Sashe 126
Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Na ku nawa ne ? nawa kuka ɗauka a wata ɗaƴa ?
In an bincika in an bibbiku da ɗai ɗai , har ma'aikatan zaria har ku na fi kowa , ɗan ɗan ɗaraɗanɗan .........
 Da kallo suka bi ta tsaurin idanun Rakiya ba sabon abu bane a wajen su duk kuwa da cewa su sun fita daɗewa a gidan domin ita sabuwar ƴar aiki ce da ubbo ta kawo wa siyama tun daga jahar kanon nigeria .
  Bata da kunya , bata kuma da tsoro ko kaɗan fallalliya ce ta ƙin ƙarawa .
****
Fuskar ta babu walwala ta zuzzuba masa duk abincin da yake wajen akan wani ɗan faranti me ɗaukar ido , ta tanadar masa duk wasu abubuwan da ta san zai buƙata a wajen cin abincin ta mike tana barin wajen bata bi ta kan yumna ba wacce ta ɗau murfin wani ɗan kwano tana miƙa mata tare da yi mata gwarancin ta na yara , ta wuce ta tana nufar sama ,....
  Ta ƙasan ido ya bita da kallo , ganin fushin ta a duk lokacin da maimounatu tayi masa aike ya haka ba sabon abu bane a wajen sa , siyama tana da zafin kishi shi da kan sa ya san haka , saɓanin maimounatu wacce tarin hikimar ta tare da wayo ya sa bata saurin bayyana kishin ta a fili har a fahimta ,
 Shi da kan sa yana mamakin yadda ake maimouna take sanin zuwan sa maraɗi tun kafin ya iso gida ,Ko da kuwa bai sanar da kowa zuwan nasa ba , ya haka da yayi zuwan bazata , zai zo ya tarar tayo shirin tarɓar sa na musamman kamar daman ya sanar da ita zuwan sa , hakan ya sha faruwa ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba maimouna tana iya sanin duk wani motsin sa a cikin maraɗi , wanda shi ya ɗau hakan a matsayin tsantsar kulawa , to ina laifin wanda ya kula da lamarin ka ??
   Cigaba yayi da cin abincin sa cikin nutsuwa , yana jin yadda hoton fuskar falmata ke yawo a ran sa har ya hana shi jin daɗin cin abincin so yake ya sake kallon ta, dan haka ya sake ɗaukar wayar sa ya buɗo hoton , yana sake kallo lokaci lokaci yana cin abincin sa tare da sanyawa yumna a nata bakin .
Abuja
Yau garin an tashi da hadari bakikkirin kafin zuwa hantsi ruwa ya fara sauƙa kamar da bakin ƙwarya ,
Yakaka ita kaɗai ce a gidan ƙwal , saboda samira bata kwana a gidan ba tun jiya da yamma suka fita tare da Alhaji Gali .
Gaba É—aya bata jin É—aÉ—in yanayin da ta ke ciki , gidan yayi shiru dayawa duk da dai ba shi da girma sosai , zaman shirun ya sa tunaninnika yi mata dirar mikiya ,
cikin kwanakin nan tunanin falmata da mama ya matsanta mata , ko dan karatun da ya É—an tsagaita mata ne ? Amma koyaushe cikin tunanin su take ,
  Yaya suke ? , ta san duk sun girma Falmata yanzu shekaru ishirin ne da ita babu ƴan watanni yayin da mama ta haura shekaru biyar ,
Tana begen ganin su duk da cewa samy baby tana tabbatar mata da lafiyar su , a cewar ta suns waya da Rahima wacce take sanar da ita halin da suke ciki , har ma ta ce yaya doctor ya sa su a makarantu , sai dai duk da haka tana son jin ko da muryar su ne amma anty samy ta hana a cewar ta ji daga garesu zai iys kawo tsaiko ga harkar karatun ta , zata yi rauni ta gaza maida hankali ga karatun ta , da jin hakan ya sa ta haƙurewa jin su ,
Ta bari har sai bayan kammaluwar karatun ta da samy baby ta mata alƙawarin zasu tafi maidugurin tare kamar yadda ta ɗauko ta ƙafa-da-ƙafa , ta je ta taya ta wanke kan ta a wajen falmata , yaya doctor , rahima da ma baba , ƙarshe kuma ta rungumi ƴar ta da ƙanwar ta su dawo tare nan .!
Duk da cewa a farkon zaman su da samy baby ta kasa sakin jiki da ita ganin irin yAudarar da tayi mata ta rabo ta da maiduguri da ƴar uwar ta , sai ta kasance cikin ɗari-ɗari da ita tana tunanin ko zata yi yunƙurin cutar da ita sai dai abunda ya sa ta saki jiki bai wuce yadda lokaci yayi ta tafiya ba tare da ta ga wani sauyi na gallazawa , tilastawa ko ɓatanci daga samy baby ba ,sai ma hidima da take yi da ita tare da kyautata mata fiye da zaton ta ,
Tsawon shekaru biyar da suka yi tare samy baby ke ɗauke da nawin duk wasu buƙatun ta na yau da kullum , cin ta shan ta suturar ta kuɗin magani da na karatun ta duk ta dalilin samy baby ta same su kuma masu kyau masu inganci da suka taimaka mata ƙwarai ta fannin yin rayuwa me cike da inganci da isasshiyar lafiya tare da nasarar kammala karatun ta ,
Dan haka a sannu sannu samy baby ta mantar da ita girman laifi tare da yaudarar da tayi mata , a ƙarshe ta sake shirya mata sabuwar ƙaryar cewa suna waya da rahima , falmata da mama suna lafiya , wanda a zahiri ba gaskiya bane , hasalima rabon ta da shiga maiduguri ita ma ya doshi shekaru huɗu , kuma bata tare da number rahima , ba ta ma sake biyawa ta kan rayuwar bayin Allah biyun da ta raba su da garkuwar su ba ,
Ta tsara haka ne saboda yakaka ta sau jiki ta zauna tare da ita , yadda gaba zata cimma manufar ta hankali kwance ba tare da yakaka ta sake tayar mata da bori ba !
