Sashe 148
Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ɗan siririn mayafinta da yake ajiye a falon shi ta ɗauka ta yafa akan rigar baccin jikin ta , ta fito a fusace bayan ta rufe ƙofar gidan da makulli ta zagaya layin bayan su kai tsaye ta doshi gidan malama Maryam da tunda take sau ɗaya ta taɓa taka gidan , Sai fa yau da zata kuma zuwa .
Ko sallama bata yi ba ta danna kai cikin gidan , ilai kuwa tana shiga falon ta tadda Yakaka tana zaune ta jingina da jikin É—aya daga cikin kujerun falon da farantin cin abinci a gaban ta wanda bata kai ga sa hannun cikin sa ba .
Da shigowar ta Yakaka ta miƙe da alamun firgici a fuskar ta wacce ta ɗan kumbura kaɗan tayi jaa ,
Anty Samy ..
Da hannu ta dakatar da ita , ki min shiru Yaks , ashe baki da mutumci haka daman? Ƙyat ! tayi Kwafa ki wuce mu tafi gida inason yin magana da ke .
Malama Maryam wacce tashin muryar Samy baby ya sanyata fitowa daga cikin ɗakin ta , ta ƙaraso wajen tana bin Samy baby da kallon nazari
Yayar Yakaka lafiya dai ko ? Anan Yakaka ta kwana tun jiya cikin dare take ta kuka taƙi sanar da mu abunda ya sameta , dan Allah idan laifi tayi miki kiyi haƙuri ki yafe mata
Wani kallon banza Samy baby ta jefawa Malama Maryam saboda ta fara fahimtar duk wani taurin kai da take hango alamun Yakaka zata gwada mata har da taimakon koyarwar Malama Maryam wacce ta lura duk wasu sabbin É—abi'un Yakaka daga gurin ta ta kwafe .
  Ki wuce mu tafi
 Ta sake maimaitawa tana mayar da duban ta kan Yakakar
Da wani irin yanayi cikin muryar Yakaka , wanda yake fallasa halin baƙin cikin da zuciyar ta ke ciki , tace
  Bazan bi ki ba Anty Samira ni daga nan Maiduguri zan koma wajen Falmata da ƴa ta , bazan taɓa yadda nayi yadda kike so nayi ba . BAZAN SAKE YIN ZINA BA
  Kif-kifta ido Samy baby tayi tamkar bata ji da kyau ba ,ta karkata kai tare da ɗage shi sama ta ce :
Kika ce me Yaks ?
Bata jira ta amsa mata ba ta É—ora da cewa .
 Maiduguri ?? Sai ta kwashe da wata gajerar dariya ,
Wa kika sani a Maidugurin ? Waye naki a can wa kike da shi a duniya ?
Da sauri Yakaka ta amsa mata har muryar ta na sarƙewa
Ƙanwata Falmata da ƴata Mama !
Hahaha !
Yaks kenan ai Falmata da Æ´ar jaririyar da kika gudu kika bari duk sun riga sun mutu , au ashe ban faÉ—a miki ba ko ? Sorry lokacin kina tsaka da jarabawa ne kin san fa ke mayyar karatu ce ...
Kukan kurar da Yakaka tayi ta tura samy baby ta faɗa kan kujerar bayan ta , ta hau ɗare-ɗare kan ta , tare da maƙure mata wuya shi ya hana samy baby cigaba da zancen da ta shiryo shi a yanzu ,
  Me na miki Anty Samira ? Me na miki ? Ƙarya kike min koyaushe Ƙarya kike min baki taɓa faɗa min gaskiya ba Ƙarya kike Falmata na bata mutu ba , Ƙarya kike yi bata mutu ba , ki faɗa min gaskiya me kike shiryawa game da rayuwata ? Me na miki ?
Da taimakon Malama Maryam suka É—aga Yakaka daga kan Samy baby wacce duk Yakaka ta yakushewa wuya , gabaÉ—aya ta birkice musu kamar me tashin Aljanu , ihu kawai take tana cewa
Falmata bata mutu ba ƙarya ne ,
  Addu'o'i Malama Maryam take tofa mata tana riƙe da ita ,
Bata cikin hankalinta ta É—ago kan ta hawaye wani na korar wani a fuskar ta ,
Ummi , ki kaini Maiduguri yanzu-yanzu dan Allah , ki kaini naga Falmata
Zan kai ki Yakaka ki nutsu ki daina wannan ihun babu kyau , kiyi innalillahi wa inna ilahi raji'oon , kiyi addu'a ki bar kukan nan haka .
Gƴaɗa kai take ba domin tana fahimtar kalmomin Malama Maryam ba , bakin ta ya gaza furta kalma guda illa karkarwa da laɓɓan ta ke yi , zuciyar ta ke wani irin bugu da tsananin tsoron da yake barazanar tarwatsa mata zuciya , kalmar Mutuwa ga Falmata tayi mata tsauri da girma ta yadda zuciyar ta gaza ɗauka , tunanin ta ya guntule cikin rashin sanin takamaimai a halin da take ciki , ƙiyayyar samy baby sabuwa fil take yaɗo cikin ran ta .
Da baya-da-baya Samy baby ta ƙarasa barin falon tana jin yadda tsoron halin da ta ga Yakaka a ciki na cika mata zuciya ,
 Â
Niamey Niger
Cikin makonni uku da ƴan kwanaki visa Falmata da Mama ta fito , Biyamuradi Youssouf bai jinkirta ba wajen fara shirye-shiryen tafiyar su , bayan ya ɗauki hutun sa na kwanaki talatin a wajen aikin sa , tare da gudurtawa cikin ran sa idan kwanakin sun gaza wajen yin abunda ya kai su , zai dawo ya rubuta takardar neman iznin hutu batare da biyansa albashi ba ya koma .
