← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 206 OF 269

Sashe 206

Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" ga jin daɗina lokacin da nake bibiyar rayuwar sa ina kafa masa tarko bayan auren mu , sai na fahimci ba ni kaɗai bace ba ke farautar rayuwar sa , ciki har da kai da Mahaifiyar ka Mammadou , babu ɓata lokaci muka haɗa hannu wajen ganin ƙarshen maƙiyin mu , kuma ga shi a ƙarshen ƙarshe mun yi nasara ,

  Wata ƴar dariya ta sake yi tana tsare ɗan sanda da ido , tace " wai ya ƙarasa mutuwa ne ko kuwa har yanzu yana shan wuya ?

    Wani ƙaƙƙarfan marin da aka ɗauke ta da shi da ya sanya ta yin tangal-tangal tare da giftawar walƙiya a idanun ta ya sanya ta rufe bakin ta ruf ,

Da wani irin yanayi a muryar Tafeeda yace ,
  " Babu shakka kin kasance mayaudariya , azzaluma ban yarda ke kina da ɗigon imani ba a ran ki , kamar yadda kika ce hukunci wanda yayi kisa ko ta yaya ne a kashe shi a irin naki ƙwaƙwalwar mai cike da duhun jahilci , da ke da duk wasu masu hannu cikin wannan mummunan aikin da kuka yiwa Youssouf muddin ya kai ga rasa ransa kamar yadda kuka so , wallahi baki ɗayan ku sai na kashe ku da bakin bindiga ta koda kuwa hukunci ya so muku sassauci , ni sai na kashe ku , sai na ....

  Muryar sa ce ta sarƙe jikinsa har tsuma yake idanun sa sun koma ciki tsabar tashin hankali , ya juya da sassarfa ya fita zuciyar sa cike da ruɗani ashe masoyin ka da ka yadda da shi kan iya zama mai farautar ranka ? Da ya tuno irin tsananin son da Youssoufa ke yiwa Maimounatou sai hawaye ya sauƙa a idanun sa ,

wacce irin zuciya ce haka a ƙirjin Mammadou da Hajiya Mama da zai sa a haɗa baki da su wajen kashe mutum irin Youssoufa shin me ya taɓa yi musu da zafi da ya cancanci ƙiyaya irin haka ? Babu shakka mutum ya tsoraci maƙiyin sa da yake ƙin sa babu wani dalili bayan ta hassada , irin wannan ƙiyayyar mai zafi ce , tsawon zamani baya tasiri wajen goge ta .

Yana kai ga ficewa daga harabar ofishin motar su Maimartaba da kansa ta sawo kai dan haka yayi baya da tasa motar tare da sake kashe ta ya fito ,

Sama-sama suka gaisa da Maimartaba a tare da shi da mahaifin shi kansa Tafeeda , sai kuma Hajiya Mama su uku ne kawai tare da direba ,

Hajiya Mama tayi firi-firi da tashin hankali ta bi bayan su Maimartaba , Tafeeda ya dafa musu baya yana jin kamar ya shaƙe Hajiya Mama ,

A ciki kai tsaye suka nemi da a haÉ—a su da Maimounatou da Mammadou ,

Bayan shigar su inda suke da har lokacin kowannen su bai rusuna ba , Mammadou yana ganin iyayen sa ya fashe da kuka yana ƙaryata duk wasu kalmomin da Maimounatou ta yi , akan yana da hannu wajen kisan Youssouf ,

  " Ranka shi daɗe wallahi ƙarya take min ban san kome ba , bani da hannu wajen mutuwar ɗan ouwana wallahi Abba ƙarya take min ,

Cike da nutsuwa Maimartaba yake kallon sa , kafin yace

   " Mammadou , Youssoufa bai kai ga mutuwa ba , har kawo yanzou yana asibiti , zuwa nan nayi saboda na fidda kai ne daga nan muddin ta tabbata baka da hannu cikin lamarin nan , muddin kuwa aka kama ka da laifi ni bani da ikon hana mahukunta aikin su , zaka cigaba da zama a nan har zuwa yadda hali zata kasance ga Youssoufa tsakanin rayuwa da mutuwa , daga nan sai mahukunta suyi hukuncin su yadda ya dace .

   Wani irin runtse ido Maimounatou tayi , tana son cewa wani abu sai dai cikar kamala da ƙima irin ta Maimartaba ya wuce ta yi wargi a gaban sa ,

Hajiya mama wacce ganin hawaye tare da tashin hankalin da ɗan ta yake ciki tare da kalaman da Maimartaba ya furta suka haɗu wajen ƙara mata tashin hankali kan wanda take ciki , ta zaburo tana cewa ,

  "  Ni nasani Mammadou ba zaka yi yunƙurin kashe ɗan ouwan ka ba , na san irin tarbiyyar da na yi maka , ni shaida ce akan irin ƙaunar da kake yiwa ɗan ouwan ka sai dai idan wannan makirar ce take ƙoƙarin samun abokin da zata raba laifin ta da shi , shine zata maka sharri , tsinannan ibilishiya ta Allah ba taki ba Youssouf zai tashi bai mutu ba ,
    Ta ƙarasa zancen tana fashewa da kukan wanke kai ,

  Kukan nata bai tsawaita ba ta tsinkayi muryar Maimounatou tana cewa ,

  " Hajiya kenan, ai ibilisan muna da yawa , amma ke ce shugabar mu , idan kin ce sharri na yiwa ɗan ki akan gubar da na zubawa Youssouf dan an samu tangarɗar cikar aiki , asirin da kika yiwa Youssouf na shan giya da neman mata domin ya tozarta ya rasa damar samun sarauta shima sharri ne kenan ? Duk da cewa kowa ya shaida saboda har ɗiyar banza Youssoufa ya ajiye aikin ki kuma ya kai ga matakin nasara kamar yadda duk kika tsara Youssoufa ya rasa martabar sa a idanun Al'umma ,

Kukan kura Hajiya Mama tayi ta shiga dukan Maimounatou , tana cewa ,
   " sharrin ki kaina zai dawo ? wallahi ranka ya dade ƙarya ɗiyar nan take min so take ta ga bayana , so take na tozarta shi yasa take faɗe-faɗen surruka masu nawi .

