← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 196 OF 269

Sashe 196

Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" To Shikenan Yakaka tunda kin ce haka bari nima na haɗa ƴan kananun kayan buƙatu na mu tafi tare , ai nima zama bai ganni ba , to na zauna nayi me ƴar nan ? Ai tunda ganga ta fashe sai ƴan rawa su watse ,

Da hanzari Hajja ta shiga harhaÉ—a kayanta, tana cewa ,
       "bari na tafi da waɗanda dole zan iya buƙatar su , sauran kuma idan Allah ya min dawowa na cigaba da Amfani da abuna idan kuwa ma tafiyar kenan , to a biyo ni da tsunmokara na , wannan lamari dai da ɗaure kai yake babu shakka da walakin wai goro a miya .

Yakaka da har lokacin a tsaye take akan ƙafafunta bata ce da ita ƙala ba ,

Cikin ƴan mintoci kaɗan ta haɗe kayanta a cikin wata babbar jakar matafiya da Youssouf ya taɓa saya mata , tana shirin yafa mayafinta suka tsinkayo sallamar Youssouf daga ƙofar falon , Hajja ta amsa tana nufar falon

A tsaye ta tarar da shi shirye tsaf cikin riga da wondo na kaftani da ya sha aiki irin na saraki , ba tare da ya yadda Hajja ta ga ƙwarar idanunsa ba fuskarsa babu walwala ko kaɗan sai tarin damuwa da tashin hankali da suka bayyana kansu ɓaro-ɓaro , cikin Amonsa da a yau ya sake kaurara da buɗuwa yace
    "Hajja ni zan tai Maraɗi yanzou Hajiya Umma tai ƙirana , don Allah ku zauna a gida har na kai ga dawowa nan da kwanaki biyu , lamarin Fatima kouwa zan yi dukkanin ƙoƙarina da Yardar Allah babu abunda zai samu Matata da abinda ke cikin ta .

ÆŠan karkata kai Hajja tayi da sigar tausayawa tace ,

" Babban soja Allah ya tsare hanya , sai dai kuma yanzu na gama fama da ita yayar Falmata kan cewa da tayi a yanzu itama za ɗau hanyar Nigeria saboda ko Allah zai sa su gamu da ƴar uwarta a tasha idan sun isa Maidugurin dan ita Maiɗakin naka ai kasan bata san ko'ina ba a can ko gidan shi mariƙin nasu bata sani ba , ana gudun kar ta ɓata ko ta shiga wani mawuyacin hali kuma a can , da naji haka sai nace to fa nima zama bai kamani ba tare zamu tafi , to kaga shirin nan da nayi ma na tafiyar ne ga kayana ma can na haɗa su gu ɗaya .

Bayan ya gama sauraron Hajja da tayi shiru tana tsumayen iznin sa , sai yace ,
    " hakka ma shawarace mai kyaou Hajja , to idan hakka ne ku taho na sauƙe ku ga tasha na sanya kou a mota , nima sai na tai gida ,

   "Amma Hajja doumin Allah dagga kun cimma gida kun tadda Fatima ki sanar min ta téléphone , sabadda na san halin da kuke ciki a can , duk da nima ba da jimmawa ba zan tai can Nigeria ɗin , kuma a nan sojin mu zasu yi bakin ƙoƙari wajen duba hanyar da ita Fatima zasu bi , sai dai kouma idan har ta ɓarauniyar hanya ta daban zasu ɓulla yanzou fatan mu dai yana ga Fatima ta cimma gida lahia .

" to babu laifi Babban soja ai sai mu tafi ɗin , Allah dai ya sassauta wannan lamari , bari na ƙira ita Yakaka ,

Mota É—aya suka tarar wacce zata tafi Kano kai tsaye daga Niamey dan haka Youssouf ya biya musu gidan baya na motar su biyu rak da daman mutum É—aya suka tarar a gaban motar dan haka nan take aka shiga neman direba ya zo kuÉ—in kujerun mota sun kammala ,

Laluba aljihunsa yayi ya fiddo kuɗaɗen ciki da baki ɗaya CFA ne , mayar da su aljihunsa yayi saboda sanin da yayi daga sun bar shiyar ƙasar su ba zasu musu wani amfani na sosai ba , ya zaro wallet ɗin sa da dalolin Amurka ke ciki a miƙe , ya matsa kusa da gilashin motar da yake sauƙe ta sashin da Yakaka take ,

Ba tare da ya dubi fuskar ta ba yake miƙa mata kuɗin da bai riga ya ƙirga ya san adadinsu ba ,

Yakaka wacce tunda ta shiga motar ta ɗauke kai daga barin kallon sashin da yake tsaye , amma tana ankare da shi ta kuma ga tsayuwar sa akanta yana miƙa mata ƙudi , bata son sake kallon fuskarsa ne dan haka taƙi ɗago kanta ,

Hajja wacce take raba ganinta a tsakanin su biyun , ta É—an zunguri Yakaka ,

  "Babba uwar Mama , Babban soja yana baki saƙo ,

  Da wani irin yanayi na gargaɗi a fuskarta ta kafe Hajja da idanunta da suke da kaifin kallo masu kamar gilashi ,

  Galala Hajja tayi tana mayar mata da martanin kallonta , sai kuma ta muskuɗa ,tana cewa

"Ajabba inji kanurai, o ni hauwa'u ,
   sai kawai ta maida ganinta can gefe tana kyeɓe baki .

