← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 211 OF 269

Sashe 211

Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Prof da Amnee basu wani damu da yadda alamun ɗan nasu ya nuna dake bayyana bai yi farin-ciki da auren da ake shirin yi masa ba , suka cigaba da yin duk wasu tsare-tsare da shirye-shiryen yadda bikin zai kasance , an riga an buga katin auren Rahima har ma an rabar , ganin cewa bikin Hamza ba na farko bane ,na biyu ne ,ya kuma zo a ƙurarren lokaci , sannan abun nasu tuwona maina ne , saboda sune dangin uwa da na uba saboda a cikin baki ɗayan dangin Uban su Yakaka har yau an gaza samo ko guda duk kuwa da cewa sau uku Khaalty Rahima tana bin sansanin ƴan gudun Hijira ko Allah zai sa ta ci karo da wasu daga cikin tsirarun dangin Mahaifin su Yakaka duk kuwa da cewar tsawon zaman su ba zaman daɗi suka yi ba , saboda karan-tsana da suka ɗora mata ita da yaranta , haka siƙau , sai dai Allah bai sa ta gamu da ko wanda ya san su ba , kai ko mutanen ƙaramin garin nasu ma Allah bai haɗa ta da su ba .

Dan haka sai basu wani damu da a sanar da dangi ba kawai suka bar lamarin a tsakanin su .

Amne ta ƙarfafa da a rufe zancen auren a tsakanin su ne saboda tsoro da take yi kar danginsu suyi wani yunƙuri na hana auren sanin da tayi tun da can daman ba ƙaunar ta suke ba ita da Rahimar ta , tayaya kuwa zasu so 'yar Rahima ta auri Hamza ? musamman da ya kasance Hamzan ai tasu yake aure 'yar yar'uwar su .

Dan haka ta dage akan a rufe zancen har sai É—aurin auren ya matso a yadda ta so ma sai sanarwar É—aurin auren kowa zai ji ,sai dai da alama hakan ba mai samuwa bane , koma menene ita dai zasu tsawaita addu'a ita da Khaalty Rahima kan Allah ya tabbatar da lamarin nan tare da Aminci

Shiri suke sosai a tsakanin su , lokaci ne yanzu na wayar tafi da gidanka , da saƙo ke saurin isa inda ake buƙata , ta waya Amnee ta sanarwa da dangin su na can N'Djamena labarin bikin da ya zama uku ba ma biyu ba , watau Hamza ,Yakaka da kuma Rahima ƙarama .

Murna ta ishe su a can nan take suma suka shiga sabunta shiri , da daman suke tsakiya da yin sa , saboda dayawa daga cikin su ,wannan karon suna shirin zuwa saboda su gana da ƴar uwar su wacce ta ɓace shekara da shekaru har aka fidda rai da sake ganin ta ,

Cikin masu zuwan har da yayun su maza da matayen su da wasu daga cikin 'ya'yan su , sai kuma dangin su na wajen uwa da na uba duk gasu nan dai gayya guda ,

Nan take labarin auren ya sake bazuwa a tsakanin su , jin cewa har da na 'yar Rahima mace da Hamza ɗan Aminatu, da za'a musu haɗin gida, nan take suka yi sabon zama na musamman , inda suka sake ninka gudummawar su da zasu tafi da shi da daman turaren wuta ne da turaren jiki na ruwa ( Humra ) har ma da na wanka da mayukan jiki da na gashi , ( kulaccan da karkar ) suka ɗau nawin yiwa Rahima ƙarama gudummawar sa ,a matsayin su na dangin uwa sai suka sake ninkawa da wani haɗin turaren wutar da humran , su kulaccan da karkar makamancin wanda yake ajiye duk suka haɗa acikin manyan mazubai suka rufe ,

Sannan suka sake ƙarawa da kayan ƙamsasa girki da daɗaɗa shi irin nasu na can , haɗi da ingantattun ganyayyaki haɗin shayi ( tea ) da suke ƙara lafiya da kuzari tare da sanya nishaɗi, shima roba-roba suka keɓence shi .

Bayan haka matar baban wan su da ake ƙira Hajje khalsum ta ƙira Amnee tana sake tambayar ko akwai kuma wani abunda suke so a taho musu da shi daga nan N'Djamena ?

Nan Amnee tayi amfani da wannan damar take sanar da ita buƙatar ta na son a haɗo mata kaya gyaran jiki tare da magagungunan mata ,irin nasu masu ɗauke da sunadaran da suke ƙamsasa kowanne saƙo na jikin duk wata matar da take amfani da shi , bayan sun mata gyara ciki da bai .

Amnee ta cigaba da cewa a faɗa mata adadin kuɗin da zai isa a kawo kayan gyaran kashi uku , kafin ta gama bayani Hajje Khalsum ta katse ta , tana sanar da ita cewa ai wannan ta kawo cuta inda ake da tushen maganin ta , domin kuwa ƙanwar ta da suke uwa ɗaya uba ɗaya , ƙwararriya ce ta wannan fanni na gyaran mata ciki da waje , domin kuwa faɗin ƙasar su ansa da ingantattun magungunan ta , babban shago ne da ita anan babban birnin N'Djamena da taƙe sayar da irin waɗannan magungunan da kayan , har kuma ƙasa-da-ƙasa ake ɗaukar ta tana zuwa gyaran jikin , tare da haɗawa mata ingantattun magunguna dan haka kada ta damu , nan da kwanaki biyar inshaAllah zasu taho tare da ita .

