Sashe 259
Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ga tunanin sa Momy Kori zata ajiye Sofi a gaban sa ta mata ko da 'yar nasiha ce tunda Baban su baya ƙasar yayi tafiya amma ga mamakin sa ko addu'a Momy Kori bata musu ba .
Mamakin sa bai ƙaru ba sai ma lokacin da suka ta shi tafiya yaga Momy Kori ta sa an kinkimi Manyan kulolin abincin nan ta ce wai a kai masu mota su tafi da abincin idan ya so gobe da safe sai Sofi ta ɗumama masa yayi breakfast .
Mamakin sa bai ɓuya ba yace "Momy ɗumamen abinci kuma.? Da Allah a mayar da abincin nan a bayar ga masu aiki .
Momy Kori za tayi magana Sofi tayi saurin katse ta "eh Momy a mayar da abincin nan Doctor fa baya cin abincin da ya kwana .
Wani kallon yatsutsu Momy Kori tayi mata kafin ta kaɗa kai ta ce "to ai shikenan kowa rai ya yiwa daɗi bayan mai shi kai kuma My Son ka bar daɗi tunda baka cin ɗumame sannu ka ji baƙin bature .
Daga haka tayi juyawar ta cikin gida su kuma suka shige mota .
A hanyar su ta komawa gida Sofi sai shisshige masa take tare da bayyana masa zallar ƙewar sa da tayi .
A can-can yake amsa mata saboda ba wai ya huce bane gaba É—aya.
Bai ankara ba ya ji ta faɗo mai jiki gaba ɗaya ƙiris ya rage kan motar ta kufce masa yayi saurin gangarawa gefen titi.
Ransa a matuƙar ɓace ya waiga yana kallon ta "Sofi wanne irin shirme ne wannan ki...
Bata ba bar shi ya ƙarasa abunda yake son cewa ba sakamakon haɗe fuskar ta da tayi da ta shi.
Sun ɗau lokaci a haka kafin ya zame fuskar sa bai ce ma ta kome ba ya fara ƙoƙarin tada motar yana dai-daita nutsuwar sa '
Ba sabon abu bane a wajen sa Sofi ta nema shi da kan ta amma yau sai ya ji sam bata wani burge shi ba kamar baya , har ji yayi tana ɗan ba shi haushi-haushi , ya fara sabo da yadda ake ɗan jaa masa aji yana nema ana ɗan nan-noƙewa ana zille masa hakan yana ba shi nishaɗi tare da sa shi ya ji cewa lalle fa shi Namiji ne .
"Sofi ki bari nayi driving please kar ki sake taɓa ni.
Bata amsa masa ba illa wani shaiÉ—anin murmushi da take jifan sa da shi tana wani kashe masa ido É—aya .
Lokacin da suka ƙarasa gida Sofi ta riga Doctor Hamza sauƙa a motar dan haka ita ta riga shi takawa zuwa wajen ƙofar kai tsaye ta miƙa hannu ta ƙwanƙwasa ƙofar da ƙarfi
Yakaka wacce take zaune zaman jiran su zuciyar ta ta doka da ƙarfi dan sanin bugun ƙofar ko na waye .
A hankali ta miƙe ta ƙarasa gaban ƙofar kafin ta buɗe sai da tayi addu'a sannan ta miƙa hannu a hankali ta buɗe ƙofar .
Kallon-kallo aka yi a tsakanin su kafin Yakaka ta ƙalato murmushi ta ɗora akan fuskar ta dai-dai da ƙarasowar Doctor Hamza ta ce "Anty Sofi sannu da zuwa .
Sofi wacce fuskar take ɓoye yanayin halin da zuciyar ta take ciki ta miƙa hannunwan ta duk biyu ta rungumo Yakaka.
"I miss you so much Lil how are you?
Ta furta hakan kafin kuma ta sake ta tana mai tura ta baya ta samarwa da kan ta hanyar shiga gidan ta wuce kai tsaye ba tare da ta sake kallon Yakaka ba.
Yakaka bata dawo nutsuwar ta ba sai da ta ji sanyin hannun Doctor Hamza ya riƙe nata hannuwan "Wafaa mu shiga ciki .
Cikin wani irin yanayi Sofi take bin gidan da kallo kamar an sauya mata shi ta ko'ina ƙamshi ne ke ta shi shiru falon sai ƙira'ar kur'ani da ke fitowa ta sifuku .
Akan kujerar da ta saba zama nan ta zauna tana harɗe ƙafafu ta miƙa hannu ta ɗau Remote tana ƙoƙarin sauya tasha .
A ɗarare Yakaka ta zauna a kujerar da take kusa da ƙofa shi kuma Doctor Hamza kai tsaye ya wuce ɗakin sa .
"Anty Sofi ina wuni.? Ya Su Momy ?
Yakaka ta furta hakan tana kallon Sofi .
Wani irin ɗago kai Sofi tayi ta tsattsare ta da ido tsawon daƙiƙai fiye da hamsin irin kallon da take mata ya kaɗa mata ciki har yasa ta nemi diriricewa .
Wani mummunan tsaki Sofi ta jaa da Yakaka ta ji shi har tsakiyar kan ta .
Lokaci É—aya ta É—auke kan ta a fusace tana kaÉ—a kai.
Nan take ta tunanin kama kan ta ya faɗo mata dan haka bata sake cewa ƙala ba sai ta ɗau wayar ta .
Zaman shirun da yake cike da ƙosawa daga ɓangaren su duk biyun ne ya miƙa suna jiran fitowar Doctor Hamza wanda sai da ya shafe fiye da mintoci talatin dan kuwa bayan wanka da yayi sai da yayi sallolin sa na shaf'i da watir .
