← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 110 OF 269

Sashe 110

Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Babu kome Alhaji zamu tafi tare , me zaman aure ma ta amince bare ni ƴar rakiya ?? Ai ko gaba da binnin sin ne Alhaji ba na ƙi raka ƴar marainiyar Allahn nan ba , kai shima dai wannan dogon balaraben nijar ɗin Allah yayi masa Albarka da duk da kyan nan nasa da cikar zati irin ta ɗa namiji amma haka ya runtse ido ya ce ya amince zai auri wannan murɗaɗɗiyar bahaguwar yarinyar , ai dole ayi masa godiya bawan Allah .

Nan dai Alhaji ya sallame su yana sake musu godiya akan biyayyar da suka ma sa ,

Kan hanyar su ta komawa hajja mai wurya tana riƙe da hannun falmata tace

   Ke ƴar nan Allah ya dube ki ya tarfawa garin ki nono , irin wannan zankaɗeɗen miji da Allah ya wanke ya ba ki ?? Ai ko ɗiyar masu mulki ba ta ƙi shi ba , to zan fara faɗa miki tun wuri tun yanzu , ki zubar da waɗannan hargitsatsun halayen naki tun a nan nigeria kar ki ce zaki tafi gidan auren ki da su , saboda wannan dai miji naki wallahi kin yi sa'a wanke hannun ka taɓa Allah dai shi sa yadda surar nan tasa take halin sa yafi haka kyau ,

Ai bazan bar gidan nan naki ba sai na ga kamun ludayin zaman naki da shi , ato sai ki shirya ni ɗin dai da kika tsana kike ƙin bani riƙon jaririya , nice dai me miki zaman ɗaki sai dai muyi wacce za mu yi mahaukaci ya ɗau rigar kurma ...

Zame hannun ta tayi daga cikin na hajja tayi gaba ta miƙa hanya , ƙalau tamkar me gani saboda yau da gobe ta fara haddace hanyar a ƙwaƙwalwar ta,

   Sasakai hajja me wurya tayi
   Au aikin banza kenan hanci ba ƙafa , to ki fi ruwa tafiya , nace ki fi ruwa tafiya , wannan yarinyar sai na dage kafin ta shiga hanya ta ɗau haske ta san me duniya take ciki kan ta hayaƙi yake ,!

Falmata ko sauraron ta bata yi ba hasalima ji tayi hayaniyar hajja me wurya ta hana kwakwalwar ta sakewa tayi tunanin da ya kamata shi yasa ta zame hannun ta ta rabu da ita ,

   Aure da ita da shi ?? Wanene shi da yace baban baby ne ? Da gaske shine baban baby ? Wanne irin aure zasu yi ? Ina ne ƙasar ta su ? Idan suka tafi zasu dawo ? Bata son barin nan inda take , burin ta watarana dr hamza ya nemo mata maman su , to amma yanzu kuma ga shi zata tafi ta bar nan ɗin ,

    Abun da ta sani zata yi kome , zata tafi ko ina zata kuma ta shiga kowannen wahala domin ta tsira da baby mama , domin ta tsaya tare da baby mama , domin baby mama kar ta sha wuya , naƙasun ta miskinancin ta , rashin idanu ,

da ace ita lafiyar ta ƙalau , bata buƙatar abokin tayi wajen gina rayuwar ƴar ta , da zata gudu da baby mama ta ɓuya wani waje tana kula da ita , to amma ita ɗin ma miskiniya ce dole ne ta bi baban baby da yace zai kula da mama ƴar sa ce !

Ƙarfe biyu cif aka fara fito da jakar bocco ɗin falmata wacce ta haɗe kayan ta da na yakaka kakaf a cikin babbar baccon yakakar , sai kuma kayan baby mama shima a cikin babbar jaka , duk aka zuba su a bayan dunƙulalliyar motar soji me ƙirar golf kofa biyu ,

Biyamuradi youssouf ya taka zuwa cikin gidan falon prof , suka yi sallama inda prof ɗin ya bi shi da kalaman godiya ya kuma ɗora da damƙa masa amanar fatima tare da roƙon sa akan ya kula da ita , ita ɗin abar a tausayawa ce ,

Nan youssouf ɗin ya amsa tare da ɗaukar Alƙawarin zai kula da ita ,

Yana zaune hajja me wurya da falmata rike da mama haɗi da rahima suka shigo , falmata tana shirye tsaf cikin sabuwar atamfar ta ruwan ganye da adon furanni farare,  ta saka farin hijabi har guiwar ta ,

Daga gefe suka tsugunna , nan prof yayi musu addu'o'i tare da ƴan nasihu ya sake ɗanƙa amanar falmata a hannun hajja me wurya har lau ,

Daga ƙarshe ya zaro kuɗin sadakin falmata naira dubu ishirin sabbin bandir ɗin ƴan ɗari biyu ,

   Ungo Rahima ,

miƙawa fatima kuɗin sadakin ta hakkin ta , fatima ina me baki haƙuri akan yadda auren ya zo a ƙurarren lokaci ban miki kome ba da iyaye ke yiwa ƴaƴan su idan zasu kai su gidan miji , amma na miki alƙawari na kuma yi magana da shi mijin naki akan idan kun isa ya tura min account number zan tura da kuɗin da za'a saya miki kayan ɗaki da na amfanin gida a chan kin ji ko ? Ki riƙe wannan sadakin auren ki ne ,

Da sauri falmata wacce idanun ta suka kawo ruwan hawaye akan irin ƙaunar da prof ke musu tare da sanin cewa yau zata bar gidan shi zuwa wani waje da bata da sani akan me zata je ta tarar , tace

  Baba na bar maka kuɗin ni babu abunda zan yi da su ,

  A ah fatima ki karɓa nace hakkin ki ne , watarana zaki samu abun saya da su ,

  Muryar ta na karkarwar kukan da ta soma tace

  Baba to ka riƙe min idan na dawo zan karɓa ,

Ba shiri hajja me wurya ta zungure ta , tana satar kallon youssouf da yayi shiru yana sauraran ta ,

   Ƙasa-ƙasa tace
  Ka ji min sakarya auren da tun baki kai gidan ba kike fatan ki dawo , ??

