← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 269

Sashe 59

Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

   sai lokacin yakaka ta lura da yasashiyar robar abincin falmata da take buɗe , ɗaukar robar tayi tana kallon abincin da ana gani an san ƙarshen tukunya ne ƙanzo-ƙanzo ,babu wani mai da yaji na kirki cincirindon ƙudajen da suka tashi daga kan abinci ya sa ba shiri yakaka ta juye shi a bakin makwarari ta wanke robar ta ɗauraye ,

Ta ɗauko malmalar ɗaya ta sawa falmata ta sake gutsuro rabi ta ƙara mata ta juye mata fiye da rabin miyar , ta kai mata tuwon gaban ta ,' tare da taro mata ruwa a kofi daga bakin fanfo , ita ma ta zauna daga gefe tana cin guntun tuwon ! Suna ƴar taɓa hirar su kamar yadda falmata take so , cikin hirar su take sanar da ita ta shirya gobe zata kai ta ita ma a wanke mata kan ta tare da yi mata kitso !

Bayan sati biyu

Rayuwa tayi wa yakaka tsanani wanda ba kome ya jawo hakan ba sai rashin  bature kam silum , domin cikin satin biyun da suka biyo bayan ranar haɗuwar su ta ƙarshe , kamar yadda samy baby ta alƙawarta mata zata nemo mata shi ta wurin abokin sa ,!

  Ta je barracks ɗin sai dai bata tarar da shi Colonel nuhu ba, an tabbatar mata da ya tafi bakin aiki ,! Wanda hakan sam bai mata daɗi ba kuma ta kirayi duk numbobin sa basa tafiya ta rasa dalilin haka ! ?

Zuwan ta daban-daban uku bata samun sa , dan haka ta ɗan tsahirta .tare da cigaba da lallaɓar yakaka wacce ta lura tayi zurfi cikin mahaukaciyar soyayyar mutumin da a yanzu take hasashen yayi wa yakaka nisa , sai dai a nemo madadin sa ! Wanda bata ga alamun samun haɗin kan yakaka wurin nemo madadin na sa ba ! , babu ranar da yakaka bata kuka akan soyayyar bature kam silum , ɗakin samy baby nan ne wurin fakewar ta ta sha kukan ta domin ita tasan matsalar ta ita tasan dalilin kukan ta , kuma ita take zaton zata iya share mata hawaye , sai dai a yanzu labarin ya sha banban kuma wankin hula na neman kai su dare ,!

A yau yakaka ta tashi bata da ko sisi domin satin da ya wuce ta kai falmata asibitin ido da kuÉ—aÉ—en hannun ta inda kuÉ—in magunguna da wasu aune-aune , ya lashe fiye da naira dubu takwas , a cikin sauran dubu goma sha biyu da Æ´an kai da suka rage mata ,

Da sauran kuɗin tayi amfani wurin cigaba da hididimun yau da kullum , musamman abinci wanda shine kan gaba wurin lashe mata ƴan kudaɗen domin kwanan nan ta tsinci kan ta cikin wani irin bala'in kwaɗayi , bata iya cin abincin da bai wadatu da kayayyakin ƙawata girki ba , bata kuma cin abinci babu nama sannan a rana bata sha lemon kwalba "pepsi " ba tasha guda uku safe rana dare ,' idan kuwa bata sha ba babu zaman lafiya wani iri bala'in yunwa mai tafe da tashin hankali zata dunga ji ,"

Da haka kuɗaɗen hannun ta tas suka ƙare !

Duk da tarin damuwar da take cin ta cikin rai , kallo É—aya za'a mata a gane ta sauya , ta sake fari har tana É—aukar ido ta cika tayi luwai-luwai kyaun idanun ta kamar gilashi sun sake haskaka ,! Tana zuwa wuri take É—aukar hankalin jama'ah .

Ture jakar kayan tayi gefe ta ƙarasa bajewa ta zauna daga durƙuson da tayi ta tallafe kumatun ta da hannu, wannan shine karo na uku tana chaje cikin kayan ta a safiyar yau ko Allah zai sa tayi gamdakatar da wani makararren chanji , sai dai koh alamar kuɗi bata gani ba idan aka ɗauke kuɗin sefa ,"niger", wanda basu da wani maraba da babu a wurin ta ,"

A hankali ta miƙe tana haɗa hanya saboda wata azababbiyar yunwar da take wuji-wuji da ƴaƴan hanjin ta ,'

ÆŠakin samy baby tayi wa tsinke ,'
  Saɓanin zaton da tayi zata tadda ta tana bacci ta jira tashin ta , sai ta tarad da ita tayi shiri tsaf , tana zaune bakin gado tana shirya kayan ta cikin ƴar jaka ta matafiya ! Gaishe ta tayi cikin ladabi !

Yauwa yaks daman yanzu nake son na tura a ƙira min ke , tafiya ta taso min jiya-jiya cikin dare Honourable yake sanar min zamu yi tafiya tare da shi zuwa abuja inda zai je wani aiki watakila ma mu wuce dubai daga chan ," ga waɗanan kayan ki ɗauka na bar miki su , ni nasan a chan zan taho da wasu masu zafi ," ta furta hakan tana mai turawa yakaka wasu kayayyaki da ta ware su gefe,!

