← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 145 OF 269

Sashe 145

Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai dai kamar yadda suka alƙawarta lokaci ya zo da zasu maiduguri , idan ya so bayan dawowar su sai ta shiga jami'a kamar yadda samy baby ta sake ƙwaɗaita mata a cewar ta jami'a shine mataki na gaba da ya dace da yakaka , duk a ƙoƙarin ta na son janye ta zuwa kan turba irin ta ta , da take ganin fa a yanzu lokaci yayi .

Ƙofar da ake bugu da ɗan ƙarfi ya sanya ta firgita ta dawo daga nisan tunanin da ta tafi .

Duban agogo tayi ta ga ƙarfe goma sha biyu na rana ,

  Fitowa tayi da nufin zuwa ta buɗe ƙofar da take hasashen dawowar samy baby .

   Har lokacin ana yayyafi yif-yif da alamun yau yinin na marka-marka ne .

     Da ɗan gudun ta ta ƙarasa bakin ƙofar ta zare sakatar ƙofar ba tare da ta waiwaya ba ta juya da gudun kar ruwan sama ya taɓa ta tana cewa

   Sannu da zuwa anty samy .

   Sai da ta tsallaka kan Balcony tukun ta juyo ,

     A tsorace ta kai duban ta ga mutumin da yake tsaye a maimakon samy baby ,

    Saurayi ne dogo wankan tarwaɗa yana tsaye ya zura hannun sa cikin wondon jikin sa , idanun sa sakaye cikin wani kwafcecen baƙin gilashi da kallo ɗaya za'a masa a fahimci rangwamen mutumcin dake tare da shi .

   Juyawa tayi da sauri ta tura ƙofar falon ta shiga sabods tunowa da tayi da riga da wondon da suke jikin ta na bacci da duk da cewa basu kama ta ba ko kaɗan amma kaya ne masu tsantsi.

   Kai tsaye ta shiga ɗakin ta ta fara bincikar hijabin ta ,

   Sai dai hannun da ta ji ya sauƙa a ƙafaɗar ta ya sa hantar cikin ta kaɗawa ,

  Da sauri ta jaa baya har tana gwaruwa da jikin wardrobe ,

  Idanun ta ya shiga cikin na saurayin da ta bari a waje ,

    Anty samira bata nan

ta furta haka , muryar ta na karkawa , lokacin da take ƙoƙarin zira hijabin da ta samu nasarar ɗauka ,

   Riƙe hajibin yayi da hannun sa ɗaya , yayi amfani da ɗayan hannun sa wajen zare gilashin idanun sa , mitsitsin jajayen idanun sa da suka sake shigewa ciki-ciki suka bayyana , yana bin ta da wani shu'umin kallo

   Da muryar sa irin ta mashaya , yace

  Wa yake ta samira tsahuwar guzuma ?
   Ga kamar ki gorgeous , ya ƙarasa zancen yana kai hannu zai taɓa kumatun ta ,
   Da ƙarfi ta make hannun sa gami da saurin zura hijabin ta ,

   Ni ba ƴar iska ba ce kar ka sake taɓa ni , ka fita min daga ɗaki ,

  Ɗan baya ya jaa yana yarfe hannun sa da ta buge bakin sa a ɗan buɗe alamun mamaki ,

   Baby har da duka ??

Bata kula shi ba ta haura ta kan gadon ta ta dira tana nufar ƙofa , sai dai taku biyu kawai tayi ta ji ya kamo ta ta baya ya haɗa bayan ta da ƙirjin sa ya ɗaga ta ciɗak , ya shiga juyi da ita ,

    To tunda wasan tsale tsalle kike so bari na miki hajijiyar ƙauna .

    ya furta haka yana ɓaɓɓaka dariya .

Tun ƙarfin ta ta fara ihu tana wutsil-wutsil da kafafu tare da ƙoƙarin son ɓanɓare hannun sa da ya zagaye cikin ta da shi ,

A guje samy baby da tun a tsakar gida ta fara jiyo ihun yakaka ta ƙaraso cikin ɗakin .

    Kai kamal meye haka ?  kayi hauka ne ?? Dallah sauƙe ta .

   Ba tare da ya sauƙe ta ba ya ce

  Ke dallah kauce ki ɗan sakayo mana ƙofa zamu buga ƙwallo ne ni da wannan me zafin kan da tayi gigin duka na .

  Ƙarasowa tayi ta jaa hannun sa ,
   Kamal kar muyi haka da kai dan Allah ka sauƙe ta , ƙanwa ta ce fa , yaushe muka fara ƴar haka da kai mutumina ??

  A hankali ya sassauta rikon da yayi mata kafin ya sake ta tana jin ya ajiye ta ta fita a guje , ƙafafun ta ko takalmi babu ,

  Kallon baka kyauta ba samy baby ta wurga masa kafin ta ja ƙaramin tsaki ,

Kai dai kamal anyi tantiri ɗan iska , to bari na faɗa maka wannan haja ce me matuƙar tsada ba irin taku ba ce domin kuwa sabuwa ce fil , ba'a riga an shiga kasuwa da ita an daka mata wawa ba ,

   Ba ta wasa bace na san a ɗan abunda ya shiga tsakanin ku a yanzu kaɗai ,laushin fatar ta da ka taɓa ya isa sanar da kai irin maɗuɗan da zasu taho ta hanyar ta muddin ta shiga kasuwa .

