← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 224 OF 269

Sashe 224

Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta waiga ga Siyama wacce take kallon ta fuskar ta cike da murmushi , "sannu ku da zuwa Mamar Yumna yaya hanya ?

"lafiya lau Fatima ƙamna ta da fatan mun cimmuku ƙalau ?

"Lafiya .

Falmata ta amsa mata a ɗan taƙaice , a mutunce suka gaisa da Aisha Mairama .

Shiru ya ɗan biyo baya kafin Asma'u ta juya ga Amnee da son jin ƙarin bayanin da take mata kan haɗin wani turarurruka ( humra )na musamman da matan N'Djamena ke amfani da shi a sassan jikin su da tun shigowar su Amnee ta tare su da tururrukan humran launi-launi cikin wasu 'yan ƙananun kwalabe da aka jera su akan ɗan wani faranti na musamman , ta basu suka shasshafa da daman haka al'adar su take na tarar ɓako da turare musamman idan baƙon na girma ne ,

Ƙamshin sun yiwa Asma'u daɗi kamar yadda ruwan turaren da kansa ya burge ta launi-launi gwanin sha'awa ga turaren ya zauna musu a jiki ko yaya suka motsa ƙamshin sake tashi yake .shine take son sanin yadda ake harhaɗa su , Amnee kuwa tayi alƙawarin koya mata .

Ita kuwa Ammi takaicin Siyama ne fal ya cika mata rai cikin ran ta cewa take "haba me ake da lusaranci irin na Siyama ? Yanzu kishiyar ce abun tarairaya da gatatawa ya haka ? Tun a can ta so a hana Siyamar tahowa saboda ita bata ga dalili ba zuwa bikon kishiya , amma Siyama ta kafa naci har da yin fushin da guntuwar ƙwallar ta , ganin haka yasa Umma amincewa aka taho da ita domin da farko ita ma ƙin amincewa tayi da tafiyar ta Siyama .

" en loi kin yi kyau sosai , ƙwalliyar ki ta burge ainun .
Mairamar sarki ta furta hakan lokacin da take baro inda take zaune ta dawo kusa da Falmata ta zauna , gani na farko da ta yi mata ta ji ta burge ta ,tana ƙaunar ta musamman da ta gan ta yarinya kamar ma zata girme mata .

"Nagode , Falmata tace tana 'yar dariya idanun ta ta sauƙe kan Yumna da aka mata Shimfiɗa da wani lallausan bargo daga gefe tana ta baccin ta da alamun gajiya a tattare da ita ,

" tayi bacci ne ?
tace da ƙaramar murya ,
Murmushi Siyama tayi tana cewa "É—iyar ki tayi baccin gajiyar hanya bata saba ba , ga shi kouma baku ko gaisa ba da alama dai yau a É—akin ki zata kwana da dare idan ta farka kun gaisa ...

"Da gaske ?
Falmata ta furta hakan tana dariya cikin zumuÉ—i ta É—ora da cewa
"bata ƙuiya sosai ko ? Ba zata yi rikici ba ko ? Tunda bata sanni ba Bana so tayi kuka .

Siyama tana murmushin jin daɗin ganin zallar ƙaunar 'yar ta a fuskar Falmata tace

" A haka zaku saba ai 'ɗiya ba ta ƙi mamar ta ba...

Kafin ta ƙarasa faɗin abunda tayi niyya Muryar Ammi ta katse mata zancen ta ta hanyar cewa .
"So kike tayi ta ihu kenan ? Wannan ai É—aukar hakki ne ki bar 'yar ki a katarar ki sai yafi alheri .

Shiru wajen yayi na É—an wani lokaci kafin muryar khaalty Rahima ta ratso wajen fuskar ta da É—an murmushi tace

" gaskiya kam bare ga baƙunta ga baƙuwar fuska abun zai zama bibbiyu , gara ta zauna a wajen Mamar ta cikin Alheri .

" Yakaka da ta lura da sanyin da jikin Falmata yayi sai tace " Falmata da son yara kike wallahi, anya ma kuwa za ki yarda a ɗau naki , zamu gani ai lokaci kaɗan ya rage ke ma ki riƙe naki a hannu inshaAllah .

Mairamar sarki ma da abunda yayar su ta ta so yi ya É—an sanyayar mata da jiki sai tace

" ai kuwa ni ce mai raino dole ma ta ba mu ɗan mu ko 'yar mu ko mon beau-père ?

Dariya Siyama tayi tana waskewa hararar da Ammi take jefo mata ta ƙasan ido tace

" É—akina ai nan ne wajen ajiyar kayan sa , ni zan dunga shirya shi , kafin a yaye shi daga an yi yaye kuma zai dawo wajena gabaÉ—aya sai dai Mamar su ta kawo mana wasu kuma .

Amnee ce katse musu hirar da suke yi lokacin da ta ce , " Aisha raka ta ta gaishe da baƙi a sashin Baban su .

Bayan dawowar su daga gaishe da su waziri Falmata bata tsaya a falon ba ta musu sai da safe kawai ta shige É—aki , tana warware lafayyar jikin ta zuciyar ta na ga tunanin bata gan shi ba ,Ina yake ? ko dai bai zo bane ?

GabaÉ—aya sai ta nemi É—an farin-cikin da ta tsinci kan ta ciki ta rasa da daman zuwa yanzu ta fahimci kusanci da shi da ta samu sanadin ganin 'yan uwansa da zaton ta tare suka zo zata gan shi shine ya sata murna .