Kawo ƙuɗin na riƙe mata Rahima, irin kunyar nan ce ta amare take gwada mana ,
  
Rahima da take murmushi a hankali ta miƙawa hajja me wurya kuɗin ,

Madallah Allah ya sanyawa auren ku Albarka Allah ya sa abokiyar arziki ce , Allah ya kauda shaiÉ—anun aljanu da na mutane a tsakanin ku , Allah ya sa mutuwa É—ai ita zata raba ku, Allah kuma ya baku zuri'a masu albarka irin wacce manzo Allah zai yi alfahari da ita !

    Laɓɓan Youssouf ne suka motsa a hankali da ,"Ameen .

    Rahima ita ta raka su har bakin mota tana jin yadda kewar su take taso mata , ai anyi sabo zaman watanni tare , duk da cewa ta so tafiyar su tafi haka tsawo sai dai damar bata samu ba , amma ko babu kome tayiwa fatima murnar samun ɗanɗasheshen mijin da ya ƙere sa'an auren ta ta ko'ina hakkun fatima me sa'a ce .

    Da wannan tunanin ta rufe musu ƙofar motar bangaren da falmata ta shiga inda suke zaune tare ita da hajja me wurya a bayan motar , Biyamuradi da direban sa suna gaba ," .

*****

Tafiya ce suka ɗora ta miƙaƙƙiya tun daga maiduguri zuwa sokoto , inda basu samu isa sokoto ba sai cikin dare misalin sha biyu da rabi , alamun gajiya da suka bayyana baro-baro ga falmata tare da baby mama wacce ta ke yin ƙananun rikici na gajiya da rikon hannun ya sa youssouf ya kama musu ƴan ɗakuna a wani ƙaramin guess inn da yake cikin garin na sokoto zuwa wayewar gari sun huta sun kuma sake shiri sai kuma su faɗa yankin niger ta," ilela ," su ɗau hanya ta birnin N'konni da zai ɗaura su kan kodoben da za su sadu da birnin Niamey ɗin niger ....!

Ba su suka samu isa Niamey ba sai ranar Asabat da misalin ƙarfe bakwai na dare duk kuwa da gudun da direban ya dunga shararawa tun da suka faɗa yankin niger kasancewar sun shigo ƙasar su , kowa yaga gilmawar motar su basu hanya ake ,

Kai tsaye direban ya wuce da su ( Radisson Blue hotel,) ƙarƙashin umarnin youssof , kasancewar shahararren hotel ɗin mafi yawan lokuta nan ne wajen sauƙar sa idan wani aiki ya kawo shi Niamey ɗin kasantuwar hotel ɗin kusa yake da manyan ma'aikatu masu muhimmanci na ƙasar da ke babban birnin Niamey ,

Babu ɓata lokaci ya kama musu ɗakuna inda hajja me wurya da falmata zasu zauna a ɗaki guda , (one bedroom Residence ) dake ƙasa shi kuma ya Kama nasa ɗakin a sama ( royal suite ) inda ya saba zama idan ya zo otel ɗin yayin da direba yayi tafiyar sa inda sauran abokanan aikin su suke ,  ya bar masa mukullin tare da motar , '

Bayan yayi wanka ya sallaci isha'i , misalin ƙarfe takwas da rabi ya sauko ƙasa , ɗakin da suke ya tasamma , ƙwanƙwas musu ƙofa yayi ,

Hajja me wurya tana sallar isha'i lokacin , falmata kuwa ta idar tana kwance bisa faffaÉ—an gadon ta sanya baby mama a gaba wacce take ta baccin gajiya bayan an cika mata ciki da madarar ta me É—umi ,

Sake ƙwanƙwasa ƙofar yayi a karo na biyu yana sake kallon number ɗakin da take rubuce a jikin wani ɗan katako dake sakale a jikin ƙofar  ,"nan ne dai ɗakin nasu ,"

Miƙewa zaune tayi
    Hajja kamar ana buga ƙofa ko ?
Ƙyat ! Ƙyat
   Hajja ta mata alama da hannu
Oho sallah kike ?
Sake bugun ƙofar aka yi da ɗan ƙarfi da ya sanyata miƙewa a hankali bayan ta zura hijabin ta ,

Ƙasantuwar ɗakin ba wani babba sosai bane taku kaɗan tayi ta isa jikin bango , dan haka ta fara shafawa bata sha wahala ba hannun ta ya sauka jikin ƙofar, 
   Waye ne ?
   Ni ne buɗe min ƙofa
    Ta shaida muryar sa
  kama mariƙar ƙofar tayi ta murɗa sai dai bata ji alamun ƙofar ta buɗu ba ,

Ban iya ba
 
Chapter 110 · 0% Book details