← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 123 OF 269

Sashe 123

Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

  A hankali ya ɗago kan sa yana duban sashin falmata daidai lokacin da ta kai ƴan yatsun ta tana ɗauke hawayen da ya biyo kan kumatun ta ,
          Tausayin ta me ƙarfi ya taso masa ,
     Fatimah ,
Ya ƙira sunan ta a ƙasan maƙoshi

  Sashin da take jin tashin muryar sa ta waiga ba tare da ta amsa ba .

  Meyyasa ba'a sanar da ni tashin ciwon mama ba ? Sai doctor ta ne daga nan ya ƙira ni yake sanar min ?

Muryata ƙasa-ƙasa ta ce

    Hajja ce ta hana a faɗa ma tace duk shekaranjiya ka tafi daga niamey , !

     Miƙewa yayi tare da ƴar sa a kafaɗa bai ce kome ba , sai da ya kai bakin ƙofa yace mata

    Bari mu tai ga likitan ta !
     Bai jira amsar ta ba ya fice daga ɗakin .

   Kichiɓus suka yi da hajja wacce take kan hanyar dawowa ɗakin bayan ta ɗan zaga ta motsa ƙafafun ta.

Riƙe baki tayi nuna alamun mamaki !

O Ni , yanzu ashe Babban soja sai da ka taho ? Kai da shekaranjiya jiyan nan ka tafi bakin aiki ? Banda abunka ai mun riga mun saba mun kuma fahimci kan ciwon mama tana fara nuna alamun rashin lafiya da hanzari muke zowa da ita asibiti , ai da kayi zaman ka bakin aiki .

Gaishe ta yayi a ladabce
   ta amsa da sakakkiyar fuska .
  Babu kome hajja ai lafiyar mama ta sa'a wuce aiki muhimmanci bari mu je ga likitan ta .

   Bayan dogon bayanin da kamar maimaici ne gare shi akan cutar ƴar ta sa wacce take ɗauke da ciwon Amosanin jini , " da a turance ake ƙiran sa da Sickle Cell Anemia,

Ya ɗora da yi masa bayani akan binciken da shi youssouf ya sanya likitan ya yi masa akan wannne asibiti ne mafi kyaun kayan aiki tare da ƙwararrun likitoci da zai iya kai ƴar sa ayi mata aikin da ake sanya ran idan har anyi sa da dacewa masu cuta irin na ta kan iya warkewa baki ɗaya .

Fitaccen asibitin nan a duniya da yake ɗauke da ƙwararrun likitoci dake ƙasar amurka ,"Mayo Clinic ," shine asibitin da likitan ya tabbatar da ƙwarewar su akan aikin dashen ɓargo  ga marassa lafiyan da ya shafi manyan cutukan cikin jini .

Miƙawa likitan hannu yayi suka yi musabaha lokacin da yake miƙewa akan ƙafafun sa domin barin ofishin .

Likitan ya kai duban sa ga mama wacce tayi luf a jikin baban ta tana wasa da adon gaban rigar sa na soji .

Madame Safiyya Baskore sommes-nous bien maintenant? pas plus d'injection non?

   dariya  tayi kafin ta amsawa likitan dai-dai lokacin da suke ƙarasa barin ofishin ita da baban ta .
   oui je me sens mieux maintenant plus d'injections .

Dariya likitan yayi yana É—aga mata hannu alamun ! bye bye !
     A hankali ta motsa laɓɓan ta tana kwantar da kan ta kan kafaɗun baban ta
  au revoir ! ( Bye ) ..

  

   Assalamu Alaikum kowa da kowa !

   Surprise ??  😂

Ina gaisuwa agare ku baki daya masu karatun da suke faranta min wajen Danna dan tauraron nan tare da ajiye min sharhin su a karkashin kowanne shafi na rubutu na,  ina son Sanar da ku cewa ina godiya me dinbin yawa agare ku.

Okay ghost readers, Makaho bai San Ana ganin sa ba sai an zungura shi ko ?? 😠

Kun san bakwa kyauta min koh? 
  
Amma ba kome a dai juri zuwa rafi wataran tulu zai fashe,  😂
[9/3, 10:14 PM] +234 806 122 1116: Fikrah writers association

MAFARI
( Hargitsin Rayuwa )

Umm'muaz

33

Wannan shafin na bada tukuicin sa baki daya ga " ZULAIHAT RANO " MEELAH " RALIYA GARBA. #I MORE THAN APPRECIATE YOU SISTERS#

Bayan an sallami mama daga asibiti sun dawo gida , idan banda lelen ta babu abunda falmata take rabon ta da makarantar ta ma yau kusan sati guda kenan ,

Domin duk yadda hajja ta so falmata ta tafi makarantar ta bar mata kulawar mama ta ƙiya ,

gani take daga ta matsa daga kusa da ita ciwon nata zai iya tashi .

A zaune suke a falo hajja tana kishingiÉ—e tana hutawa bayan ta gama Æ´an kananun aiyukan ta na safe ,

Mama tana kalmashe bisa cinyar falmata , wacce take bin duk gaɓoɓin maman tana tausa mata su sannu a hankali , jikin ta sanye da ruwan hodan kayan sanyi na yara mata me adon ƴan ƙula-ƙulai farare , ƙafafun ta a ƙunshe cikin fararen safar ƙafa .

