← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 269

Sashe 82

Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ni ina yaran na jiyan nan waɗanda na ga kun gaisa da su , su biyu yakaka da falmata aina suke ne ? Ƙira min su mana !
       Anty samira nima ban san inda suke ba fa ,
      Oh na ɗauka anan kusa suke , ?

Ah ah .

   Rahima ta amsa lokacin da take sunkutar jakar ta tana barin wajen ,
  A sarari ta fara ƙunƙuni
  Naƙi na ƙira muku su ɗin , ku sasu a gaba kuyi ta sasu aiki da aike kamar bayin ku ,ba kyau dai walakanta ɗan adam wallahi !
     Ta cigaba da tafiya tana mita ,"

Sashin doctor hamza ta nufa wurin su yakaka , a kwance ta tadda yakakar ta miƙe , falmata na zaune daga gefen ta tana matsa mata kafafun ta da tace suna mata tsuku ,"saboda wahalar aiki da kai kawon da tayi kwanaki biyu da suka wuce ,"

Yau har sun É—an yi kyaun gani daga jigatar aikin da suka sha ," tun safe basu fita a sashin ba rahima ita ta kawo musu abinci suka ci anan suka yi wanka , amma kayan jikin su suka maida domin rahimar tace musu su bari sai anjima idan an kusa fara wushe-wushe sai su yi kwalliya su je wurin .'

Da dariyar ta ta ƙaraso ,
   Yakaka , fatima ,  wai anty samira tana tambaya ta ku nace ban san inda kuke ba ," kun san ta ne ? Nagan ku tare jiya .
    Anty samira ? Yakaka ta tambaya tana miƙewa zaune ,"
   Ko dai anty samy ?
Falmata ta sake tambayar ta ,

Ita , kun san ta ne ? Ai friends É—in ta ke kiran ta samy baby ,

Tace wai kuna ina ,?  watakila aiki take son sanya ku ,"

  Shiru suka yi aka rasa mai ƙwaƙƙwaran motsi ," samy baby tana son kawo musu matsala cikin zaman su a gidan nan ,!

   Yakaka ta katse shirun ,

Mun san ta mun yi aiki a gidan da take kafin zuwan mu nan !
  Oho toh ina ga shiyasa take neman ku ashe ta san ku ne !

*****

Karfe ɗaya cif jirgin da ya ɗebo tawagar angwaye ya sauka a maiduguri international airport , tun a Abuja tafeedah yake gwada kiran layin youssouf domin ya sanar da su tasowar su , da lokacin da zasu iso domin ƙwarai suka ƙagauta da su ga juna bayan tsawon watanni takwas da suka yi rabo da juna , sai dai wayar tana ƙara ba'a ɗauka ne ,

ji yayi hankalin sa na neman tashi domin ƙarshen wayar da suka yi a daren jiya misalin ƙarfe tara na dare youssouf ya sanar da shi ya kusa shiga birnin maiduguri , yana kan hanya .

A maiduguri international hotel aka yiwa angwayen masauƙi yayin da iyayen kuma aka tafi da su wani babban gidan da ya kasance mallakin mahaifin su hamza ,"

Tun da youssouf ya baro gidan madam saly yake cikin halin gigita da ruɗani , dakyar ya dawo da kan sa hotel ɗin da ya kama ɗaki,  ganin abun yake kamar mafarki , duk shirin da yayi kafin zuwan sa ya rushe saboda wacce yayi domin ta bata nan ta ɓata ba'a ma san inda take ba tukun ,"

gefe guda sabon gingimemen al'amarin da yake neman kutso kan sa dole cikin rayuwar sa na barazanar zautar da shi ,"cikin jikin ta da babu wanda ya danganta shi da nasa ,illa zuciyar sa da tunanin sa da suke masa rubdugu wurin tabbatar masa da babu shakka cikin sa ne , saboda me ?? Yarinyar shi ya fara sanin ta É—iya mace kuma har zuwa lokacin da ya bar ta bata tare da kowa sai shi ,"

Jayayya  yake da zuciya da tunanin sa akan lalle cikin ba nasa bane , ai ba jiya suka rabu ba , rabuwar su yanzu tsawon watanni shidda zuwa bakwai , zata iya yiwuwa bayan rabuwar su ta cigaba da bibiyar maza ne har ta ɗauki ciki ,

Sai dai sam zuciya da tunanin sa sun ƙi karɓar bangaren wannan hasashen nasa mai rauni ,"a kowacce daƙiƙa sake bijiro masa suke da dangantakar dake tsakanin sa da cikin jikin ta ,"

tsawon rayuwar sa bai taɓa shiga halin ruɗani irin haka ba , ya zama dole ya nemo yarinyar ko domin ya samu nutsuwar zuciya akan cikin jikin ta , nashi ne ko ba nashi bane  ?,"

Bai yadda ya danganta cikin da nasa ba , sai dai ya san ko da ba nasa bane samuwar cikin a tare da ita wani babban ƙalubale ne akan manufar sa game da ita da irin shirin da yayi na gyara rayuwar ta , shi bai san kome akan ta ba , amma yayi mata shiri mai kyau akan hasashen da yake kan dalilin da ya jefo ta rayuwa a wannan gidan da taje a matsayin ƴar aiki ," ko dai ta gudu a gidan su saboda rayuwar matsi da wahalarwa, ko kuwa auren dole , ko kuma tsantsar talauci da rashin galihu ya jawo mata neman kuɗi ra kowacce hanya ,"

