← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 131 OF 269

Sashe 131

Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ware idanu sosai hajja me wurya take cikin son tabbatar da fuskar wanda take gani tarwai a fuskar ƴar tv da take kunne cikin ɗakin su na hotel da basu fi mintoci ishirin da dawowa cikin sa ba daga asibiti da aka sallamo baby mama wacce tayi sumul da ita tana ƴan wasanni ta tamkar ba ita ce jiya ta sha wahala ba ,

   Ke fatima wannan ba mijin naki bane ake masa ƙarin girma a wajen aikin sa? Ga shi nan ana nuna sa a tv,?  ashe babban SOJA kike aure , ah ki ce shiyasa kike firirita , ashe matar soja ce ,

   SOJA ?
waye ne sojan ? Ita fa bata ƙaunar soja ko jin sunan su ta yi zuciyar ta tsinkewa take , mutanen da suke da bindigogi da jiragen yaƙi ita kuwa ai bata manta bama-baman da sojoji suka dunga sakar musu a daji ba, da har ya sa ta gurɗe ƙafar ta gurin gudun ceton rai ,

  Saitin inda take jin tashin tv ta maida hankalin ta kafin ta ce
   Hajja waye ne soja ?
Shi baban jaririyar taki ,
Gwalalo idanu tayi
  Soja ne daman ? Soja masu ƴaki da bindiga da jirgin ƴaki hajja ?

Au daman baki ma san irin aikin mijin naki ba ? Hunm abun naki sai ido , bebiya ta auri makaÉ—i ,

Shiru falmata tayi tana jin wani tsoron sa sabo dal yana É—arsuwa a ran ta , baban baby SOJA ne ?, "

****

La'asar tayi musu a gidan da yake matsayin na biyamuradi youssouf da falmata , sojan da ya kawo su niamey shine ya je ya ɗauko su daga hotel ɗin ƙarƙashin umarnin youssouf da tun safe suke tare da maimartaba tare da wasu manyan ƙusoshin ƙasar a ainahin cikin gidan gwamnatin tarayya ,

Tunda suka shigo gidan da bayan sojan ya gama shigar musu da kayan ya danƙa ƴan mukullayen ga hajja me wurya ,

  Santin gidan hajja take tana bin kowanne lungu da saƙo tana leƙawa tare da addu'o'i tana jere su iri iri ,

Gidan ba wani babba bane amma tsarin sa me kyau ne dai-dai da rayuwar mai rufin asiri kuma ƴan gayu , ɗakuna uku ne a cikin dan madaidaicin falon sai kuma kitchen da yake ta cikin falon sai keɓantatcen wajen cin abinci , ko'ina an sanya kayan da suka dace ,

cikin ɗakuna biyun gadaje ne iri ɗaya tare da wardrobe ɗin su,  sai dai ɗaya ɗakin akwai set ɗin gadon jarirai har da ƴar kwabet ɗin jera kayan jarirai da yake mallakin baby mama , gidan kam yayi kyau sai sa albarka hajja me wurya take , ita kaɗai ba tare da falmata ta kula ta tanka mata ba ,

yammaci lis biyamuradi Youssouf ya iso gidan tare da shi akwai sabon direban da gwamnati ta ba shi , bayan motar su cike taf da kayan abinci zuwa ƴan kananun kayan buƙatu na gida irin su , omo , sabulai , toothpaste
d

a sauran su, 

Kai tsaye ya shiga gidan bayan ya ƙwanƙwasa ƙofa hajja ta buɗe masa , kan ɗaya daga cikin kujerun falon ya zauna bayan sun gaisa da hajja wacce take ta shi masa albarka har ma ta taya shi murnar ƙarin girman da ya ssmu wajen aiki ,

Dumm ! Yayi , ƙaƙa ankayi ta san an masa ƙarin girma ?

Kamar ta san tunanin da yake cikin dariya tace ma sa
   Ɗazu na gani a tv , gaskiya ɗan nan ka sha hotuna , anya hasken majigin hoto bai kashe ma karfin gani ba ? Yadda ka ƙware a rawar nan ta ku ta soji ka burgeni ai naso ita ma wannan matar ta ka tana gani ,da ta ga yadda kake shan juyi a fili nasan dole ka burge ta , hahaha

Ɗan murmushi yarima yayi yana maida kallon sa ga falmata wacce take gefe a ƙasa riƙe da baby mama , alamun rashin kuzari duk sun bayyana agare ta ,

   Fatima miƙo min ɗiyar ki na ga fuskar ta ko kouwa har yau kina mini rowar ta ne ??

Cikin sauri ta girgiza kan ta , "

   Hajja miƙa ma sa ita !

Hajja me wurya ta karbi baby ta bashi ,

  Ya karbe ta yana tambayar yanayin lafiyar jikin ta a yanzu ?

