← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 229 OF 269

Sashe 229

Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ɗan zaman mintoci tayi ta miƙe domin komawa ciki kan hanyar ta suka ci karo da Babbar baiwar da take kula da shiyar abincin gidan wanda a shekaru aƙalla zasu yi sa'o'in juna bayan sun gaisa har Hajja ta gota sai Tabawa ta dawo da baya tayi ƙasa-ƙasa da murya tana ɗan leƙen baya tace " Hajja Hauwa da fatan dai kin taya Uwargiyar ki shiri ? Dan Kin kouwa san ɗiyan yanzu ba irin mu bane masu duƙufawa bauta ga Miji .

A É—an jahilce Hajja tace "Shirin me fa Tabawa ?

Kama haɓa tabawa tayi tana ɗan karkata kai tace "kada dai kice min Uwargijar ki Gimbiya batta da sanin Yarima na daf da shigowa Masarauta ba ? dan kouwa a halin yanzu ma suna Niamey zuwa yammaci kouwa suke shigowa nan .

Da hannu biyu Hajja ta dafe ƙirji muryar ta na bayyana mamakin ta tace  " Dan Allah fa Tabawa?

A mamakance ta cigaba da cewa "yo ina kuwa muka sani muna zaune bonono , ai tsayuwa bata ganni ba dole na yi hanzarin komawa ciki, ke dai tabawa nagode miki.

A zaune ta tarar da Falmata tana mammatsa yatsun ƙafafun ta da suke mata tsiko , ba tare da ta ɗago kai ba ta amsa Sallamar Hajja wacce ita ma kai tsaye ta zarce banɗaki ,bata tsaya yi mata dogon bayani ba  .

ruwa mai zafi ta tarawa Falmata ta tuttula duk turarurrukan wanka da ta tarar da su a guri na musamman a jere da wasu ma ƙila ba na wanka bane ita dai Hajja ta zuba ƙamshi gum kuma ya cika banɗakin ya ratsa har waje .

"Fatima tashi ki je kiyi wanka maza-maza zama bai gan ki ba 'yar nan .
Hajja tace haka lokacin da take dawowa cikin É—akin

Falmata da ta riga ta saba da subaɗaɗin Hajja ta ɗan dubi Hajjan tana komawa ta kishingiɗa a ƙasa tace "Hajja duk yaushe nayi wanka da safe ? Sannan kuma wanka da tsakar ranan nan ƙarfe ɗaya saura Hajja lafiya dai ko ?

" lafiya lau sai Alheri 'yar nan domin kuwa yau UbanÉ—akina ke dawowa Babban soja Baban Mama yau amaryar ki kike uwarÉ—akina wankan taryar miji za kiyi .

"Da gaske Hajja ?

. Falmata ta tambayeta tana miƙewa  zaune fuskar ta ɗauke da yanayin da tashi ɗaya ba'a ba shi matsayi ba .

bata jira Hajja ta bata amsa ba ta cigaba da cewa " Amma kuma ba wanda ya faÉ—a mana ko Maman Yumna ma bata faÉ—a min ba anya Hajja da gaske ne ? wa ya faÉ—a miki ?

. " mts , ahaf ai ga irinta nan ke wa ya faɗa miki kishiya tana zama abar dogaro ɗari cikin ɗari ? Wa yace miki ana bada amanna da Amana baki ɗaya ga kishiya ? Ni daman daga ganin yadda take miki nan-nan nasan tsagoron kissa ce da kilbasa ai kin ga ga shi da tasamu labarin dawowar mijin ku ɗif ta ɗauke ƙafa tana can ta duƙufa shirya kan ta , ta bar ki baki sake ,

"Yanzu kiyi maza ki tashi ki gyagiije dan waɗannan ƙananun muri-mirin kowacce mai ciki sai tana yin su basu isa hana kome ba ai ciki ba cuta bace , kiyi azamar yin wankan ki fesa ado irin na shiga gasa ki tafi gaida Mahaifiyar sa daga nan ki zauna a falon ciki wajen ta , ta yadda daga ya sanyo kai falon zai gan ki tunda kuwa dai daga ya iso gidan gaishe da ita shine abu na biyu da zai yi bayan gaishe da Mahaifinsa , kin ga ita Siyamar take ko wa ? Da take miki ƙafar ungulu kin riga ta ganin sa , tashi maza uwarɗakina ba'a bori da sanyin jiki ...

"Hajja ni dan Allah ki rabu da ni , kina ganin dai yadda koyaushe muka je gaishe ta ɓata rai take yi dakyar take ansawa sannan .....

Kafin ta ƙarasa Hajja ta katse ta "banda abun ki uwarɗakina faɗan da ya fi ƙarfin ka ai mayar da shi wasa kake , idan ta amsa yau da kyar watarana da fara'a zata tare ku ke da 'yan jikokin ta kiyi haƙuri kin ji  inda ba'a son ka anan arziƙin ka yake ke dai gwada mata ɗa'a sai ki ribaceta da kyawawan ɗabi'u kin san su saraki ne sai ana musu bangirma kin jii ko?  .

Turo baki Falmata tayi da cigaba da cewa "  sannan Hajja shi ma ɗin ai bai ma san mun zo ba tunda kin ga fa bai taɓa neman mu ba gaskiya ni ba zan kai kaina wajen sa ba idan shi ya zo shikenan idan bai zo ba ma ni.....

