Sashe 86
Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kai tsaye ya sa kan sa cikin gidan hanyar da ya bi jiya ita yau ya bi ya zo har bakin ƙofar ɗakin madam saly , har lau bai ga giftawa kowa ba tamkar gidan ba kowa ,"
  Garam ! Ya ga ƙofar ɗakin madam saly garƙame da ƙwaɗo har biyu ƙarami da wani fankacece iri na rufe ƙofar babban gareji ,"
 Duka ya kaiwa ƙofar ɗakin da ƙafar sa da matuƙar ƙarfi wanda ba domin ƙofar ta ƙarfe bace da ta karye,
 Ya ɗaga murya yana cewa
 Ina masu gidan ??
 Ina masu gidan ??
Ko giftawar kadangare bai gani ba , bai buƙatar a sanar da shi , ya fahimci sun gudu ne ," nan take wani malolon bakin ciki ya maƙale masa a maƙoshi ,"
Murza fatar goshin sa yake yana kokarin saita kan sa lokacin da yake kan hanyar barin gidan cikin ran sa yana aiyana zai dawo kuma haɗuwar su ta gaba baza ta taɓa yiwa madam saly kai dama duk mutanen gidan kyau ba ,
  Cikin takun da bai ko duba inda yake jefa kafafun sa ya bar gidan yana jin yadda zuciyar sa ke azalzalar sa da ya ɗan kora ruwa ko zai samu sa'ida azabar damuwa da yake ciki ta isa haka , amma tunowa da tafiyar ratsa daji da take gaban sa ya sa shi yakice tunanin shan barasa a wannan lokacin ,
ya fisgi motar da matsanancin haushin rashin cikar buri ya bar wajen bai ko kula da taron Æ´an cha-chan da suke baje akan wata babbar tabarma daga Æ™arÆ™ashin bishiya a gefe suna faman yin karta tare da dara , da ya watsawa ruwan kwatami daga jikin su har zuwa fuskokin su ba ,Â
  Wucewar sa kenan ɗan liti ya fito daga banɗaki inda yayi maɓoya , bayan ya tabbatarwa da su madam saly su watse kaf su bar shi shi kaɗai a gidan zai jira zuwan kurtun ɗan sandan , ayi wacce za'ayi ɓera ya zubda garin kyanwa!
Banten uba ! Kuturi ai yau da na yadda ya ganni sai ɗan buzu na , ai wallahi da sai dai Baba malmo ya auro wata safara'un ta haifi wani ɗan litin ba dai ni ba ,! Chab kai ka ga mutum kamar safurarren doki ??? Yana tafiya haka - haka - haka ,"kamar jarumin sadauki a fagen daga ??  Ko a mafarki na gan ka ai nayi sadaka !
   Ahayyeee saly fara ta zo ta lale min kuɗin gadin gida da nayi mata ta biya ni ,," kurtun ɗan sanda kuwa cewa zanyi na gama da shi ," ah to meye ?? Ko banza ai na shaƙi tsoro da bugun zuci, " Rikicin duniya kuwa ai da me rai ake yin sa ehe ,!
****
 Bayan kammala bikin zainab da sati guda doctor Hamza ya sanya yakaka a makarantar islamiyya da Rahima take zuwa , amma ta ta bangaren matan aure take zuwa kullum da safe karfe 8am.zuwa 12pm falmata kuma aka cigaba da koyar da ita arabi da bokon a gida ,'
A makarantar yakaka ta san sabon sunan da doctor hamza ya laƙaba mata a matsayin sunan ta na yanka ,watau AMINA MUSTAPHA DILMARI ,
Sosai take mayar da hankalin ta kan karatun ta kamar yadda doctor hamza kullum yake gargaɗin su , a gefe guda kuma cikin ta na cigaba da bunƙasa ta yadda har girman sa ya so yin yawa dan haka a awun da ta je cikin satin nan aka hana ta shan su madara da sauran cimakar da take sa yaro ya girma sosai a cikin mamar sa ,"
  Da wata safiya tayi shirin makaranta ta fito zata tafi sai ga motar samy baby ta tsaya a gaban ta , gaban kaɗan da gidan su doctor Hamza
  Nan ta nemi ta shigo suyi wata maganar da take tafe da ita , tayi murna ma da suka haɗu anan waje ,"
ba musu yakaka ta shiga motar tana murna sake ganin samy baɓy a dai-dai wannan lokacin da ran ta yake cike taf da son sani game da youssouf
  Nan cikin motar samy baby ta fara yiwa yakaka huɗubar da ta zamto kuskure na biyu da yakaka zata afkawa a rayuwar ta ,
A sanyaye ta fito daga motar bayan ƙarasowar su gaban makarantar , ta luluƙa a duniyar tunani , ta yadda har bata san lokacin da samy baby ta jaa motar ta tayi tafiyar ta ba ,"
 Idan aka zo ga batun ƙaunar ta ga youssouf kome kunce mata yake , tana son shi sosai , yana birge ta fiye da kowanne mahalukin da ta taɓa cin karo da shi a rayuwar ta , amma anya ? Anya girman son da take masa ya kai mizanin da zata dai-daita shi da falmata ? Ƙanwar ta jinin ta ? Abar batun cikin jikin ta shi wani sabon abu ne da yanzu yake kan hanyar shigowar sa cikin rayuwar ta , duk da cewa akwai ƙauna irin ta ɗa da uwa a tsakanin ta da abinda yake cikin ta wanda tasirin son da take yiwa shi youssouf ɗin yake mamayar abun da yake cikin cikin nata tare da ninka mata ƙaunar son gudan jinin sa da ke tare da ita ,
To amma falmata ba ?? Falmata haske ce kuma sanyi ce sannan cikamakin farin ciki ce cikin rayuwar ta , tun asali akwai shaƙuwa da so mai tsanani a tsakanin su fiye da wanda aka saba sani tsakanin saƙo-da-saƙo na haihuwa , ya zarce ƙauna irin ta tsakanin ƴa da ƙanwa sai dai a kwatanta shi chakuɗuwar jini da soyayya irin ta tsakanin tagwaye wanda ƙarya ɗan adam ya zare wannan tsananin wannan son da shaƙuwar da ya samo asali tun daga ranar faruwar halitta a cikin mahaifiya , sai dai fa ikon rabbi ,"
Zata iya kome domin ganin ta samarwa da falmata farin ciki a kowanne bigire na rayuwa fatan ta a koyaushe ta hango farin ciki bisa fuskar miskiniyar ƙanwar ta , sai dai wannan lamarin da yau anty samy ta zo mata da shi , yarda da shi tare da yin aiki da shi tamkar ta ɗau takobi ne ta gille duk wani farin cikin da Falmata zata iya shinshinowa a rayuwar ta , tamkar ta kassara ruhi da gangar jikin falmata ne , wacece FALMATA idan babu YAKAKA ???