A yanzu kuma da ta fahimci bai zo ba duk sai ta ji ƙunci na safko mata wani sashi na zuciyar ta taji yana raɗa mata , " Falmata ke fa kike damuwa da shi dan rashin zuciyar irin taki , shi bai damu da ke ba tunda ga shi ya ƙi zuwa wajen ki sai wasu ya turo wai su tafi da ke sai kace wata kaya , zuwan nasu da bai wani burge ta ba , a gurin ta da shi kaɗai tal yazo , ta gan shi suka yi komawar su tare da hakan ne zai sanyata farin-ciki akan waɗannn da aka turo ga shi tun a gaban iyayen ta ma wannan yayar ta shi sai wani hararar take , ko meyasa ta tsane ta ? Oho .
Mts
Tayi tsaki lokacin da take zama bakin gado , tana ƙoƙarin ture tunanin sa dake damun zuciya da kwakwalwar ta .

" Falmata na , ai damuwa kuma ta ƙare tunda ga 'yan uwan sa sun zo tafiya dake , za a mayar da ke gun angon ki mu huta da jin kukan ki da ganin ƙuncin ki "oh su soyayya manya .

Yakaka ta furta haka da dariyar tsokana lokacin da take ƙarasowa cikin ɗakin ,

Yamutsa Fuska tayi ta kawar da kai gefe kafin tace " waye yake cika miki kunne da kukan Yakaka bana so .

"Rabu da ita en loi , jibi war hakka kina cikin masarautar mu bayun ki na miki hidima daÉ—a ai ke É—in sarauniya ce matar Yarima ,

Murmushi su duk biyun suka yi da ganin shigowar Aisha da ta cigaba da cewa

" kun yi waya da Biyamuradi ko ? Ya jikin na shi da sauki kou ? Ni dai nan tunda munka tasso da mun ka baro shiyar ƙasar mu Téléphone carte sim pas de service .

A hankali Falmata ta É—ago kanta zuciyar tana sauya bugu , da wani yanayi a muryar ta tace " Daman ba shi da lafiya ne ? Me ya same shi ?

Da sauri Aisha ta dafe kai tunowa da tayi da farkon zuwan su a can falon Prof bayan Waziri ya yiwa Prof taƙaitatcen bayani kan rashin lafiyar Youssoufa da shine dalilin da ya kawo jinkirin zuwan su , amma zuwa yanzu lafiya ta fara samuwa gare shi da yardar Allah , a ƙarshe suka daɗa neman afuwa tare da neman iznin tafiya da Falmata a gobe .

Prof ya jajanta musu sosai ya kuma yi musu addu'o'i sannan sai shima ya shigar da neman Alfarma kan a ƙara masa kwana guda tal a bar tafiyar tasu zuwa jibi , sannan kuma ya nemi da a sakayawa ita Falmata batun rashin lafiyar Mijinta tunda bata riga ta sani ba saboda halin da take ciki da ba'a son abunda zai tada mata da hankali .

A take duk suka yi Na'am da shawarar Prof kan cewa za'a rufe rashin lafiyar Youssoufa har sai Allah ya masa dawowa sannan kuma zasu É—aga komawar su zuwa jibi .

"Aisha daman Youssouf jinya yake ?

Yakaka ta tambaya tana dafa kafaÉ—ar Falmata da ta lura ta shiga damuwa sosai .

Da ƙoƙarin sauya akalar zancen Aisha tace " eh ,Ah ah ba wani ciwo bane ya dai tafi india ne , kai Mutanen Maiduguri kun ji daɗin ku ko'ina turaren wuta yana ci
Ta ƙarasa zancen tana musu nuni da ɗan burner da take cin turaren wuta a hankali .

" yayi tafiya ? Kuma kika ce ba shi da lafiya ne , dan Allah ki faÉ—a min mana ,

Falmata ta furta haka tana jin wani gagarumin tashin hankali na rufar mata , muryar ta har 'yar ƙyarma take yi .

Da sauri Aisha ta zo gefen ta ta zauna , ta dafa kafaÉ—ar ta sannan cikin taushin murya da alamar rarrashi tace ,

" en loi kadda ki damou Biyamuradi ya shiga haÉ—arin rayuwa ne Amma Allah ya fidda shi , doumin kouwa yanzu yana samun lafiya sosai , cikin watan ga mai kamawa shi ke dawowa da yardar Allah kin ji kou ?

Gyaɗa kai kawai Falmata tayi daga haka ta miƙe daga tsakanin su , su duk biyun da kallo suka rakata har ta shige banɗaki .

Yakaka ta sauƙe ajiyar zuciya tana dawo da ganin ta kan Aisha , cikin yin ƙasa-ƙasa da murya tace .
"amma ciwon da yake damun sa ba mai tsanani bane ko ?

Ita ma cikin raɗa Aisha tace " ya fa fara samoun sauƙi nima dai baƙina ya subce min .

Miƙewa tayi tana ƙarasa cewa " bari na kouma ga masauƙin mu daman na tou yi muku sai da sahe .

" ku huta gajiya Aisha mun gode ,

Yakaka ta furta hakan da 'yar dariya ganin yadda duk Aisha ta ruÉ—e da ganin sauyawar Falmata .

bayan ta fita a sarari Yakaka tace "Hmm indai wannan 'yar rigimar ce ba ku ga kome ba .

" wa kenen ?

Falmata ta tambaye ta lokacin da take takowa cikin ɗakin kai tsaye ta nufi ɗan saƙon da suke yin Sallah ta hau Sallaya bayan ta zura dogon Hijab har ƙasa ta fara haramar tada iƙhamar sallar shaf'i .
Chapter 224 · 0% Book details