← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 176 OF 269

Sashe 176

Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

To amma kuma shi ya zai yi ne? Ji yake kamar an raɓa ƙwaƙwalwarsa da duk wata tunani .

Cigaba yayi da tsayuwa a wajen ya gaza motsawa

Hannuwan ta ya ji sun ratsa kirjin sa daga bayan sa ta rungume shi , tare da kwantar da kan ta a bayan sa ,
Cikin sanyin muryar ta tace

"Baban Mama tun ɗazu nake jiran ka , kazo muyi Sallah mu godewa Allah , akan wannan babban arziƙi da ya bamu .

Hannu ya kai ya zagayo da ita ta gaban shi ,

Kallon fuskarta da take ɗauke da tsantsar farin-ciki yayi , suɓul da ita sai ƙyalli take tare da wani irin haske na musamman da ta ƙara a 'yan kwanakin nan,

Ji yayi tsikar jikinsa ta tashi dawowar kalaman Tafeeda cikin kunnuwan sa yasa jinin jikin sa tsinkewa ,

"Fatima ina son ki dayawa , je t'aime tellement Fatima

Yace da wata irin murya lokacin da yake rungumeta tsam a jikin sa , yana fidda ajiyar zuciya a zahiri .

Ji tayi riƙon da yayi mata yayi tsanani da kyar take fidda numfashi  , dan haka ta motsa da kyar ,

"Baban Mama mu shiga ciki na zauna ,

Tana jikinsa suka taka zuwa cikin gidan ya zaunar da ita akan kujera , amma shi ya gagara zaman saboda tashin hankalin da yake ciki ,

"Baban Mama ...

"Fatima ku zauna a gida ke da Mama ku jiraye ni zan fita na sayo mana abubuwan buƙatu kadan yanzu nake dawouwa da gaugawa ba zan daɗe ba kin ji kou ?

A sanyaye ta amsa da "to , tana gyaÉ—a kai ,

Daga haka ya juya ya fita , ba tare da ya san inda zai tafi ba , kawai so yake ya zama shi kaɗai bai san ɗanɗanon shakuɗuwar farin-ciki da baƙin-ciki a lokaci guda ba sai yau ,

Bai san girma da tsoron da yake cikin rasa abunda kake so ba sai yau da layi yake shirin shatuwa tsakanin sa da abubuwa biyu mafiya soyuwa agare shi ,

Bai san da irin wannan tashin hankalin da yake sa É—imuwa ba sai da ya tsinci kan sa can nesa da unguwar da yake ba tare da ya sani ba ,

Tsayuwa yayi a ƙarƙashin Doguwar bishiyar (Pinus taeda) da duk ganyayyakin ta suka gama zubewa saboda sanyi ,

Hannun sa ya zira a aljihun rigar sanyin jikin sa cikin rashin sanin makomar rayuwar sa ,

Waye zai tallafa masa ya fahimce shi ? Tayaya zai yi bayani a fahimce shi cewa kome da ya faru gare shi ya faru ne bisa ruÉ—in shaidan da kaddara maigirma , kaddarar haihuwar Mama da Auren Fatima ?

Waye zai faÉ—awa ya saurare shi cewa Fatima ta riga ta zama mahaÉ—i na cikamakin farin-cikin rayuwar sa ?

Mama ɗiya ce jini daga cikin jinin jikin sa dake gudana ,ta yaya zai iya tsame ƙwayar jinin sa daga jikin sa ?

" daga gefe ya hango wani brewery ( wajen sayar da giya ) ya tsallaka ya shiga wajen ya zauna , akan É—aya daga cikin kujerun gurin , É—aya daga cikin ma'aikatan wajen ta zo da tare da gaishe shi ,

Kan sa yana kallon teburin gaban sa ya ce mata

Please bring a bottle .

bata tafi ba ta fara lissafo masa sunayen giyar da suke da ita, ya katse ta ,

  Bud Light

Bata jima da sai gata ɗauke da kwalbar giyar da ya buƙata da ɗan kofin gilashi , tare da farfasassun ƙanƙara cikin wani ɗan mazubi na gilashi .

Tsirawa kwalbar ido yayi yana jin ƙaruwar damuwar sa da yake zaton idan ya kurɓa giyar zata gusar masa da wannan damuwar , da rabon sa ya sha ya kai wasu shekaru ,

Ɓincine bakin yayi ya tsiyaya a kofin , tunani ya shiga yi irin nacin addu'a da ya dunga yi akan Allah ya nufe shi da daina shan giya , da ƙarfin addu'a da tirjiyar da yake yiwa shaidan aduk lokacin da ya ji jarabar son shan giyar, ya samu nasarar daina sha sam

Yau sanadin damuwar da giyar ce ta zama sanadin faɗawar sa domin ita ce sanadin kome gata a hannun sa yana son sake sha , wataƙila masifar da zata iya sake jefa shi ciki sai yafi wanda yake ciki s yanzu

Ajiye kofin yayi ya miƙe zumbur ! tamkar ya ga abun tsoro , istigfar ya shiga yi a zuciyar sa ,

Da hanzari ya zaro kuÉ—aÉ—en da bai san adadin su ba ya ajiye akan teburin ya kama hanyar barin shagon , zuciyar sa na tsananta bugawa ,

Ya kama hanyar komawa gida yana sake zurfafa a tunani ƙwarai yana buƙatar wani babba a cikin lamarin sa da Fatima , waye zai tintiɓa ?

Hajja , ita tafi kowa kusanci da Fatima a halin yanzu , yana buƙatar suyi magana shi da ita , ko ita zata fahimce shi ?

Wayar sa ya zaro daga aljihu ya shiga neman layinta , ƙira ɗaya-biyu ta ɗauka suka gaisa , tana tambayar sa su Falmata da Mama ?

