← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 269

Sashe 52

Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamar a majigi ya ji al'amuran da suka faru gare shi tsawon yinin jiya sun fara komawa baya suna giftawa ta cikin ƙwaƙwalwar sa tare da hotuna ," har zuwa kan al'amuran da suka gudana tsakanin sa da yarinyar da take gaban sa a yanzu ,"

  Wani irin sufa yayi ya wawuro yakaka wacce ta cika tayi fam ta tsattsare shi da ido ,"

    Riƙe ta yayi gam ,!

Yarinya yi gaogawa sanar da ni mafalki muke faɗa mini ba gaske bane ni nayi tarayyah da ɗiyar mutane ta hanyar banza , ki ce mafalki ne, ya ƙarasa zancen yana jijjiga ta .
    Gaba ɗaya ya shiga ruɗani ji yake tamkar ya haukace yana son ya gano wace masifa ce ta kunno cikin rayuwar sa daga jiya bayan wacce yake ciki na shan burkutu? Shi bai sha'awar zina hasalima yana ƙyamatar masu yin ta ," wani tsoro ne ya ziyarce shi da ya sa shi angaje yakaka lokacin da ya tuno da girman laifin sa wurin ubangiji ," zuwa yanzu ya gama tuno da kome da ya faru da shi  ,"

Bai san lokacin da ya fashe da kuka ba da dukkanin karfin sa , kuka yake babu kakkautawa ,"ji yake kamar ƙasa ta tsage ya shige cikin ta ," zuciyar sa ke sake raɗa masa ya tabbata mutumin banza gafalalle lalatatce , "

Cikin mamaki tare da shakkun samuwar cikakken hankali a gare shi yakaka ta ware ido tana kallon sa tare da nutsuwa cikin shirin ko ta kwana idan ya kawo mata chafka ta daka tsalle zuwa waje ,"

Sai da yayi kukan sa mashi'i cikin ransa kuwa ya rasa takamaimai addu'ar neman tuba da zai yi kowacce ya kamo sai ya ji ta tayi ƙanƙanta wurin rokon Allah akan yafiyar zunubin da ya aikata ," chak ya tsaya da kukan lokacin da ya tuno da dauɗar da ke tare da shi ,"

A sukwane ya nufi kofar da bai da tantama ta banɗaki ce ,"ba tare da ya kuma kai duban sa ga yakaka ba wacce take ɗosane a gefen gadon tana ƙare masa kallo ,"

Maimaita wankan tsarki yake yana kuka , sai da ya gaji dan kan sa ya sanya tufafin sa gami da fitowa ,"

Karaf suka haÉ—a ido da yakaka wacce ta zubawa kofar banÉ—akin ido tamkar mai tsumayin fitowar sa ,"

Kallon ta yayi na ƴan wasu dakikai da idanun sa da suka yi jawur ," cikin ran sa yana gorantawa kan sa yanzu wannan ƴar ficiciyar yarinyar da bata wuce merama ba ita ya saukewa larurar sa ,'? Shin wai ma meya sa ita yarinyar nan bata yi masa turjiya ba yana tune da shine mutum na farko da ya fara tarayyah da ita , shin ko ita ma abun da ya faru da shi ne a jiyan ita ma ya faru da ita ? Toh amma kuma ai ita ta so taƙi yadda da shi sai dai a ƙurarren lokaci ne , har yanzu yana tuno amsa kuwwar kalmomin ta waɗanda suka gaza tasiri wurin daƙile shi ga aikata abun da yayi niyya a jiya da yanzu kuma kalmomin suka zama tamkar ɗigar ruwan dalma a kunnuwan sa , bai ko son tuno da su ," ko ma menene ita ma tana da nata laifin a wurin shi na yadda ta gaza yin hoɓɓasa wurin dakile fadawar su ga halaka ,"

Tsaki ya ja tare da auna mata harara , ki tashi na maida ki inda na É—auko ki ,!

Tafiyar kuramen suka sake yi babu um ba a ah ," kowannen su yana sauraren taÉ—in zuciyar sa ,

Ga yakaka ita har yanzu bata daina mamakin mutumin da bata kai ga sanin ko da sunan sa ba har zuwa yanzu , bata wani jin nadama koh damuwa akan halin da suka kasance ciki tare idan aka É—auke É—an raÉ—aÉ—in da take ji a jikin ta,

dalili shine bata kai ga sanin girma tare da darajar budurcin ta ba , rayuwar kaɗaici suka taso a ciki , ko a garin su a ware suke cikin jama'ar gari sannan mahaifiyar su bata yi wani yunƙuri wajen nuna musu girman budurcin su ba , basa makaranta illa mahaifin su da yake koyar da su karatun sallah a gida ,"

Chan wani saƙo na zuciyar ta kuwa yaba gayu tare da gogewar biyamuradi yousouf take har ma take jin yana matuƙar burge ta , hakan ya sa take yawan satar kallon sa zuciyar ta na tuno mata da mahaukaciyar soyayyar sa da ya gwada mata a daren jiyan tamkar zai cinye ta ,'