Biyamuradi ya shigo falon , a shirye yake tsaf cikin kakin sa na soji , fitowar sa kenan daga sashin sa da yake sabon gidan da ya saya musu wanda ya fi wanda suka fara zaman haya a cikin sa girma da tsari , domin wannan sashi uku ne da shi ƴan madaidaita , sashin da su falmata suke da sashin baƙi wanda ba'a amfani da shi sai kuma sashin biyamuradi da idan ya zo garin yake sauƙa a cikin sa a wasu lokuta , musamman a lokacin da ya tarar da rashin lafiyar mama , wasu lokutan kuwa a hotel yake zaman sa .

Mama tana jin sallamar sa ta miƙe daga jikin falmata wacce take ƙoƙarin riƙe ta ,
Mama ki tafi a hankali kin ga ba wani ƙwarin jiki kika samu sosai ba ,

Bata kula ba
Ta taka da ɗan gudun ta , da sassarfa shima ya ƙaraso ya chafe ta sama ya cillata ,

Yana juyi da ita kafin ya sauke ta zuwa ƙirjin sa yana dariya ,

Bonjour papa , ina kwana papa .

tace daidai lokacin da take kai hannu tana ƙoƙarin cire hular kan sa ,

Taya ta cire hular yayi ya É—ora mata bisa kan ta da aka mata manyan kitson kalba suka zubo har kan kafaÉ—un ta ,

Bonjour mon cher ," yaya kin ka tashi ?
Lafiya papa
tace da shi daidai lokacin da take ƙoƙarin sauƙa daga ƙirjin sa ,

Ya sauƙe ta yana riƙe da hannun ta suka ƙarasa cikin falon , ya samu mazauni kan ɗaya daga cikin kujerun wajen yana gaisawa da hajja wacce ta miƙe zaune daga kishingiɗar da tayi ,

Kamar yadda ta saba , yanayin ta babu walwala idan har yana waje ta gaida shi , tana riƙo hannun mama wacce take ƙoƙarin ajiye mata hular baban ta a kai ,

Bata iya hana ta ba sai da ta É—aura mata hular akan hular da take rufe akan ta wacce take mahaÉ—in doguwar rigar jikin ta ruwan madara me É—an nawi saboda tashi da aka yi da É—an sanyi garin sakamakon ruwan sama da aka kwana yi daren jiya .

Shafa fuskar ta mama tayi , kamar yadda yake al'adar su ita da mamar ta .

Maama kin yi chau dayawa ,
Papa ka ga maama na tayi chau , donne-nous des photos ,

ta ƙarasa zancen tana hayewa kan kujerar da falmata take ta zagaya ta bayan ta gami da sarƙafa hannuwan ta biyu ta wuyan falmatan ta cusa fuskar ta gefen wuyan ta .,

Biyamuradi wanda ya fara yiwa hajja bayani game da shirye-shiryen da yake na tafiyar su US , ya juyo da duban sa kan su idanun sa suka sauƙa kan fuskar falmata wacce haƙoranta ke buɗe tana murmushin da yake bayyana farin cikin ta da ganin walwalar mama ya assasa mata ,

Kamar maganaɗisu ya riƙe shi , ya kasa janye idanun sa daga kan ƴar fuskar ta da komen ta yake ɗan madaidaici idan aka cire manyan idanun ta ,

Ba tare da ya iya É—auke ido daga kallon ta ba ya zaro wayar sa daga aljihu , ya juyo baki É—ayan sa ya saita cemara ya haska musu hotuna wajen kala shidda ,

Da gudu mama ta sake sauƙowa ta dawo wajen baban ta , tana cewa zata ga hoto ?
Ta É—are cinyar sa ,
Batare da ya sake mata wayar ba ya nuna mata hotunan , da sauri ta sanya hannu tana sake tura huton gaba , fuskar wata Æ´ar baby me kyau kamar ta ya cika fuskar wayar , Æ´ar yarinya ce da bata wuce shekaru biyu ba tana tsaye a hoton ,

A hankali mama ta É—ago kan ta tana duban fuskar sa

Papa bebe waye ?

Zare wayar yayi daga hannun ta ba tare da ya bata amsa ba, daidai lokacin da hajja ta ke cewa ,

Wannan yarinyar da surutu kike kamar aku , duk kin bi kin tsare shi da surutu kin hana shi ya yi magana , bayan kuma yayi shirin tafiya aiki , ni zo nan ki zauna na miki tafiyar tsutsa a ƙafar ki .

Sauƙa tayi daga jikin sa , maimakon ta tafi wajen hajja , sai ta nufi mamar ta , tana zuwa ta zauna a gefen ta gami da kwantar da kai a jikin ta tayi shiru ,

Boyayyar ajiyar zuciya Biyamuradi yayi , cikin ran sa yana hamdala da hajja ta katse masa tambayoyin mama , domin Alƙawari ya ɗaukarwa kan sa ba zai taɓa yiwa ƴaƴan sa ƙarya ba , akan duk wata tambaya da suka masa , sai dai ko ya sakaya amsar idan kaifin hankalin su bai kai su fahimce ta ba , amma a yanzu bai shirya amsa ba ga tambayar da mama tayi ma sa .

Cigaba da yiwa hajja bayani yayi , inda yake sanar da ita , yana son ranar litinin ya zo su je ayiwa falmata da mama passport , zai fara nema musu visa

Idan Allah ya yadda daga sun samu visa shi da su zasu tafi US , da ba zai wuce tsawon nan da wata É—aya da Æ´an kwanaki ba nan gaba ,
Chapter 123 · 0% Book details