A hankali Youssouf ya zura hannunsa kaɗan ta cikin motar ya sauƙe mata kuɗaɗen akan cinyarta yana cewa "Hajja Allah shi kiyaye muku hanya don Allah Hajja duk yadda lamari ya kassance muku ki jisheni ,

" Amin Amin Babban soja , da yardar Allah zan sanar da kai duk yadda ake ciki , kaima kuma Allah ya tsare maka hanya , mungode , mungode sosai Allah shi yiwa rayuwa Albarka .

"Amin Hajja nima nagoude , yace yana kama hanyar barin wajen ,

Yakaka wacce tunda ya ajiye mata ƙuɗin ta runtse idanunta tana tuno da lokaci na farko a haɗuwarsu , yadda ya ajiye mata kuɗin da ya sayi martabarta da su akan cinyarta ya haka ,

    Hannunta ta kai tana ture kuɗin da ya ajiye mata a yau zuciyarta cike take da rauni mai tarin yawa , sanin da tayi a yanzu Youssouf ya haramta a gareta , ta kuma Haramtawa kanta shi koda kuwa babu ran Falmata .
      Tashin ƙugin motar su yazo dai-dai da sauƙar hawaye a idanunta , haƙiƙa so gaskiya ne , so halitta ce da Allah yake sarƙawa a tsakanin zuciyoyin bayin sa domin ya samar da Salama a tsakanin ƴan Adam , yafiya , haƙuri tare da tsusayawa tafe suke a cikin so na domin Allah ,

Babu shakka Youssouf shine mutum ɗaya da Allah ya ɗarsa mata son shi tun bata san menene so da kansa ba , ta kuma so shi ba domin kome da ya mallaka ko ya taɓa mallaka mata ba , cikin rashin sanin ta jarrabawa ce Allah yayi mata kan soyayyar sa ,

   Tun ranar da ta san laifin da Youssouf yayi mata kan Yaudarar ta da yayi ya ɓata mata rayuwa bata taɓa jin tsanar sa tsana irin ta ƙiyayayya ba , sai dai ta ji tsanar shi bisa ga laifin da tasan ya aikata mata, take kuma neman yadda zata yi ta hukunta shi domin ta goge wannan tsanar da tayi masa a dalilin laifin sa ,

Dawowa da tayi ta tarar ya auri Falmata , ya rugurguza mata zuciya , lamarin ya girgiza ta fiye da duk wani abu da ta taɓa cin karo da shi cikin rayuwarta ,

Tashin hankalin da ta hango tare da Youssouf lokacin da tayi tattaki ta same shi take masa togaciyar ya saki Falmata , tare da tirjiyar da yayi mata sun shaida tare da bata tabbacin cewa Youssouf yana son Falmata , so kuma mai  tarin yawa , abunda ya kassara mata duk wani karsashin ta ,  ya kuma ƙara mata hau-hawar ɓacin rai ,zuciyar ta ta shiga tuhumar ta kan yaya zai yi mata haka ?

Rana ta farko da ta san da tabbatuwar cikin jikin Falmata sai ta ji ta tsani kanta tana kuma tir da zuciyarta da ta gagara yakice shi baki ɗaya daga cikinta , alhalin tuntuni ya zama mallakin ƙanwar ta ,

A yau saƙo-da-lungu take bi tana zaƙulo duk wani ɓurɓushi na son sa tana zarewa daga cikin ranta  , duk wani gurgun tunani ko hasashen da ta dunga yi a baya na zasu dawo suyi rayuwa tare da ita da shi da ɗiyar su har ma su haifi wasu ƴa'ƴan ,  yana zagwanyewa tare da gogewa daga cikin ƙwaƙwalwarta , ta rabu da Youssouf da sunan so kamar yadda Allah ya rabata da Mama ,

Youssouf ba nata bane ,  ya taɓa zama nata ne kaɗai akan shimfiɗar da shaitan ya shimfiɗa musu .

Youssouf na Falmata ne tare da Æ´a'Æ´an da zasu haifa nan gaba da kuma sauran matansa ,

Takurewa tayi a jikin ƙofar motar tamkar zata tsaga ta koma ciki saboda wani irin zogi da zuciyarta ke yi , babu shakka cikin sadauƙarwar soyayya ta gaskiya akwai ciwo mai tsanani .

***

Ya juya tare da tarin tausayinta cikin ransa , yaso ko da sau É—aya ta bashi dama ya nemi yafiyar ta bisa ga laifin da shi yasan ya aikata mata , har abada ita ai uwa ce ga É—iyar sa mafi soyuwa a gare shi , bai so ba suka sake yin rabuwa makamanciyar ta farko ,

A shekaru da girma gami da hankali nashi irin na cikakken Namiji , ba sai ita ko wani ya taɓa faɗa masa cewa tana son shi ba so kuwa mai tarin yawa da shi yake iya hango shi a kwance cikin idanunta ɓaro-ɓaro koyaushe ta dube shi , 

Sai dai shi da ita dukkanin su sun faÉ—a ne ga jarabawar rayuwa , kuma shi bai mata so irin na auratayya ko kaÉ—an , sai dai yana tausayawa mata sanin yadda ciwon so yake ,ga wanda duk Allah ya jarabta .
Chapter 196 · 0% Book details