Cikin satin zuwan sa Maradi sau biyu , bayani sosai ya tsarawa Maimartaba tare da hajiya Umma kan cewa aiki ne zai kai shi zouwa ƙasar Amurka ,
Babu shakku cikin ran su suka masa addu'o'in samun nasara kan abunda za shi nema , tare da fatan dawowa lafiya .
Bangaren matan sa ma bai samu matsala da Siyama ba , wacce take da tsananin yarda ga mijinta , dan haka ta hau shirya masa ƴan kayan cimaka da zai iya yin guzurin su zuwa ƙasar da za shi , zuciyar ta cike taf da kewar sa da ta fara tundaga yanzu , lokaci-lokaci tana sharar ƙwalla rabuwa da masoyi duk da cewa ba sabon abu bane shafe kwanaki masu yawa irin haka basu tare , amma haka kawai taji wannan tafiyar tasa ta tsaya mata a zuci ko domin ƙasar zai bari bakiɗaya zuwa wata nahiyar ?
Ga Gimbiya Maimounatou kuwa sam bata gamsu ba da zancen barin sa ƙasar , hasalima batun tafiyar sa ya kawo mata tsaiko ne kan wani Al'amari da take ɗorarwa akan sa , sai take ganin tamkar da gayya ya tsiri tafiyar ,hakan ba kome bane face salo ne na kauda-bara da ya sha faruwa a duk lokacin da take kan gaɓa na son cimma ƙudirin ta , sai dai baza ta fasa ba , ba kuma zata gaza ba wajen cigaba da bibiyar kome a sannu har sai haƙar ta ta cimma ruwa .
Dan haka babu ƙarsashi a tare da ita suka yi bankwana bayan ta haɗa masa ƴan nata kayan cimakan da basu cika yawa ba saboda zuciyar ta da take shaƙare da takaici , duk da cewa tayi iyakar ƙoƙari kamar yadda ta saba ta boye abunda ke binne ƙarƙashin ran ta .
Daga Tafeeda kaÉ—ai ya so samun tangarÉ—a wanda yake da sani sosai akan harkar aikin su , ya kuma titsiye Biyamuradin da tambayoyi akan aikin da yace zai kai shi US , sai dai ga mamakin sa hanya-hanya da zamiya iri-iri Biyamuradi ya dunga yi masa da ya hana shi sanin takamaimai gaskiyar lamari game da tafiyar ta shi ,Â
karshe dai ya fahimci babu shakka akwai abu me girma da Aminin sa ke ɓoye ma sa wanda kuma lalle wannan abun ya shafi rayuwar sa ta kurkusa , sai ya ɗiga ayar tambayar . Cikin ran sa ya ƙudurci bin diddigin kome .
Duk wani shirin tafiyar su ya kammala , kamar yadda Biyamuradi ya Alƙwarta ga Hajja , ya ƙira direban da zai kai ta ana washegarin ranar tafiyar su , ya sanar da shi gobe da safe ya zo su kama hanyar Nigeria da Hajja .
Jakar matafiya karama da Babba Ya kawo musu ,
Ya miƙa Babbar ga Hajja , yana cewa
Hajja ga wannan jakar ki shirya suturun ki ciki , wannan ƙaramar kouma na Fatima ne , kayan ta kaɗan zata ɗauka ba wasou masou yawa ba kawai aboubouwa masu muhimmanci da zata iya bouƙata su zata zouba a ciki, ita kouwa Mama ba sai an ɗauka mata wasu suturu ba , kaya biyu kawai sun isar mata idan munka kai can duk za'a saya wasu suturu sabouda yanayin mu da nasou ba ɗaya bane .
Au Babban soja wai da ni har mun shirya kayan a cikin manyan akwatuna ? Fiye da rabin kayan nasu ma ai mun loda su a akwatuna har huÉ—u , ashe tafiyar ba ta guzurin kaya bace ikon Allah .
ÆŠan murmushi yayi , a ah hajja a ajiye waÉ—annan suturu a gida zamu sayi wasu a can .
To ai babu kome , huta-roro ( waken gizo ya ƙi 'Ya'ya ) wannan babu neman masu dakon kaya a tashar jirgin sama , oh duniya kullum cigaba ake watau ita turai ba'a zuwa da kayayyaki dayawa ? Dayake ma can gidan kaya ne , kamfaninnika ne da su na suturu sai ka zaɓa ka darje , kuma fa irin atamfofin nan namu arhar bulus ne da su a can ko Babban soja ?
Cikin gundura da hirar hajja , yace
hajja ai can basou sanya tufafi hakka irin namou , su suturun su duk kananun kaya ne sai kouma kayan sanyi ,
Firfito da idanu tayi bayan ta rafka tagumi fuskar ta cike da alhini ta É—ora da :
Ƙananun kaya ni hauw'u ? Da kai da Falmatar watau duk ƙananun kaya za ku dunga sawa ? O'o ana bariki a turai , to ita dai Mama ku dunga suturtata da kyau saboda yanayin lafiyar ta daman ba kumari ta cika ba . Kai tir da rayuwa da ba ta Musulunci ba
Sai kuma ta É—an saki murmushi tunowa da tayi da wani abu ,
Kuma ka ga ƙananan kayan zasu amshi jikin ku Babban soja , musamman ma ita Falmata , ƴar riga da wondon nan na zamani ka daure ka saya mata ɗanɗasa-ɗanɗasa ba ƙaramin haska ta zasu yi ba .
 Ɗan zunkuɗawa yayi akan kujerar jin an taɓo masa inda yake masa ƙaiƙayi ,