Maimartaba bai ce ƙala ba ya juya ya fita , yana fita , Maimounatou ta tunkuɗe Hajiya Mama da ƙarfi , cikin tsawa tace ,
    " Saurara ɗiyar talakawa , mai gajaren asali ni nan da kike gani na ɗiyar sarki ce , sarkin da ya yafi duk wani sarki ƙarfin mulki a ƙasar nan ,  dan haka ahir ɗin ki da ki sake taɓa lafiyar fatar jikina , kiyi ta kan ki da ramin da yake gaban ku ke da ɗan ki,  idan ku ka faɗa babu mai iya cire ku , ni kuwa kin ganni kome girman ramin da na faɗa daga Mahaifina ya ziro hannu zai tsamo ni .

Kamar wacce aka yiwa umarni Hajiya Mama tayi hanzarin barin É—akin zuwa inda su Maimartaba ke tsaye suna sauraron muryar duk labarin da Maimounatou ta bayar ,da Æ´an sanda suka naÉ—a a waya .

Bai jira karshen labarin ba Maimartaba yace su tafi kawai , jami'an tsaro su cigaba da yin aikin su duk ta yadda ya dace da ƙa'idar aiki ,

shi hankalin sa baki ɗaya yana ga Youssoufa da yake asibiti cikin mummunan yanayin mutu-kwakwai rai-kwakwai  da a halin yanzu an gama shirin kome na fita da shi ƙasar India , lokacin tashin jirgin su kawai ake jira nan da awanni uku .

A gidan baya na motar da Hajiya Mama da Maimartaba suke zaune , banda raba ido cike da rashin gaskiya babu abunda take yi ƙwarai Kalaman Maimounatou a gaban Maimartaba suka shammace tare da ƙara mata tashin hankali , ganin kome na shirin kwaɓe mata cikin ƙanƙanin lokaci .

Muskuɗawa tayi tana kallon Maimartaba tayi ƙanƙan da kai ta fara cewa ,
    " wannan ɗiya lamarin ta abun tsoro ne, dukkananin kalamanta cike suke da ƙarairayin....

Da hannu ya dakatar da ita ba tare da ya dubi sashin da take ba yace
"  Su kalaman mutum suna iya zamar masa tarko su fallasa ko wanene shi , ita hanyar mugaye kuwa duhu ne baƙi ƙirin, kamar duhun dare , da har sukan faɗi a cikin turbar su amma ba su san abin da ya sa suka yi tuntuɓe ba , sukan manta da cewa ita mugunta rami ce mai zurfi da a ƙarshe da mai tonon ta take ruftawa ciki , ki adana kalaman ki akwai wajen yin su ba nan gabana ba .

Muƙut ta haɗiye busasshen yawun tashin hankali , ta san irin wannan zaurancen na masu hikima da mafiyawancin lokuta Maimartaba ya fi amfani da su cikin kalmomin sa .

Hasashen manufar kalamansa ya sa gumi karyo mata yana tsiyaya ta cikin jikin ta , " Babu shakka kwaɓarta tayi ruwa tsululu .

****

Ƙarfe biyu na ranar jirgin da zai tafi ƙasar India ya ɗaga da Youssoufa yana a halin rashin sanin ina yake ?  A tare da shi da Maimartaba da kansa , da Hajiya Umma da kuma Tafeeda .

Tamkar wutar daji haka labarin gubar da Matar Biyamuradi Youssoufa da ɗan ouwan sa Mammadou suka ciyar da shi ya shiga ratsa kowanne lungu da saƙon ƙasar Niger baki ɗaya ,

Cikin kwanakin duk wasu kafar yaÉ—a labarai zancen ake ana sake maimaita sa , har wani sashi na daga muryar Maimounato cikin labarin da ta bayar kan dalilinta ake sakewa ,

A halin haka labari ya shiga sauya salo da launi iri-iri dake ƙara munana sa , wasu ma cewa suke ai fasiƙanci Maimounatou da Mammadou suke yi , da kuma sanin ita uwar Mammadou ita ce ma ta bada gubar da aka ciyar da Youssoufa ita .

Tozarta da ɓacin suna irin wanda Hajiya Mama bata taɓa zaton afkuwar sa a gare ta ba , ita ce ta faɗa mata lokaci ɗaya ,

Tuntuni labarin irin auka-aukar da Maimounatou tayi ya iske kunnen iyayen ta , da hakan ya sa take jinin Maimartaba sarkin Agades ya hau , aka ciccɓe shi ranga-ranga zuwa asibiti .

Nan take wasu daga cikin dangi suka fara Allah wadarai da ita .

 

    Assalamu Alaikum masu karatu da fatan kuna lafiya ?

Ina sane da haƙurin bibiyata da kuke yi , ina kuma godiya bisa yawan ƙaunar ku ga rubutuna nagode irin sosai ɗin nan , nima ina ƙaunar ku a duk inda kuke ina muku fatan Alkhairi .

Nagode
[12/26/2019, 9:58 PM] +234 706 503 6187: MAFARI
( Hargitsin Rayuwa)

Umm'muaz

47

Falmata tun tana zuwa É—akin Hajja tayi ta zama ba tare da ta iya faÉ—in abunda ke kaita É—akin ba ,
Chapter 206 · 0% Book details