Zuciyar Khaalty Rahima ta daɗa cika da ƙaunar 'yar uwar ta , domin ko bata faɗa ba tasan cewa dan Yakaka ne Amnee ta ƙira Mai gyara , da daman tuntuni take son tayi wani yunƙuri akai , amma kunya da kara suka hana ta ganin cewa duk wasu ragamar bikin na hannun Amnee , sai kuwa ga shi zata sa a gyara mata Yakaka ,

Duk abunda ake na zafafa shirye-shirye , Yakaka ta maida kan ta mai zaman ɗaki , daga kuma ta samu sarari sai ta shige banɗaki taci kukan ta , tsoro da damuwa sun hana ta walwala , tuƙuru tsoron rayuwar da zata riska nan gaba kaɗan take ,

Daga Amnee har Khaalty Rahima ba wacce ta bata sarari bare ta ji damuwar ta saboda sun riga sun san ko damuwar ta mecece ?dan haka suka kyale ta suna sabgogin su ,

Ganin bata yin wani shiri , ko alamun gayyatar ƙawaye koda na mutunci ne yasa suka fara lallashin ta kan cewa " yakamata ita ma ta gayyaci mutane , ranar auren ta rana ce mai ɗimbin tarihi wacce yakamata mutanen da duk tayi ko da zaman mutunci da su ne su shaida wannan ranar ,
Yakaka tace " ita fa bata da ƙawaye , ƙawarta ɗaya Lubna kuma tayi aure , bayan ita bata da wata ƙawa , da suka matsa mata ma kuka ta sa tana cewa " Amnee Mama kun san fa irin rayuwar da muka yi , ina mutane suka mu'amalance mu da mutuntawa bare har su kai mu kusa da su ? Da zamu iya ɗorar da zumunci idan bayan Malama Maryam da Lubna babu wasu mutane ta wajena ,

sai ta basu tausayi suka bar maganar , amma daga baya sai suka sa ta ƙira Malama Maryam ,bayan sun gaisa ta miƙawa Amnee wayar dan ita kunya take ji ta faɗi ranar auren ta da kanta , ta baki da baki Amnee ta shaida mata sanya ranar bikin 'yar ta kuma ɗalibar ta ,

Ba ƙaramar murna Malama Maryam tayi ba har ma tayi Alƙawarin halartar bikin ,

basu bi ta kan Yakaka ba wacce take faman ƙwalan-ƙwalan da ido tana son sake yin wani kukan , suka yi ficewar su daga ɗakin suka bar ta , dumuwar ba zai sa a fasa kome ba , domin na ɗan lokaci ne kuma gata ne babba ake shirin yi mata .

Cikin kwanakin nan Falmata sai ta fita walwala , domin ita labarin bikin Yakaka da Yaya dakta yayi awo gaba da kaso kusan talatin na damuwar ta , duk da cewa ba wai ta daina jin damuwa da rashin ji daga Biyamuradi bane , farin-cikin auren Yakaka ne yake saisaita mata damuwar ta .

Doctor Hamza kuwa tun ranar da ya isa Abuja ya so sanarwa da Sofiya halin da ake ciki kan lamarin aure da ya taso masa , saboda hakkin ta da yake kan sa ya zama dole ya sanar da ita .

Sai dai yadda ta tare shi cike da ɗoki kamar wanda ya shekara rabon sa da ita ba kwana guda ɗaya tal ba , sai ya kashe masa ƙwarin guiwar sanar da ita labarin da yake tafe da shi sanin da yayi ba abun farin-ciki bane a wajen ta,

Sai yayi zaune kawai yana bin ta da kallon yadda take ta ririta shi tana tarairayar sa , tayi kwalliyar ta fes-fes cikin riga da siket , ta mammatse manyan kayan da yafi so tare da ita sun firfito ko yaya ta motsa suna rangaji tare da dusashe masa ƙarfin gani suna tayar masa da kwaɗayi .

Shi dan ta shi tuni ya haƙura da ya zauna tare da ita ,ita kaɗai saboda a halin zaman su na aure babu ta inda ta kuskuro shi sai ta wajen girki wanda shi kuma hakan bai wani dame shi ba saboda shekarun girma da ya fara shigo masa , a matsayin sa na likita shekara arba'in ya kamata ya fara kiyaye kansa daga ciye-ciye barkatai da sunan jin daɗi .

Rashin haihuwar su kaɗai ke ɗan taɓa ransa , kuma yayi-yayi da ita taje asibiti ya haɗa ta da kwararrun likitocin mata su duba ta taƙi , daga baya yayi watsi da ita lokacin da ya fahimci akwai wata matsala tata da take ɓoye masa , koma menene ita ta sani shi dai ya san lafiyar sa rass , domin a farko-farkon shekarun auren su yayi gwaje-gwaje da dama kan rashin haihuwar su domin gano ina matsalar take ? Ta haka suka tabbatar masa da ingancin lafiyar ƙwayayen halittar sa dan haka shi bashi da fargaban kome ,

Yawan ƙaunar da take gwada masa salo-salo yasa yake ɗaga mata kafa , domin kuwa ta san ta kan sa sosai bai wani cika murɗe mata ba muddin ta raɓu da jikin sa ,
Chapter 211 · 0% Book details