← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 269

Sashe 3

Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin kuka da dushewar muryar da bata fita sosai tsabar kuka take cewa lokacin da muka fara jin harbi sosai sai mama ta ɗauki  bulama da yaana, ni kuma ta saka ni cikin randa "saboda tasan bazan iya gudu da sauri ba dan bana GANI " ta ce min zata kai su yaana gona ta boye su ta dawo nima ta ɗauke ni , shine har yanzu bata dawo ba, Yakaka ina baban mu ? Ki kaini gurin sa ya nemo mana mama da su yaana ,,, ina jin tsoro dazu naji mutane har gida suna neman mu inajin ihu a gidan su modu da gidan su yanziye naji suna ihu da cewa wuta wuta , ana ta kuka da salati ina ji ana harbin mutane , meye yake faruwa yau a garin mu ?

Jin shiru ya sa falmata ta fara lalube har ta kama hannun yakaka wacce tun da  falmata ta fara bayanin take kuka , kukan mutuwar mahaifin su , da batan mahaifiyar su da ƙannen su , kukan tausayin falmata da take MAKAUNIYA , marar gata marar galihu , daman gatan su Allah sai kuma iyayen su to gashi sun rasa su a lokaci ɗaya , ba iyaye kawai suka rasa ba har da dangin su ƴan uwa , makota da abokan arziki , gidan su da garin su baki ɗaya , dan ko ba'a fada musu ba ta san garin su ya tarwatse , hakan yana nufin sun rasa kome nasu .

Wani irin kuka me karfi ne ya kwace mata ta sake rugume kanwar ta tsam-tsam tana jin bata da kowa bata da kome sai Allah sai *FALMATA KANWAR TA* ,

Kukan su ya tsannanta lokacin da yakaka ta gama sanar da falmata  kome game da mutuwar baban su  , kuka suke an rasa me rarrashin wani a tsakanin su , ga wani irin mugun tsoro da zukatan su ke ciki na rashin jin motsin kowa a unguwar su kusan ma garin nasu baki daya , ga baƙin hadarin da ya hado bakikkirin wanda ya kara wa sararin samaniyar garin da dare ya riga yayi duhu sai walkiya da cida ,alamun ruwan sama gaf yake da fara zuba .

A hankali yakaka ta É—ago falmata daga jikin ta tana share mata hawayen da suke zubowa daga gurbin idanun ta wanda idan ba an fada maka ba ko kuma ka lura kaga yadda suke tsaye kem alamun basa amfani uwa uba kagan ta tana lalube , baza ka taba cewa bata gani ba domin tar idanun ta biyu suke a buÉ—e ,ko meye sanadin makantar ta ? Ko haihuwar ta aka yi da shi ?

Ɗaga kai tayi ta sake kallon sama tana tunanin ina zasu samu mafaka daga dukan ruwan saman da yake daf da tsugewa , da sauri wata dabara ta faɗo mata cikin dusashiyar muryar  tace falmata muyi sauri muyi sallah  kin ga ruwa za'a fara ke kuma kin san kina rashin lafiya idan ruwan sama ya doke ki "zazzabi da mura"  dan haka idan mun idar da sallah sai ki koma cikin randar ki bani hijabin ki na haɗa da zani na na rufa a bakin randar sai na daura murfin "wani ƙuzajjen farantin kwano ne" na rufe ki a ciki zuwa lokacin da ruwan zai tsaya sai musan in da zamu yi .

gƴada kai kawai falmata tayi , cikin sauri-sauri suka yi alwala suka duddungura sallolin su wanda kana gani kasan akwai ƙarancin ilmin addini a tare da su, ko kafin su gama an fara yayyafi da karfi da ya sanya yagana yanke doguwar addu'ar da ta fara ta kama hannun ƙanwar ta tare da kama mata ta koma cikin randar  .

ko kafin ta gama toshe mata bakin randar ruwan ya riga ya tsinke, cikin hanzari ta gama rufewa ta tsugunna a bakin randar daga ita sai rigar ta da É—ankwali sai kuma siket É—in ciki, haka ta takure jikinta ruwan nan yana dukan ta , ta É—aura kanta akan gwaiwar ta hawaye yana sauka a idon ta tare da zubar ruwan saman da yake sauka a fuskar ta yana wanken hawayen da yake sauka, bakin ta É—auke da addu'o'i iri-iri da take yin su cikin yaren ta.