Ba ta san ta kawo karshen makarantar ba sai da ta ji ta kaiwa bango karo ,
Zamewa tayi ta zauna dirshan a cikin ƙasa gami da fashewa da kuka , a sarari take furta kalmar," bazan iya ba , bazan iya ba, !
****
Cikin satittikan da suka biyo baya samy baby ta cigaba da zirya tsakanin makarantar su yakaka inda take killace ta tana cigaba da cusa mata ra'ayin da take ganin zai iya tsallakar da yakaka daga faÉ—awa hannun sofi , ta hanyar yin amfani da kalaman yaudara da wayo ta cikin amfani da makahon son da yakaka take yiwa Youssouf ,
har ta kai ga nasarar samun haɗin kan yakakan ta wani ɓangare ba tare da ita yakakar ta san haƙiƙanin meke cikin ran samy baby ba,
iyaka son youssouf tare da ƙwaɗayin son samun sa a matsayin miji ya sa ta fara amincewa da shawarar samy baby , ɓangaren zuciyar ta dake gargaɗin ta tare da tuno mata da so tare da tausayin dake tsakanin ta da falmata ya fara samun rauni , ! Soyayya tayi ƙarfi ta yadda ta fara rufe mata idanu !
Sannu sannu , yau da gobe zuciyar yakaka tare da taimakon huɗubar samy baby da ta shaiɗan , ta ƙeƙashe da son ganin cikar burin ta na mallakar youssouf a matsayin mijin ta , kamar yadda samy baby ta wanzu tana ƙara ƙwaɗaitar da ita ,
bata ko duban hidindumu tare da gatan da doctor hamza yake gwada masu ita da ƴar uwar ta musamman ma ita da komen ta yake mai matuƙar muhimmanci agare sa , ko sau ɗaya bai taɓa burge ta ba , Koyaushe ɗaukar sa take a matsayin me kirki me TAIMAKON SU,
hankalin ta a kullum daÉ—a tafiya yake ga youssouf wanda a yanzu hoton sa ya zama abun É—ebe kewar ta kullum dare har ma ta kan É—an zanta da hoton idan dare yayi nisa wutar so kuma ta ruru iya ruruwa , sai ta fara sakin sambatun so ,
Sai dai tana ƙoƙari wurin boyewa musamman ga doctor hamza , wanda watarana a cikin ranaku ya kamata tana kici-kicin ɗaura agogon da youssouf ɗin ya bar mata a tsintsiyar hannun ta ,
ta shagala cikin bege sai murmusawa take har haƙoran ta na bayyana , sakamakon yadda idan ta ɗaura agogon yake zamewa daga hannun ta idan ta sauke hannun , sai tayi maza ta taro agogon ta chafe shi ta sake mayarwa cikin hannun ta , tana lailaya shi kamar tana ganin fuskar youssouf ɗin a jiki ,
Ya ɗauki lokaci dogare a bakin kofar yana kallon ta cikin shauƙin ƙauna , sosai tayi kyau a idanun sa tana sanye da atamfa buɗaɗɗiyar riga da zane, tayi ƴar madaidaiciyar ƙiba ta buɗu kaɗan , sai ɗaukar ido take
Hankalin sa ne ya koma kan agogon da take wasa da shi a hannun ta , yana iya hango girma tare da ƙƴallin agogon daga inda yake tsaye ," ya shaida agogon maza ne ,"Â
Takawa yayi ya ƙarasa cikin falon bata lura da zuwan sa ba , sai gani tayi hannun sa ya riga ɗayan hannun ta chafe agogon lokacin da yake silmiyowa daga tsintsiyar hannun ta ,"
Ɗaga agogon yayi yana ƙare masa kallo daga gani ba tambaya agogon mai matuƙar tsada ne , da samun irin sa sai a hannun goggagun attajirai ,"
Cikin taushin murya da nutsuwar da take mahaÉ—in cikar kamalar halittar sa yace ,"
  Agogon waye ?
Shiru tayi tare da sunkui da kai, tun usul ƙarya bata cikin halayyar su , basu ma san yadda ake yin ta ba idan ba yanzu da duniya take ƙoƙarin koya musu ba ,"