Ga biyamuradi youssouf kuwa tunane-tunane barkatai cikin kan sa har ya rasa takamaimai na kamawa , shin yaya iyayen sa zasu ji lokacin da labari ya isar musu na irin lalacewar da yake ace wai bayan shan barasa shi youssouf har neman mata ya fara yi yayi nadama da bai amince an ɗaura musu aure shi da maimouna ya taho da ita ba da duk wannan masifar bata auka masa ba da bai lalata ƴar mutane ba shin yaya shi zai ji lokacin da wani abu makamancin wanda ya aikata ga ƴar yarinyar nan ya faru akan meramar sa ?? Runtse ido yayi yana mai jin nadama na sake lulluɓar sa , yayi nadama kuma yana alƙawartawa kan sa ba zai sake yi ba ,  burkutun da kan ta a yau yana jin wani irin karfin imani da ya jima bai ji irin sa ba akan barin shan ta, ya bar shan burkutun ma , zai yi nesa da duk wasu manyan zunubai tare da yaddar Allah ,

Yana tsayuwa ya juyo ya dubi yakaka wacce daman shi take kallo , suna haÉ—a ido ya murtuke fuska ,

Duk wasu kuɗaɗe da suke aljihun sa na niger da nigeria sai da ya tattaro su  ya zube su akan cinyar yakaka , " maida hannun sa yayi kan Steering ya ɗauke kan sa da nuna alamun yana jira ta fitar masa a mota ne ,

A hankali yakaka ta É—ago kai tana kallon sa bayan ta kalli kuÉ—in da ya zube mata su a jiki , kuÉ—in na menene ? Wani abu zata sayo masa ? toh amma ai waÉ—annan kuÉ—in sun yi yawa a sayan abu a dai unguwar nan tasu , anya anya kuwa mutumin nan kan sa É—aya , ???

Ta wutsiyar ido yaga irin kallon shakkun da take yi masa wanda ya fassara shi a kallon rainuwar yawan kuɗin da ya bata , dan haka ba tare da yace ƙala ba ya sunce agogon hannun sa na ɗanyen farin azurfa da aka ƙawata shi da ƙananun duwatsu masu daraja , ya ɗora mata akan kuɗin ,

    Idan kin ka saida shi kudi ne me tarin yawa ," ki gaugawar fita ina da tafiya mai nisa a gaba na ,"

  Cikin in-ina yakaka tace

Me zan sayo maka da kuÉ—in toh ?

Wani kallon baki da hankali biyamuradi youssouf ya wurga mata ,"

  Kuɗin biyan ki taimakon da kika min ne , ki fita ni zan tafi ,"

Toh ai wannan kuɗin sun min yawa babu abunda zan yi da su ta furta hakan tana mai sauke masa kudaɗen tare da agogon nasa agefen kujerar ta saka kafafu da nufin ficewa a motar kamar yadda yake buƙata ,"

Wata razananniyar tsawa ya daka mata

   Ke bani son sokonci kwashi abun da na baki kiyi tafiyar ki , bana so na sake ganin fuskar ki ,"

cikin ran sa yana jin takaicin yarinta tare da rashin wayewar ta da take nuna masa a fili wanda yake sa shi ƙara ganin laifin sa tare da zubewar ƙimar sa wai ace kamar shi ya haiƙewa ƴar yarinyar da bata ma kai ga sanin kan ta ba a matsayin mace," wannan abun kunya agare shi dayawa yake ,'

Yadda yayi maganar cikin hargagi yasa ba shiri yakaka ta kwashi duk abunda ya bata ta naÉ—e cikin zanin rufuwar ta da ta tafi da shi a jikin ta jiya ," cikin sauri ta sauka daga motar

Bata yi taku biyu ba ya jaa motar a zabari ya bar harabar wajen yana mai jin yadda bugun zuciyar sa ya fara sauyawa tare da iya adadin nisan tazarar da yake yi da yarinyar ,"

Jiki a sanyaye yakaka ta juyo cikin gida tana mai jin yadda wani abu mai kama da rashin jin daɗin rabuwar su a wannan lokacin yana mamaye ta bata ƙi ba ya zauna tayi ta kallon sa ita dai yana burge ta ɗan gayu ne bugun farko .

Biyawa ta fara yi ta É—akin samy baby domin ta ajiye kuÉ—in da ya bata amma sai ta tadda É—akin a datse da kwaÉ—o ga alama samy baby bata kwan a gidan ba ,

Zubawa Kuɗaɗen ido tayi tana kallon su kuɗaɗen suna da yawan da ita bata san adadin su ba , ta san suna buƙatar kuɗi ko domin su jaa jari kamar yadda suke da ƙudirin yi , to amma ina zata boye kuɗin ba tare da wani ya gani ba , samy baby tayi niyyar baiwa ajiya ita kuma ga shi bata nan , tana da tabbacin idan har ta shiga da kudin cikin gidam madam saly ta ƙyalla ido ta gan su , raba ta da su zata yi ,

Hannu ta sa gami da ɗaukar agogon da yake ta ɗaukar ido a hasken ranar hantsi , tsaruwar agogon ya burge ta ko ba'a faɗa mata ba kuma ko da ta kasance bagidajiya ta san wannan agogon mai daraja ne , bare mamallakin agogo da bakin sa ya ce agogon mai kuɗi  dayawa ne ," shin har taimakon da tayi masa ya kai ya bata wannan agogon da dukkanin kuɗaɗen sa ?  Watakila shi ɗin mai kirki ne ,

ÆŠaga rigar ta tayi ta soka agogon a bakin zanin ta tare da gyara É—aurin zanin gam-gam ,

Burum aka shigo Æ´ar kewayayyiyar rumfar katakon da samy baby tayi a gaban É—akin nata ,"

A firgice yakaka ta É—ago kan ta tana mai kokarin boye kuÉ—aÉ—en hannun ta ,"
Chapter 52 · 0% Book details