Kowanne daga cikin dalilan nan yayi niyyar tunkarar matsalar ta ya magance mata ita , ya tsame ta daga rayuwar gidan saida burkutu zuwa kyakkyawar rayuwa ,

ya maida ta gidan su gaban iyayen ta ya gargaɗi iyayen ta akan sakaci da tarbiyyar ta idan ta kama ma yayi musu barazanar haɗa su da hukuma idan ya kama su da laifin wahalar da ita  , 

kuma ya tsaya mata tayi karatu, idan ta kama ya buɗe mata account ne ma zai buɗe mata wanda ko da ya bar nigeria saƙon sa zai dunga isowa gare ta , a ƙarshe ya bar mata numbobin wayar sa wanda a duk lokacin da wata matsala mai girma ta taso mata kowacce iri ce ta neme shi ,

Insha Allah zai magance mata idan ta kama ya tado da mutane ne ma daga chan ƙasar su zai turo , shi dai babban burin sa kar ya zamto a dalilin sa yarinyar ta faɗa mummunan rayuwar karuwanci wanda za'a dunga raba zunubin ta da shi , da ya fara lalata da ita ,"

Sai dai ashe ya makaro aikin gama kuma ya gama , ƙarshen lalacewa dai har ciki tayi ba tare da aure ba , "

Sam yaƙi ya bawa kansa dama ya hasaso kan sa a matsayin uban cikin jikin ta , " ya san tabbatuwar hakan wani al'amari ne da zai iya yin ɗai-ɗaya da farinciki na duk wani mahaluki da yake da girma cikin rayuwar sa , a karan kansa kuwa tunanin sa yayi kaɗan wajen tsinkayo irin halin da zai iya kasancewa a ciki .

Har tsuma yake lokacin da yake tunanin yadda zai sata a gaba ta kai shi har gurin É—an iskan da ya É—irka mata cikin , bai tunano irin azabar da zai gana masa ko da kuwa biyan ta yayi da amincewar ta yayi mata cikin ," a fili ya furta

   Mtss doluwar watakila shima taimakon sa tayi ,"

tsabar kan sa ya É—au chaji bai ma lura da wanda yake kiran sa ba ya É—au wayar ya danna ta silent lokacin da ya ji tana neman damun sa da tsuwwa ,"

Ya ɗauki tsawon lokaci a ɗakin yana saƙa da warwara har bai san lokaci ya tafi dayawa ba sai da ya tsinkayi kiraye-kirayen sallah daga nesa ,

Wayar sa ya ɗauka dan ya ga lokaci anan ya tarar da miss calls ɗin tafeedah dayawa , ɗan dafe kan sa da ya fara sara masa yayi , shaf ya mance da lamarin bikin ma baki ɗaya ," bin bayan ƙiran nasa yayi

mon amie kana lafiya kou ? Ina ka bar  téléphone ɗin ka ? je vous ai appelé mais vous n'avez pas répondu ,

Lafiya nake É—an ouwa , kun kai ga isowa gari ?

Muna a gari yanzou haka ,

Aina kun ka yi masauki ?

Maiduguri international hotel,  , " kai kana ina ?

Barwee hotel ,

nan tafeeda ya tambayi angon da yakasance haifaffen garin yanayin tsaro ya sa suka yi ƙaura daga garin zuwa birnin tarayya ,"  ko ya san barwee hotel ? ɗan ouwan sa da yake bashi labari chan yake da masauƙi ,

Nan take ya ce zai tura a É—auko shi yanzu idan har ya shirya ,"
  Da haka suka yi sallama bayan an sanar da youssouf tasowar driver ,

****

Karfe huÉ—u da rabi angwaye suka iso harabar gidan su amaryar inda anan aka riga aka fara wushe-wushe , dukkanin su sun yi anko na shuÉ—iyar shadda mai duhu ," kan su da jajayen hulunan dara ,"shigar su ta kanurai !

Ta ko'ina filin ya ƙawatu da adon gargajiya na kanurai , yayin da makiɗan ,"ganga kura" ( kiɗan kanurai na gargajiya )  suke tsaye daga gefe suna ta buga manyan gangunan su ga masu hura algaitun su na gargajiya suna hura ta tana bin kiɗan da mabanbanta sauti ,

Ƙamshin turaren wuta da aka sa a kowacce kusurwa na wajen yana tashi a hankali ta cikin electric burner ,"

Isowar angwayen bai ɗauki lokaci ba amaryar ma ta iso ƙarƙashin rakiyar ƙawayen ta waɗanda su ma suka yi ankon shuɗiyar shadda haɗe da baƙi ," ( danga-shaw ) sun rufe kan su da jaan gyalen ,"( mandil ),"

Amaryar kuwa wata farar haɗaɗɗiyar lafayyah ce ta naɗe jikin ta da shi ,  wuyan ta ya ƙawatu da babbar sarƙar mirjani haɗi da siririyar sarƙar gold ,"

Nan amarya da ango suka zauna a mazaunan da aka tanadar musu , yayin da ƙawayen amarya suka fara shiga filin rawa suna bin kiɗan malikii da yake tashi sannu a hankali suka fara rawa ta burgewa mai cike da ƙasaita , ɗaya bayan ɗaya abokan angon ma suka fara takawa zuwa cikin filin rawar kowannen su yana fuskantar  ɗaya daga cikin ƙawayen amaryar suna bin kiɗan tare da rawa kamar yadda tsarin rawar kiɗan malikii yake ,"
  Nan take guɗa ta fara tashi daga bakunan manyan matan wajen ,
Chapter 82 · 0% Book details