Yakaka wacce tun da taji kalmar tafiya jikin ta ya sake yin sanyi laƙwas ,! Ta durƙusa bisa guiwar ta ,' a gurin samy baby take ɗan samun nutsuwar zuci , take kuma ɗan taimakon ta da wasu abubuwa ,  baza ta so ba ta tafi ta bar ta a wannan halin tsaka mai wuya da take ciki ,
    Cikin sanyin murya tayi mata godiya , bayan ta haɗa kayan ta ƙulle su a ɗankwali ,'
    Cigaba tayi da zama tana bin kowanne motsi na samy baby da ido cikin ran ta tana ayyana dama ita ma da bature kam silum ya tashi tafiyar sa ya nemi rakiyar ta mana ? !

    Lura da yadda jikin ta yayi sanyi yasa samy baby , ta ce
      Ni bani ma lambar wayar ki idan naje ma dunga yin waya , ba kina da waya ba ?
    Gyaɗa kai tayi
Amma ban san nambar ba wayar ma tana ƙasan kaya na babu chaji ,
   Mts idan banda ke yaks waye zai saka waya ƙarƙashin bacco ? To wannan ai ko yariman ma ya kira ki ba sani zaki yi ba ," gidadancin ki yayi yawa yaks bari dai na dawo daga tafiyar nan inaga darasi zan fara baki dalla-dallah
   Ƴar takarda ta ɗauka daga jakar ta ta rubuta mata lambar wayar ta ta miƙa mata ,"
    Ga lamba ta nan ki kira ni idan kin saka wayar a chaji kuma ki daina ajiye wayar a nesa watakila ma shi baturen naki yayi ta nema bai same ki ba ,'
      Cikin ɗan ɓurɓushin farin cikin jin an ambaci sunan masoyin ta tace
    Toh anty zan dauko yanzu idan na koma ɗaki , anty kuma yaushe zaki dawo ?
    Ban sani ba yaks ni ƴar rakiya ce ! Sai lokacin da ya gam Abun da ya kaushi zamu dawo tare .
   Gƴaɗa kai ta sake yi !
Toh anty sai kin dawo Allah ya kiyaye hanya ! ta furta hakan bayan ta miƙe tsaye da ƙullin kayan ta ,"  har ta je bakin kofa ta tsinkayo muryar ta
      yaks ungo wannan kƴa ɗan sayi pepsi ki sha tun da yanzu naga yayin ɗaga ƙwalbar pepsi kike ! Ta ƙarasa zancen da ƴar dariya

Dubu biyu ta bata , da murnar ta ta ƙarba ," tana jero godiya

     Zuwa tayi ta kai kayan da ta bata ɗaki ta dawo domin yi mata rakiya,

Tare suka jera yakaka ta É—aukar mata jakar kayan nata , suna tafe tana sake karfafawa yakaka guiwa ganin yadda duk ta bi ta damu da tafiyar da zata yi , har zuwa bakin babban titi inda ta samu "mai adai-daita ", ta shiga tare da yin bankwana da yakaka !

Akan hanyar ta ta komawa gida tayi zurfi cikin tunanin ƴar ƙanƙanuwar duniyar ta ,wacce babu kome cikin ta sai tarin ƙalubale , mutanen duniya tausayi yayi ƙaranci a zuciyar su , son kan su tare da son dukiya sun makantar da su wurin duban na ƙarƙashin su da ƙyautayi da kyautatawa , kaɗai suna duban na ƙasa da su ne idan wata buƙata tasu ta tashi wanda suke buƙatar wannan ya kawar musu da ita ,

Da ƙarewar kuɗin hannun ta da tsayuwar rayuwar yancin da ta fara dai-dai suka zo domin tun lokacin da madam saly ta fahimci fa yanzu ta koma faƙiriyar ta kuma ta daina ganin gilmawar mutumin da ya tsaya mata tare da jin yayyafin nerar da yake yi mata , ita ma taci burki daga duk wani mutunci da lallaɓawar da take yiwa yaks , ta koma karta mata walakanci tare da bautar da ita ," ah toh me zata jira ? Ai kawai ungulu ta koma gidan ta na tsamiya , jaki ya tai gidan uban sa !

Ita ba gallazawar bautar aikin yafi damun ta ba illa yadda ƙarfi da yaji madam saly ta fara kai ta gaban ƴan iska tana tallar ta , ita baza ta jure hakan ba , bayan bature kam silum bata jin zata iya yadda da wani ɗa namiji har suyi abun da suke yi tare da shi ,  cikin su wanene mai kamannin sa ? Mai tsaftar sa ? Mai wayewar sa ? Mai gayun sa ? Mai irin ƙamshin sa ? Babu ! Idan kuwa haka ne ita baza ta yadda da kowanne ƙaton ɗan iska ba bata son su !

Zata jure kowanne irin aikin bauta da wahala , amma ban da harkar taimako ta wannan sigar , bature kam silum kaɗai yake da wannan ƙimar a gurin ta , zata zauna zaman jiran sa har ranar da zai dawo gare ta !

Da wannan tunanin ta ƙaraso shagon "fashe mai shayi ! Tace a fasa mata ƙwayaye shidda a soya su da indomi manya biyu , a haɗa mata shayi da madarar ɗari bonbita na hansin ! Ta miƙa kuɗin aka bata ƴan chanjin ta .

Aka sarrafa mata aka zuba a leda ta ƙarba , Shagon gefen sa ta wuce ta sayi lemon kwalba na pepsi mai sanyi ,
Chapter 59 · 0% Book details