Hajja ta amsa masa da samun tabbatuwar lafiya ga baby mama ,

ya shagaltu da yiwa ƴar sa wasa daga shi sai falmata da ke rakuɓe daga chan gefe ,

Hajja tana cikin kitchen tana aikin gyarawa tare da sanya duk wasu kayan abinci a inda suka dace ,

bata yi aune ba ta ji ƙarar bindigogi da sauti iri iri ya karaɗe falon da ya sa ta yunƙura da gudu tana neman wajen tsira , rashin sanin kan falon ya sa ta dunga cin karo da kujeru ,

    Wani mummunan karo ta ci da doguwar kujerar falon da yasa tayi baya tare da sakin ihun da yasa biyamuradi miƙewa a zabari ya taro ta da hannun sa ɗaya , jin mutum a kusa da ita da ƙara kusantowar harbe harben da take ji ya sa ta ƙwaƙumewa a jikin sa ta zagaye dukkanin hannunwan ta biyu zuwa bayan sa ,

Hajja da ta fito da gudu saboda jin ihun falmata da ƙarar harbe-harben bindiga , sai ta ɗan yi turus tana yawo da ido neman bindigar take ,

Miƙa mata baby mama yayi ganin yadda take ƙoƙarin sanya kuka saboda ƙaƙƙarfar rungumar da falmata tayi masa ya sa ta firgita ,

Hajja ta karɓe ta tana cewa ƙarar bindiga nake ji ɗan nan ,  ince dai ba wai yaƙi aka soma ba ??

Bai amsa mata ba illa zaro wayar sa da yayi daga cikin aljihun sa bai duba waye ke ƙiran ba ya katse kiran ,

  Hajja ku yi haƙuri sautin ƙiran téléphone ne hakka ba wani abou bane ya kai ga faruwa ba ,

Au to to , ai cewa nake yaƙin ne ya biyo mu har nan , !

Wucewa tayi da baby mama É—aki tana neman abin goyo ,!

Fatima
   Sakar ni haka nan , na faɗi miki ƙarar talfo ne ...

   Wayar sa da ta sake ɗaukar ruri ita ta sa falmata ƙara sanya ihu tana sake shigewa jikin sa idan banda ƙyarma babu abunda jikin ta ke yi ,

Sauri yayi ya ɗaga kiran ganin sunan me ƙiran na sa

       princesse

Allô ma jolie fille.

Ya furta dai-dai lokacin da yake yin baya ya zauna akan kujerar da ya tashi tare da falmata wacce har lokacin riƙe take da shi tsam ta runtse idanun ta ,

Allo Mon amour !

tu me manques mon amour comment vas-tu aujourd'hui?

  Gimbiyar maimouna ta amsa masa cikin salon sautin ta na gogaggun matan da suke tsakiyar ganiyar su ,

Je vais très bien et tu me manques aussi,
     Ya amsa mata yana jin yadda daɗin sautin ta yake ratsa jikin sa ,
   
    Ma princes , Albishirin ka ?
   Tace da shi  .

Ɗauke da amon murmushin da ya bayyana har a fuskar sa yace  ,

   Gorro farare gimbiya !

Ko kassan yanzou jakka ( jakadiya )  ke sanar mouna saƙo ya taho dagga masarautar ku maigirma , ɗauke da gorron tsayar da ranar amren mu , gomma ga wata me kamawa , tabbas sa'a zata tabbata gare ni ranar da anka ɗamra amren mu da kai biyamuradin maraɗawa !

Wani irin daɗi ne marar misaltuwa ya ji yana ratsa zuciyar sa , tabbas zuciyar sa na ƙaunar maimounatu fiye da kowacce ɗiya mace , samun ta kuma nasara ce maigirma saboda a ta suffa da ƙawa tayiwa sauran mata zarra a wajen sa ,

    Cikin shauƙi ya sake riƙe wayar sa da kyau yana ɗan bubbuga bayan falmata wacce ta fara dawowa hayyacin ta , da ɗayan hannun nasa ,

Wannan albishir naki mai girmou ne tauraruwar Agades , votre histoire a fait son chemin dans mon cœur, s’enfonçant dans mon âme.

tamkar Falmata ta ji abunda ya faɗi , sai ta ɗago kan ta daga jikin sa , a hankali ta zare jikin ta daga nasa , ta miƙe tana taku sannu-sannu da ƙoƙarin barin falon , zuciyar ta shaƙare da haushin sa , ita shiyasa ta tsani soja ,

kome na su akwai sumfurin mugunta a ciki bayan haka tayaya sautin ƙiran waya da ta san ƴar ƙara ce mutane ke sawa a wayoyin su amma sai ga shi ta shi wayar ruwan alburusai take har da tashin boma bomai ,"

Cigaba yayi da hirar sa cikin nishaɗi yana jin yadda albishirin da tayi masa yake ƙara masa kuzari , lalle maimartaba yayi masa attaque par surprise
 
    Fiye da mintoci ishirin suna hirar su sannan suka yi sallama ya aje wayar sa ,
   
   Bankwana yayi da hajja wacce har lokacin tana kitchen goye da mama tana girka musu ɗan abinda zasu ci kafin kwanciyar bacci ,
   
    Har ƙofa ta raka shi tana masa addu'a da godiya

    Inda yake sanar da ita gobe zai wuce garin su zai iya kaiwa sati biyu zuwa kwanaki ishirin idan ya tafi saboda haka zuwa goben su masa lissafin abubuwan da zasu iya buƙata baki ɗaya ,

    Bayan fitar sa ta kulle ƙofar ta dawo ciki zuciyar ta cike da wasi-wasi akan hirar da ta ji youssouf ɗin na yi da wata wacce bata kai ga sanin wacece ba , sai dai cikin hirar su da mafi yawa da faransanci shi youssouf ɗin yake bada amsa , ta fahimci mafi yawan maganganun nasa na soyayya ne saboda zaman da tayi a ƙasar kamaru , kurtun ɗan sanda ne mijin nata a bariki suka yi rayuwar su dan haka sosai take tsintar wasu kalmomin faransanci duk da dai shekaru ya sa ta manta yaren sosai !
Chapter 131 · 0% Book details