙananan gidaje da suke manne da juna ,waɗanda kallo ɗaya za'a musu a fahimci mutanen cikin su na rayuwar rashin wadata,"

Mafi akasarin matasan da suke yawo a unguwar irin Æ´an shaye-shayen nan ne masu rabin kai a aske ga kuma uwa uba rangwamen tsafa da ta bayyana sarari a gare su ,

,"duk tashin muryoyin su irin na Æ´an maye ne da take tafe da amon kalmar arziki É—aya ashariya goma ,"

Yaran su ƙanana kuwa kaso tara cikin goma yawo suke kafafun su babu takalma ,dauɗa ta samu mahallin zama na dindindin a jikin su da suturun su ,"

Ga Ƴan mata birjik waɗanda mafi yawa hannayen su zuwa kawunan su ɗauke yake da robobi zuwa bokitaye da fantekun ,ababen ci na sayarwa ," sun sha kwalliyar gazal da jar hoda ,laɓɓan su na ƙyallin jan baki 24 awa ,",

Duk ba wannan yafi girgiza zuciyar yakaka ba asalima ita bata hango wani aibu koh naƙasu a tare da mutanen unguwar ba idan aka ɗauke ashariƴar da suke amfani da ita cikin maganganun su wanda hakan yake bakon abu a wurin ta ,sai dai duk da haka ta ɗauki hakan a matsayin wayewa irin ta ƴan birni duba da cewa ita a wurin ta wayayyun mutane ne .,

Abun da yafi takura yakaka da firgitata shine yawan karnuka tare da ƙyanwowin da take ganin giftawar su a cikin unguwar tamkar dai yadda akuyoƴi da tumakai suke yawo a garin su wanda hakan babban barazana ne a gare ta kasantuwar ta ma'abociyar tsoron karnai , yakaka tana ƙin kare yadda take ƙin mutuwar ta koma fiye da haka , dan tabbas da tasan zata haɗu da karnuka irin haka da ko daga cikin sansanin su baza ta fito ba bare har ta ɗauko kafa ta shigo wannan unguwar ,",

Ga bangaren yagana kuwa yanayin tsarin unguwar ne sam bai mata ba a zaton ta zata ga sun doshi unguwar hamshaƙan masu kuɗi ne ,"inda zata yi kallon birni sai take ganin su a wata ƙazamar unguwa wadda koh a garin su ba'a sanya ta cikin unguwannin arziki ba ,' duk sai ta ji tafiyar ta daina yi mata armashi .,
Chapter 28 · 0% Book details