Ya amsa mata da duk suna lafiya , sai kuma ya gaza fayyace mata cikin sa kamar yadda yayi niyya to ta ina zai fara ƙiran kan sa da mazinaci ? Kai bafa zai iya ba 
"Hajja ki fara shiri idan Allah ya kaimou nan da sati mai zuwa direba zai zou ku taho Niger mouna dawowa nan da kwanaki goma sha huÉ—u

Daga ɓangaren Hajja ta amsa da murnar jin zasu dawo ta san an samu nasarar abunda aka je nema kenan .

"Babu kome Babban soja zan yi shiri kafin ranar nayi sallama da yan uwa ,

"Nagode Hajja , zai zo miki da sakon da za ki bawa dangi ki kuma sayi abun buƙatar da kike so kafin ku taso ,

"Har da wahala kuma Haba ? To madallah nagode , nagode Babban soja ,

Suka yi sallama ta ajiye wayar , Yakaka wacce tare suke da hajja a kitchen suna hidimar girkin dare,  da duk hankalin ta ke kan zancen Hajja da ta ji tace zata tafi , ta ɗan matso kusa da ita ,

"Hajja tafiya ce ta kama ki ne ?

A kaikaice Hajja ta dube ta kafin ta cigaba da kaÉ—a miyar da take yi ,

"Eh Uwarɗakina Falmata ce zasu dawo daga Amurka , zan koma cikin sati mai kamawa ,  na gyara gidan kafin su iso ,

"Hajja nima zan je , zan biki na ga Falmata na , zan nemi izni wajen Baba .

Ba tare da ta jira amsar da hajja zata bata ba ta fita da saurin gaske , zuciyar ta maƙare da tasowar binannen bakin-cikin ta , lokaci ya matso na raba tsakanin ƙanwar ta , tare da ƴar ta,  da wannan mugun mutumin , mayaudari .

Assalamu alaikum ,

Da fatan duk kuna lafiya ? Nasan kun yi mamaki ko ? Haaaa , ina masu cewa sai wani watan zasu ga sabon update ?ha'aan kun ji kunya ko ? 😂

To ƙaƙa ƙara ƙaƙa ? Yau ina son jin ra'ayoyin ku pls ,

A gaskiya ghost readers sake bunƙasa kuke yi amma ba kome liti bad boy yana madakata shi da Hajja suna jiran ku 😂

Nagode .
[11/23, 5:46 PM] +234 706 635 0638: MAFARI

( Hargitsin Rayuwa )

umm'muaz

40

Cikin sa'a da Yakaka ta nemi izni wajen Prof kan ta bi Hajja zuwa wajen 'yar uwarta sai Prof bai hana ta ba , sanin cewa da yayi haƙiƙa akwai buƙatar su ga juna ita da 'yar uwar ta  .

Sai dai yayi mata jirwaye da kamar wanka , ya yi mata nasiha tare da jaan kunnen , a ƙarshe ya gindaya sharadin kar ta wuce kwanaki goma zuwa sati biyu a Niger ɗin ta dawo gida nan wajen sa ,

Cike da ɗokin sake ɗaura idanunta akan Halittun biyu mafiya soyuwa agareta ta fara shiri, duk wasu 'yan kuɗaɗen da take da su irin wanda Prof yake ba ta da wanda Rahima ke mata kyautar su da suka tasamma dubu goma sha biyar duk ta tattara su ta ƙulle ta nufi kasuwa ,

Sayayya ta shiga yi gefe guda na zuciyar ta na cigaba da saƙe-saƙen irin mummunan matakin da zata ɗauka akan Youssouf ,

Daga Jiya zuwa yau,  iyakar tunanin ta kan matakin da take ji zata iya ɗauka ya ƙare ne akan kawai abu mafi sauƙi shine ,

Idan Har sun hadu zata ce da shi, ya saki ƙanwar ta ya kuma bata 'yar ta , ko kuwa ta kai lamarin gaban iyayen sa , waɗanda ta riga ta san ko su , su waye ? ta san cewa shi ɗan sarki ne tun a lokacin da Samy Baby ta goranta mata akan sa ,

Ta san wannan ce kaÉ—ai madogarar ta , idan har ba haka ba ai ita bata isa jaa da shi ba .

Tana da tabbacin ba zai yarda asirin da yake tsakanin sa da ita ya tonu ba da ta riga ta san ya ɓoyewa mutane dayawa ciki kuwa har da Falmata ,

ita kuma ta shirya sanar da ita gaskiyar kome da ya faru tsakanin su da Youssouf ɗin, ta tabbatar daga lokacin da Falmata ta san kome baza ta sake yarda da shi a matsayin Miji ba , za kuma ta taya ta su ƙwato Mama suyi dawowar su nan.

Da tunanin hakan ta ƙaraso wajen sayar da Takalman mata da yara irin na roba masu sauƙin kuɗi ,

Tafi son ta saya musu 'yan kayan sanyawa a jiki musamman dayake bata san yaya rabuwar ta su da shi Mayaudarin zai kasance ba ,

wataƙila suyi irin rabuwar da yayi da ita a baya , watau ya yasar su akan titi babu ko suturun kirki ya kora su .

Dan haka ya zama dole ta yi musu guzurin kaya daga Falmatan Har Mama .

Daga wajen 'yan takalman inda ta ɗauka musu ƙafa bibbiyu duk da cewa kintata tayi ta auna girman ƙafafun su a tunanin ta ,

Sai ta nufi wajen 'yan kayan yara , nan ma ta auna da girman Mama da ta gani a hoto ta saya mata shiga biyu masu sauƙin kuɗi ,
Chapter 176 · 0% Book details