Sashe 24
Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Duk da cewar siyama bata jin yaren su na azbinawa amma ta fahimci zancen ta aka yi jin an ambaci "maraÉ—i "Â
Tunanin ta ya katse lokacin da taji hadima ngala wacce ga alamu ita ce shugabar bayin gimbiya maimouna," duba da cewa tun da gimbiyar ta fito duk sauran bayin suka kai gaisuwa tare da ficewa daga shigifar sai ita ta rage", ta ɗurkusa tana ahuwa cikin girmamawa take neman iznin ta jagorance ta zuwa wata shigifar ,"
Ware ido tayi tana me sake tsuƙe fuska ta gƴaɗa kai ," abun mamaki kunnuwan ta sai suka tsinkayo mata ngala na mata ƙirari "ɗan murmushin gefen baki tayi tana mai bin bayan ta ,"
Cak ta tsaya sakamakon sallamar sa da ta tsinta cikin amon muryar sa mai samar mata da kasala ,"
Waiwayowa tayi suka dubi juna ido cikin ido ,"dai-dai lokacin da gimbiya maimouna ta miƙe tana mai nufar sa cikin takun ta ," fuskar ta ɗauke da tattausan murmushin da duk cikin maza shi yayi zarrar samun irin sa ,"
Juyawa tayi cikin sauri ,kafin idanun ta su hango mata irin tarɓar da zasu yi wa juna wanda zai haifar mata da damuwar da zata hana ta bacci ,"
Cikin nutsuwa ta sauya kayan ta zuwa na barci bayan taci abinci ta getse ta sake yin wani wankan duk cikin ƙarƙashin kulawar gnala da take hidima da ita cikin girmamawa hatta ruwan wanka da kayan baccin ita ta haɗo mata ," yayin da a halin yanzu take kishingiɗe kan makeken gaɗon kwatankwacin nata sai dai wannan ya fi shi girma , gnala tana daga ƙasa ta miƙe bisa guiwarta tana tausa mata kafafu ,"
Tare da nazari take kallon ta tana son samo bakin zaren ta inda zata fara yi mata maganar da take son yi wato yi mata tambayoyi akan uwargijiyar ta ," sai dai kuma tana shakka akan koh zata samu haÉ—in kan gnala É—in ,"
A hankali ta murɗa kofar ɗakin gami da shigowa ƙarƙashin rakiyar sassanyan kamshin ta mai shiga zuci ,cikin sabuwar shiga mai banbanci da ta ɗazu domin a halin yanzu sanye take da doguwar rigar siliki ruwan zaiba da duwatsun jiki suke ta faman ɗaukar ido ,miƙaƙƙen gashin ta ya zubo har gadon bayan ta yayin da madaidaiciyar fuskar ta mai ɗauke da manyan fararen idanu ta faɗaɗa da lallausan murmushi ,"
Sallama tayi musu tare da zama bisa gefen gadon da siyama take a zaune bisa a halin yanzu ," maida duban ta tayi ga gnala ,"
     daɗa a bamu wuri mu zanta tare da ƙauna ta ,"
    Toh ranki shi ɗaɗe ku tashi lafiya ɗiyan saraki ,
Barka da zuwa ƙauna ta siyama kin iso lafiya ? Yaya umma da fatan kun baro kowa lafiya kun iske mu lafiya ?
Cikin murmushi siyama take amsa mata kafin daga bisani hira ta fara gudana cikin taka tsantsan daga kowaccen su ," domin ita ma gimbiya maimouna koh da ta tambayi biyamuradi youssouf wacece wacce suke tare ya tabbatar mata ƙanwar sa ce kuma sunan ta siyama ,sannan ita ma niamey ta nufa shiyasa tafiyar su ta zo guda ,"
Daga haka bai wani bata fuskar da zata sake zouwa mar da batun siyaman ba ," yayin da ita kuma hankalin ta yafi karkata ga batun tafiyar sa da yayi ta faman rarrashin ta da kyar ta amince suka rabu cikin aminci tare da alkawarin kasancewa akan wayar tafi da gidan ka a har kullum ,"
   Ƙauna ta daga shigowar ki cikin garin mu zuwa saduwar ki da masarautar mu menene yafi burge ki yafi baki sha'awa ?