     Ƙafar sa ɗaya dake sanye da wani ƙwamemen takalmi sau ciki ya ɗaga yana tokare ta da jikin gadon yakaka .

Ni kuma kin san maƙudan da kike faɗa ba matsala ta bane , ko ruwan su kike so nayi miki kin san zan iya , muddin zan mayar ƙwaɗayi na akan wannan nunanniyar gwandar , nawa kike sa mata kuɗi ??

  Two Million Naira
   Ta furta cikin gatsali

Bani account number da zan zira miki su ,
 
   A ɗan jirkice ta dube shi cikin ran ta tana son ƙure shi , domin kuwa duk da sanin da tayi wa kamal na shahararran ɗan masu hali da iyayen sa suka gama gurɓata tarbiyyar sa , ya zama tamkar ɗan taure wajen bibiyar mata , manya da ƙanana kyakkyawa da mummuna shi baya zaɓe kawai dai idan ran shi ya biya ya samu ya maida mugun yawu shikenan kuma bai ƙara bi ta kan mace , bata zaton wasan sa da kuɗi ya kai ya haka .

   A ɗage ta karanto masa account number da suna , cikin abunda bai gaza mintuna biyu ba sai ga wayar ta dake cikin jaka ta ɗau ƙara ,

Jikin ta na mazari ta fiddo wayar ta duba ,
   Alert  ne na adadin kuɗin da ta buƙata cif .

    Ɗan wara ido tayi da sigar mamaki , sai kuma ta kaɗa idon cikin yanayi na shanye mamakin ta irin na gogaggun matan bariki .

    Babu shakka ka ɗau haja me girma , kuma na san baza ka yi wadarai da ita ba , yaushe kake buƙatar ta ?

   Haɗe fuska yayi kafin ya watsa hannu
   Ka duba wannan da wata maganar iska ? Irin waɗannan kuɗaɗen da na cire har sai kin min iyaka da ita ? Ai yadda ta sani haɗiyar mugun yawu dole daren yau na fanshe kuɗi na , daman ga gari ya ɗau sanyi yanayi ne na shiga daga ciki da sauri .

Ta saki Wata dariyar da take bayyana farin cikin ta akan kuɗaɗen da ta samu da dama tana tsakiya da buƙatar su ,

   Alhaji kamalu ,  to baka da damuwa ,  yanzu ka tafi , sai ka aika mun address ɗin da kake son na kai maka ita ni da hannun na zan miƙa maka ita anjima da dare ,

  Kasan na faɗa maka sabuwa ce bata harkar nan to sai na maka yaƙin shawo maka kan ta ,

ÆŠaga kafaÉ—a yayi cikin nuna halin ko oho ,

     Ni dai ki tabbatar kin mata Wankan irin yadda ya kamata
   Ya ƙarasa zancen yana kashe mata ido ,
    Alhaji kamalu , kar ka ji kome .daren yau na kai ne a sama .

Yakaka wacce take zaune dirshan a cikin ruwan sama ta jikin bangon ɗakin ta ta baya  ,

  Ta kai hannuwan ta duk biyu ta toshe bakin ta a ƙoƙarin ta na hana kukan da take fitowa sarari kar su samy baby su ji , kamar yadda duk zantukan su ya ratsa kunnuwan ta .

  Ashe daman anty samy yaudarar take akan kome , ashe burin ta ta tsundumata cikin irin rayuwar da tunda ta fahimci girman saɓon da ake aikatawa ta hanyar zina take yi mata addu'ar Allah ya sa ita ma ta tuba ta daina ,

Manufar ta ashe ta mayar da ita ga aikata zunubin da tayiwa ubangijinta Alƙawarin ta daina baza ta sake ba !

Ƙuka take da hawaye wani na korar wani , tana jin yadda tsoro ke mamaye ran ta , tsoron kowa da kome , tsoron sake yin zina ta hanyar tirsasawa ,

Takurewa tayi ta sanya fuskar ta tsakanin ƙafafun ta , sanyin ruwan da ya ɗan sake dawowa da ƙarfin yana ratsa ta ta hanyar jiƙa kayan jikin ta .

Assalamu Alaykum .

Gaisuwa tare da fatan Alkhairi a gare ku baki daya!

Nagode.

  

      
   

 

 Fikra writers association

MAFARI
( Hargitsin Rayuwa)

umm'muaz

34

Fiye da awa É—aya Samy baby ta kwashe tana shirya Yakaka , wacce ta sha fama da kanta kafin ta iya tsayar da hawayenta batare da bari Samy baby ta fahimci cewa ta san manufar ta ba ,

Wacce ta shagaltu wajen shirya ta tana jaan ta da hirararrakin da suka shafi jin daɗin duniya , wankan da kansa so tayi ta wanke ta sai dan ganin ba fuska ya sanya ta tsayawa daga bakin ƙofar banɗakin tana sake jaddada mata ta fa yi wankan nan siral ta fita , domin inda zasu tafi waje ne na manyan ƴan gayu kar ta sake tayi abinda zata jawa kan ta raini ,

  Daga cikin banɗakin nan ta ci kukan ta a ƙarshe ta tattara duk wani tunani nata da Allah ya mata baiwar sa ,ta matse ƙwaƙwalwar ta, ta haɗa kai da bango akan tunanin hanyar da zata bi ta samarwa da kan ta mafita .
Chapter 145 · 0% Book details