Ruwan saman sai yayi kamar zai tsaya sai kuma ya sake tsugewa , a hankali sai da tsakar gidan su ya cika taf da ruwa, " kamar yadda ya saba" cikin karamar muyar falmata ta ankarar da yakaka wacce ta yi nisa cikin tunani har bata jin yawan ruwan da ya haura idon kafar ta ,"ruwa ya fara shigowa cikin randar yakaka,' cikin tashin hankali da sauri ta zame dankwalin kan ta ta matsa ruwan jiki ta sa dankwalin ta toshe hudar jikin randar da ruwan ya ke tsiyaya ciki ta ɓulin,

Ta sake tsugunnawa gami da takure jikin ta cikin jin matsanancin sanyi da wani ciwon kai da suka dirar mata lokaci daya , hakoranta sai karo da junan su suke tsabar karkarwa,
a hankali ruwan ya fara tsagaitawa bayan kwashe kimanin awa daya da kusan rabi ana tsugawa , sai iska me karfi da matsannancin sanyi ne yake busawo tare da sauran feshin ruwan saman .

*************

   *MARAƊi Niger République*

Jihar maraÉ—i itace cibiyar kasuwanci a kasar Niger wacce Allah ya albarkace ta da masana'antu , masu kudi, da ma'aikata sanan kuma tana daya daga cikin garuruwa na kudancin Niger karkashin manyan garuruwan kasar hausa kuma ta kasance karkasin mulkin katsina shiyasa ma ake mata lakabi da katsinar maradi domin katsina ta mulke ta tun lokacin yakin kasar hausa kuma hasalima yanzu idan za a kira sarautar maraÉ—i sai ance sarkin katsinar maraÉ—i.

Kenan zamu iya cewa maraɗawa katsinawa , tun asali Maraɗi tayi yake yake sosai a kasar hausa inda taci nasarar wasu garuruwa wasu kuma su ka bata kashi amma dai tarihi ya nuna bamaraɗe jarumi ne kuma baya tsoro wanan shi yasa ta bunƙasa har zuwan turawan mulkin malaka a kasar hausa inda  suka sha gwagwarmaya da turawa a wancan locakin ,a zamani sarkin katsinar maradi tsakanin shekara ta 1892 zuwa 1894 .

Bayan jihadin sheik usmanu fodio inda ya yaki sarakunan kasar hausa ya kuma jaddada addinin islama a wanan nahiyar ya kuma canza sarakuna da dama musaman wadanda suka bijirewa kaidodin sa maradi ta shiga cikin jerin kasashe da wanan abu ya ritsa da su
Kuma tasamu sarakuna 23 Tun daga kan Sarkin katsinar maradi  Dan kassawa 1817, 1830
Har izuwa kan na yanzu .

Wannan kenan

Cikin Tafkeken falon wanda yake É—auke da kayan ado da alatu , irin wanda ake samun su kaÉ—ai gidan sarakai ,cikin masarautu irin namu na gargajiya ,

Mutane biyu ne cikin falon Mutumin da kallo daya za'a yi masa a hango girman cikar kamalar sa ,kasaitar sa da mulkin da ke gare shi yana zaune kan É—unÉ—umemiyar kujerar da take ware daga tsakiyar falon tana fuskantar duk me shigowa cikin falon .