  Ɗan jimm siyama tayi tana nazari "ga dama ta samu ," murmushi tayi tsarin ginin masarautar ku sosai ya burgeni , sannan na biyu girke-girken ku na gargajiya sun ƙawatar da ni kuma sun min daɗin ɗanɗano wanda har zan so na dunga samun irin girkin lokaci zuwa lokaci
   Murmushi maimouna tayi jin siyamar ta yabi masarautar su ,idan kuwa haka ne zan baki baiwa ƙwararriya ɗaya daga cikin masu min girki ki tafi da ita zuwa duk inda zaki ta dunga yi miki irin girkin mu a duk lokacin da kika biɗa ,"
Cikin farin cikin ganin tarkon da ta É—ana yayi kamuwa kuma zuwan ta yayi alfanu domin zata tafi da wani bangare na kusa da gimbiya maimouna tayi mata godiya tare da yabawa akan karamcin da tayi mata ,"
Tare da nishaɗi gimbiya maimouna ta amsa tana mai jin daɗin zuwan siyamar domin ta daɗe tana son ta samu dama irin haka da zata tura wani na kurkusa da ita zuwa maraɗi "saboda wani boyayyan dalili nata ", tunani ta fara yi cikin amintattun bayun ta wa zata tura ?
   *GNALA*
  Hasken alfijir ya fara haskowa ta tsakanin labulen tagar ɗakin nata ,tana zaune daga bakin wata doguwar kujera jal da take ɗakin nata da ta sha shimfiɗun alfarma , gefe daga ƙasa baiwar ta ce ngala
    "zaki tahi zuowa maraɗi a matsayin kyautatciyar baiwa da na ba da ki ga ɗiyan sarkin maraɗi siyama ,"zaki tahi a matsayin mai yi mata girke girken gargajiya irin namu ," zaki yi duk wani kokari ganin kin samu mazauni mai kyau wurin sabuwar uwargijiƴar ki ,"ta yadda zata sau miki jiki ki samu shiga cikin lamuran ta wanda ta haka zamu san lamuran da suke gudana baki ɗaya a cikin gidan tun kafin wanzuwa ta ,"wanda hakan shi zai sa naji saukin tafiyar da dukkanin lamurana idan naje cikin su ," ba akan mutum guda zaki sanya ido ba akan duk wasu makusanta biyamuradi youssouf , nasan tsawon shekara guda zai ishe ki kammala aykin da na aike ki ," idan na zo babu wahala zan sauyawa siyama ke da wata baiwa daban ,amma a yanzu ke yafi chanchanta da ki tahi ," ki kula sosai bana so a samu matsala zan dunga tuntuɓar ki lokaci zuowa lokaci ,"
 Cikin girmamawa da miƙa wuya baiwa gnala ta amsawa uwargijiyar ta ,"cikin ran ta kuwa tana tunanin wanne lamurra uwargijiyar ta ke son aiwatarwa a masarautar na maraɗi da har zai kai ta zaman aure da magajin garin ,????????