Sannan ya fito falon ya same su kamar wasu gumaka , ita Yakaka kan ta yana ƙasa tana amfani da wayar ta ita kuwa Sofi sai sauya tasha take , bayan ya musu Sallama bai ɗau lokaci ba ya musu 'yar gajeruwar nasiha da ƙare ta da gargaɗi tare da hannuka mai-sanda ga Sofi kan cewa babu shakka shi ba zai sake ɗaukar raini ko rashin kunya tare da neman fitina ba dole ne kowaccen su ta zauna da 'yar uwar ta lafiya a ƙarshe ya sake musu batun rabon kwana inda ya tabbatar da yin ƙwana ɗai-ɗaya a matsayin ranakun girkin kowaccen su '
Bayan gama nasihar sa da dukkanin su suka nuna Amincewar su tare da ɗaukar gargaɗin sa ita Yakaka miƙewa tayi bayan ta musu Sallama.
Taku ɗaya tayi shi ma Doctor Hamza ya miƙe , yana yin taku ɗaya ya riƙo hannun ta da yazo dai-dai da jin sauƙar hannun Sofi da yayi a cikin ɗaya hannun nasa.
Yakaka tana juyowa idanun ta suka sauƙa akan hannun sa da Sofi ta riƙe wani abu ta ji ya soki zuciyar ta da yasa da sauri ta zame hannun ta daga cikin na shi .
Ba tare da ta sake juyowa ba ta nufi É—aki tana shiga ta murÉ—a É—an makulli ta rufe .
Jikin ta kamar babu lakka ta samu wajen zama a bakin gado .
Bata ankara ba kuka ya taho mata ta kai hannun ta biyu ta toshe bakin ta .
Ta kasa sanin dalilin da yasa zuciyar ta ke ƙonewa bayan kuma ba yau ne ba rana ta farko da Sofi ta fara riƙe Doctor Hamza a gaban ta amma a baya bata taɓa jin irin yadda take ji yanzu ba ko me yasa ?
Kukan ta chak ya tsaya lokacin da ta ji ya taɓa ƙofar cikin kwantatciyar muryar sa yake ƙiran sunan ta .
Shiru tayi ba tare da ta amsa ba "Yau lokacin Sofiya ne Yakaka kar ki aikata abunda idan aka aikata miki ba za ki so ba.
Zuciyar ta ta mata gargaɗi mai kama da tunasarwa , dan haka taƙi yarda tayi ko da ƙwaƙƙwaran motsi haka tana jin sa ya ɗan yi mintoci biyu zuwa uku yana taɓa ƙofar kafin ta ji takun sa yana barin wajen .
Silalewa tayi ta kwanta ruwan hawayen idanun ta na hagu na shiga cikin na dama .
****
Washegari da safe lokacin da Doctor Hamza ya sauƙo daga ɗakin Sofi a kitchen ya tarar da ita tana aikin ta hankali kwance duk yadda ya so ya hango wani sauyi a tare da ita bai ga ko alama ba daga yadda take masa bata sauya ba .
Sai ya ji ta saƙe ƙima a idanun sa ƙaunar ta kuma ta sake ninkuwa a zuciyar sa babu shakka managarciya ce tana kuma da dattaku.
Shi ya taya ta suka ƙarasa aikin kafin a gurguje ya shirya kafin ya gama shiri ta haɗa musu abin karyawa .
Yana gaf da kammala Breakfast Sofi ta sauƙo yau dai da alama ta ji faɗan Doctor domin doguwar riga ce a jikin ta mai faɗi wacce bata ƙarasa ƙasa ba ta tsaya gaba kadan da guiwar ta sai hula da ta sa ta rufe kan ta .
Kadaran-kadahan ta amsa gaisuwar Yakaka kafin tace mata "zuba min abincin na ga ko zan iya ci .
Da sauri Yakaka ta É—au faranti ta zuba mata abincin butter chicken ne tare da khubsa.
Tun Sofi tana ci tana wani gatsine-gatsine har dai ta sau jiki daÉ—in girki ya kwashe ta ta buÉ—e baki tana wurga loma bayan loma .
"Doctor wannan Butter Chicken É—in kamar daga HH Continental aka yi order ko? Dan naji irin dandanon girkin su ne.Â
Ta gefen ido ya dube ta dai-dai lokacin da yake miƙewa ya ce "Ni da nake da Mata kamar Wafaa yaushe zan tafi yawon gidan sayar da abinci ai wannan ya zama tarihi sofiya .
Hannun Yakaka ya kama "Wafaa mu je ki min rakiya ni zan tafi .
Sofi tana son miƙewa amma daɗin abinci ya danne ta dole tana ji tana gani Yakaka ta tafi raka Doctor Hamza ita tana kai lomar girkin Yakaka.
Bayan ta dawo daga rakiyar sa ta tarar Sofi ta gama cin abincin ta bar kome a wajen ta koma kan kujera ta hakimce .
Bata gaji ba ta tattara kwanukan ta kai kitchen ta wanke .
A É—arare ta dawo falon ta zauna akwai wani series ne da take son kallo da bata samu damar gani ba jiya ta san suna maimaitawa da safe .
Tana zama ta ji Sofi ta jaa wani ƙaton tsaki.
A hankali ta miƙa ɗaga idanun tana kallon ta irin mummunan kallon jiya shi ta hango a idanun Sofi .
Har ga Allah tsoron yanayin kallon take domin kallo ne irin na hatsabiban mutane mugaye , kallo ne da yake ɗauke da saƙonni masu zafi tare da ƙaƙƙarfan gargaɗi .
Ciɗak¡ ta miƙe bata tsaya ba sai ta wuce ɗaki tana jin lokacin da Sofi tayi wata ƙwafa mai ƙarfi .