Wannan karon a hasale Hajja tace "to ai shikenan zauna kiyi ta jiran sa anan shi da yayi yi jinyar ya zo ya gaishe ki Iya-gwamma , tunda ni dai ba ki É—aukeni bakin kome ba a zaman mu ban isa baki shawara ba ai shikenan .
Daga haka tayi ficewar ta

Bayan fitar Hajja a ɗakin sai duk jikinta yayi sanyi , tunda take da Hajja bata taɓa ganin tayi fushi ya haka ba duk sai ta ji ba daɗi dan haka ta miƙe a hankali ta shiga banɗakin

Bayan fitowar ta da daga banÉ—akin da ta kwashi wajen mintoci talatin a ciki tana wanka.

jikinta ba kuzari ta zauna a kujerar gaban gadon , har yanzu Hajja bata shigo ɗakin ba , tunanin da yake nuƙurƙusar ta sake yawaita yake yi

"da gaske yau yake dawowa amma bai neme ta ba ? Tun rabuwar su har yau bai taɓa jin kewar ta ba kenan ? Shiyasa bai neme ta ba , tunda Aicha tace suna yin magana a waya kuma ko bayan dawowar su maradi rannan da kunnen ta taji suna waya da Aicha , kenan ita ce bai nema saboda baya buƙatar ta ko me ?  to meyasa ita kuwa zata damu kan ta da tunanin sa ? Har Hajja zata matsa tayi wani shiri na musamman a domin taryar sa .

Har ruwan jikinta ya bushe bata shafa Mai ba , agogon ɗakin ta duba ƙarfe biyu har da kusan rabi dan haka ta miƙe ta sake komawa banɗakin tayi Alwala ta zo tayi Sallar azahar bayan ta idar bata miƙe akan sallayar ba ta cigaba da zama akai tana istigfar lokaci-lokaci tana murza idanun ta da suke mata mil-mil tunda tayi wanka da alama sabulan da tayi amfani da su wajen wankan sunfi ƙarfin lafiyar idanun ta .

Tana zaune har aka ƙira la'asar bata jinkirta ba tayi Sallar kawo lokacin rashin jin motsin Hajja ya fara damun ta dan haka ta miƙe ta buɗe Babbar wardrobe bango guda da aka zube mata suturunta ciki ta dauko wata doguwar baƙar riga ta sanya a jikin ta ba tare da ta shafa ko hoda ba sai ɗan mai da ta mutsiƙa a fatar ta .

Dawowa gaban Babban mudubin tayi ta tsaya tana duban kan ta cikin ta da ya É—an tasa ya bayyana a sarari ta cikin rigar ta tsirawa ido.
"Kunyar fita a haka ana gane mata cikin ya kamata ta .
"Mts shi cikin nan ma duk ya bi ya hana mutum sakewa .
tayi mitar haka lokacin da take cire rigar jikin ta ta zaro wata doguwar riga har lau launin ruwan zuma mai duhu da ya ɗan sirka da zane a tsai-tsaye launin farar ƙasa , rigar faffaɗa ce da take da rufaffen wuya sannan tana da ɗan nawi kaɗan a can Rochester ta taho da ita ,

lokacin da ta Sanya a jikinta ita da kan ta sai da ta ɗan murmusa saboda yadda rigar ta amshi zubin jikinta na dirarriyar mace mai matsakaicin tsawo da 'yar ƙiba kaɗan sai cikin nata ya ɓuya a rigar

Rigar bata da mayafi dan haka ta ɗau wani babban mayafi launin farar ƙasa da aka masa adon duwatsu ta yafa akan ta ya rufe mata jiki kirif , har zata matsa daga gaban mudubin idanun ta suka kai kan 'yan kunnayen ta da tunda ta taho da su daga Maiduguri ta cire su ta ajiye ana,  su ta kai hannu ta ɗauka 'yan gajeru ne ta maƙala su a kunnuwan ta a hankali ta sanya ɗan yatsa ta lakaci mai ta shafe siraran labbanta marasa tudu .

Takalmanta masu kama da silifa 'yan madina amma wannan daga Rochaster ta zo da su su ta zira a ƙafar ta ta fito bayan ta shafe jikinta da Humra da kamshin ta ke tashi kaɗan-kaɗan .

Boyayyar ajiyar zuciya tayi lokacin da ta fito falon ta ga Hajja zaune daga gefe da alama Salla ta idar .

Da fara'ar jin daÉ—in ganin ta ta matsa kusa da ita kafin tace " Hajjata anan kike ?

ÆŠan waigowa Hajja tayi kamar bata san da fitowar ta ba tace " uhm anan nake .

" to sannu da hutawa Hajja nima yanzu na gama shirin zan shiga na gaishe su yadda kika ce .

. Wannan karon Hajja ta ɗan saki fuska jin Falmatan tace zata yi yadda ta sa ta dan haka ta ce " to Madalla ko kefe fa uwarɗakina ? Maza je ciki ki zauna idan son samu ne ma ki samu wajen da yake fuskantar ƙofar shigowa ki zauna kin ji ko ?

. " to Hajja
Falmata ta amsa cikin ran ta tana gujewa rigimar Hajja ne amma idan ba haka ba ita ba wani niyyar zama tayi ba .

Da kallo Hajja ta bi bayan ta cikin ran ta kakkabin wannan rigar ta Falmata take yi taɓe baki tayi kafin a fili tace " ana yi yafi ba'a yi tsarkin mahaukaciya da kunu , idan ba haka ba wannan riga da kika sako ai bata da maraba da buhu .

A ɗarare Falmata tayi sallama a bakin  falon da daga inda take tana jin tashin hayaniya da dararrakin mutane da alama akwai wasu baƙi masu ɗan yawa a ciki .
Chapter 229 · 0% Book details