Gefe da gefen kujerar ƴan kananun teɓurin gilas ne dayan teburin saman sa ɗauke yake da ƴaƴan itatuwa nunannu lafiyayyu tun daga kan inabi,ruman ,zaitun,tuffa,tanjari, da sauran manyan ƴaƴan itatuwa masu daraja , ɗayan teburin kuwa ɗauke yake da wata kyakkyawar butar  shayi da take kan wani babban farantin da suka zo tare ruwan zaiba tare da kananun kofunan ta da chokulan da daga  gani du tare suka zo ,

Daga kasa kuma tsakanin kewayen manya-manyan kujerun da suka yiwa tafkeken falon ado , wani dogon saurayi ne wanda bayan sa kawai za'a kalla a gane tsawo da cikar halittar sa ta ɗa namiji kansa a sunkuye ,kafafun sa a tanƙwashe yayi zaman raƙumma gaban wannan mutumin yana sauraran duk wasu kalamomi da suke fitowa daga bakin sa ɗaya bayan ɗaya , da yake cewa ,

YOUSSOUFA na samu sakon bukatar da Ka zo da shi ,sai dai ina bukatar jin ƙarin bayani daga gare ka ,? Cikin kwantar da murya wanda aka kira da youssoufa ya ce ranka ya dade kamar yadda na fada wa jakadiya , wani aiki ne ya taso daga gwamnatin kasar nan wanda ta zabi sojoji kimanin dubu ɗaya da ɗari biyar,  ta kuma wakiltani a matsayin shugaban su da zan jagorance su zuwa kai tallafin gaggawa ga yankin makociyar mu kasar Nigeria akan ƴan tawayen nan na boko haram da suka addabi yankin arewacin kasar wadda idan muka yi wasarere mu ma annobar tana iya shafar kasar mu nan Niger saboda boda da makoftakar da muke  da juna ta kurkusa ,ya ɗan tsagaita gami da ɗaga kai ya kai kallon sa ga fuskar mutumin da ya zuba masa ido yake saurarar sa da dukkan hankalin sa.

Sake sunkui da kai yayi gami da cigaba da cewa shine nake neman alfarma akan a ɗaga biki  zuwa lokacin da zan dawo wanda nake tunanin ba zai gaza nan da shekara ɗaya ba , do Allah ayi mini alfarma mai Martaba ,"ya karasa furta hakan cikin marairaicewa da kwantar da murya " ?

Ɗan gyaran murya yayi kafin yace ,wagga lamari naka da ban mamaki ike kai youssoufa anya aikin taimakon ƙasa zai wucce raya sunnah ?   ɗan jim yayi ɗaga bisani yace tashi kaje du shawarar da muka yanke tana iso maka ta hannun jakadiya ,

Ras-ras yaji zuciyar sa ta tsinke tun da Mai Martaba yace sai yayi shawara yasan bai gamsu ba bai amince da alfarmar da ya nema ba hakan yana nufin bazai amince masa ya tai zuwa nigeria  wanda kuma hakan yake dai-dai da rasa aikin sa da tun da yayi wayo a duniya ya san soja ya kasance  bashi da wani burin  da ya wuce ya zama SOJA , duk da kasancewar sa ɗan sarki kuma BIYAMARADI , haka ya dunga kawar da duk wasu kalubalen da zasu shiga tsakanin sa da cikar burin sa ya shaa gwagwarmayar da ta kawo sa kan matsayin da yake na yanzu me amsa cikakken sunan COLÓNEL YOUSSOUF ABDOUL AZIZOU BASKORE !!!!!!!....
[6/24, 9:49 AM] +234 701 013 7848: Fikrah writers association

*MAFARI.......* ( _HARGITSIN RAYUWA_ )

             *Umm'muaz*

2

Cikin sanyin jiki tare da rashin kuzari yake takawa yana wuce zauruka da sashi sashi kamar yadda aka San tsarin ginin masarauta yake.
Chapter 3 · 0% Book details