Sai dai kamar yadda suka alƙawarta lokaci ya zo da zasu maiduguri , idan ya so bayan dawowar su sai ta shiga jami'a kamar yadda samy baby ta sake ƙwaɗaita mata a cewar ta jami'a shine mataki na gaba da ya dace da yakaka , duk a ƙoƙarin ta na son janye ta zuwa kan turba irin ta ta , da take ganin fa a yanzu lokaci yayi .
Ƙofar da ake bugu da ɗan ƙarfi ya sanya ta firgita ta dawo daga nisan tunanin da ta tafi .
Duban agogo tayi ta ga ƙarfe goma sha biyu na rana ,
 Fitowa tayi da nufin zuwa ta buɗe ƙofar da take hasashen dawowar samy baby .
  Har lokacin ana yayyafi yif-yif da alamun yau yinin na marka-marka ne .
   Da ɗan gudun ta ta ƙarasa bakin ƙofar ta zare sakatar ƙofar ba tare da ta waiwaya ba ta juya da gudun kar ruwan sama ya taɓa ta tana cewa
  Sannu da zuwa anty samy .
  Sai da ta tsallaka kan Balcony tukun ta juyo ,
   A tsorace ta kai duban ta ga mutumin da yake tsaye a maimakon samy baby ,
  Saurayi ne dogo wankan tarwaɗa yana tsaye ya zura hannun sa cikin wondon jikin sa , idanun sa sakaye cikin wani kwafcecen baƙin gilashi da kallo ɗaya za'a masa a fahimci rangwamen mutumcin dake tare da shi .
  Juyawa tayi da sauri ta tura ƙofar falon ta shiga sabods tunowa da tayi da riga da wondon da suke jikin ta na bacci da duk da cewa basu kama ta ba ko kaɗan amma kaya ne masu tsantsi.
  Kai tsaye ta shiga ɗakin ta ta fara bincikar hijabin ta ,
  Sai dai hannun da ta ji ya sauƙa a ƙafaɗar ta ya sa hantar cikin ta kaɗawa ,
 Da sauri ta jaa baya har tana gwaruwa da jikin wardrobe ,
 Idanun ta ya shiga cikin na saurayin da ta bari a waje ,
  Anty samira bata nan
ta furta haka , muryar ta na karkawa , lokacin da take ƙoƙarin zira hijabin da ta samu nasarar ɗauka ,
  Riƙe hajibin yayi da hannun sa ɗaya , yayi amfani da ɗayan hannun sa wajen zare gilashin idanun sa , mitsitsin jajayen idanun sa da suka sake shigewa ciki-ciki suka bayyana , yana bin ta da wani shu'umin kallo
  Da muryar sa irin ta mashaya , yace
 Wa yake ta samira tsahuwar guzuma ?
  Ga kamar ki gorgeous , ya ƙarasa zancen yana kai hannu zai taɓa kumatun ta ,
  Da ƙarfi ta make hannun sa gami da saurin zura hijabin ta ,
  Ni ba ƴar iska ba ce kar ka sake taɓa ni , ka fita min daga ɗaki ,
 Ɗan baya ya jaa yana yarfe hannun sa da ta buge bakin sa a ɗan buɗe alamun mamaki ,
  Baby har da duka ??
Bata kula shi ba ta haura ta kan gadon ta ta dira tana nufar ƙofa , sai dai taku biyu kawai tayi ta ji ya kamo ta ta baya ya haɗa bayan ta da ƙirjin sa ya ɗaga ta ciɗak , ya shiga juyi da ita ,
  To tunda wasan tsale tsalle kike so bari na miki hajijiyar ƙauna .
  ya furta haka yana ɓaɓɓaka dariya .
Tun ƙarfin ta ta fara ihu tana wutsil-wutsil da kafafu tare da ƙoƙarin son ɓanɓare hannun sa da ya zagaye cikin ta da shi ,
A guje samy baby da tun a tsakar gida ta fara jiyo ihun yakaka ta ƙaraso cikin ɗakin .
  Kai kamal meye haka ? kayi hauka ne ?? Dallah sauƙe ta .
  Ba tare da ya sauƙe ta ba ya ce
 Ke dallah kauce ki ɗan sakayo mana ƙofa zamu buga ƙwallo ne ni da wannan me zafin kan da tayi gigin duka na .
 Ƙarasowa tayi ta jaa hannun sa ,
  Kamal kar muyi haka da kai dan Allah ka sauƙe ta , ƙanwa ta ce fa , yaushe muka fara ƴar haka da kai mutumina ??