Kafin karfe baƙwai na safe siyama ta gama shirin ta ,an yi mata jagora zuwa sashin matan sarkin ɗaya bayan ɗaya ta kai gaisuwa inda a karshe tayi zango a fadar mai martaba sarkin agades inda nan ma ta kai gaisuwa tare da biyamuradi youssouf wanda shima yake shirye tsaf cikin shirin sa na tafiya,"
Ƙarƙashin rakiyar dogarai suka sadu da wurin da motocin su suke batare da bata lokaci ba suka shiga , sai dai a yau saɓanin jiya baiwa gnala ita ce a mazaunin mai zaman banza yayin da siyama take maƙale daga jikin kofa gefen biyamuradi wanda tun bayan gaisuwar su da ya amsa ita da gnala ɗin bai sake bi ta kan su ba bai kuma tambayi siyama wacece gnala ɗin ba ,"domin gimbiya maimouna ta gama yi masa bayanin kome ,"inda ta bayyana masa ayken ngla ɗin tayi zuwa niamey ,???( koh meyasa ta boye masa gaskiya )
             _______
Tafiya yankin azaba tabbas haka ne domin ba su suka sami isa niamey ba sai bayan magarib ," yayin da kai tsaye ya sa suka wuce gidan "ubboh" wacce tun jiyan take ɗokin zuwan ƙanwar ta mafi soyuwa agare ta ,"
Da gudu-gudun su suka fito ita da ƴan kyawawan yaran ta huɗu ," suka tarɓe su tare da jagorantar su zuwa ciki , inda ta miƙawa mai kula da hidimar gidan namiji ,"mukullin sashin da suke sauƙar baƙi ya buɗewa youssouf da muƙarabban sa sai dai biyamuradi youssouf ɗin ya dakatar da ita ta hanyar sanar mata da cewa karfe takwas suke da taro (meeting) kuma zuwa asubahin yau jirgin su zai ɗaga zuwa nigeria dan haka basu da isashen lokaci ," hakuri ya bata ganin yadda tayi kicin-kicin da fuska tana mitar bata lokutan da aka yi wurin shirya musu abinci shi da muƙarabban sa ,"ƙarshe dai dole ta sa suka kwashi abincin bayan ta sa anfito musu da shi ,suka yi sallama cike da ƙaunar junan su ,"domin duk da kasancewar su abokan faɗan juna amma wannan tsabtatatciyar ƙaunar ta tsakanin saƙo da saƙo tana nan tana gudana a tsakanin su ," koh sun yi faɗa basa jimawa suke shiryawa ba'a shiga tsakanin su ,"
Har ta ga ficewar motocin sa daga gidan tana ɗaga masa hannu zuciyar ta cike da ƙauna tare da tausayin ƙanin nata ganin irin aikin wahala da bautawa ƙasa da ya zaɓarwa kan sa ,"
Gefe guda kuma tana tinanin damuwar da ta hango kwance a ƙwarar idanun siyama cikin sassarfa ta juya gami da nufar cikin gidan ," koma meye dole zata magance mata matsalar ta saboda ita kam duniya bayan mahaifan ta bata da kamar mahaifiyar siyaman har abada baza ta mance da ƙaunar ta ba ,"
             _____
Â
Â
Karfe huÉ—u da rabi na asubahi agogon niamey jirgin su biyamuraÉ—i youssouf ya É—aga Daga "Diori Hammani international airport " zuwa nigeria ,inda karfe shiddah da mintuna arba'in suna cikin tashar jirgin sama na "Nnamdi Azikiwe international airport Abuja Nigeria ",......
Naso chapter nan tafi haka yawa, "amma ban samu dama ba, "kuyi manage da wannan din insha Allah mai yawan yana tafe, "
Koh kun San comments din ku suna kadan? 😕ku Kara ku yunkuro a tattauna ku fada min ra'ayoyin ku akan abun da yake faruwa, da ma Wanda kuke hasashen zai faru a nan gaba, Domun nishadin ku nake yi. ðŸ˜
#vote
#comments
#share
#son so
#fkrh
[6/24, 9:59 AM] +234 701 013 7848: Fikrah writers association
*MAFARI........*
( _Hargitsin Rayuwa_ )
*Ummu'muaz*
9
Misalin karfe biyu na rana ya kammala da kome da ya shafi sabon wurin da zai fara aiki inda aka tura su shi da sojojin dake ƙarƙashin sa chan tsakanin bodar da ta haɗa nigeria da niger ta cikin jahar borno ,"