Sashe 78
Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ba su suka fito daga maɓoyar su ba , sai da suka ga gari ya fara duhu , daga inda suke suna iya jiyo kiraye-kirayen sallar magariba , ga kuma hayaniyar da suke ji da ke nuni da cewa ƴan bikin ne suka dawo ,' daga wurin party ,"
Da rakaɓe-rakaɓe suka bullo ta cikin gidan , iya ganin su mutane ne ko ta ina da alama an samu ƙaruwar wasu baƙin ,"
Suna tsaye daga gefen kofar falon suna shawarar su shiga ko su koma maɓoyar ta su kawai su kwana a chan , tun da sun san dai ko sun shiga falon basu da takamaimai wurin kwana ," !
Yauwa , fatima , yakaka tun ɗazu nake neman ku , gaskiya kun wahalar da ni kusan ba ɗakin da ban duba ba a sashin mu , ina kuka shiga haka ?ko kun fita ne ? Cewar rahima wacce take ƙarasowa wurin su .
Muna daga nan bayan É—akuna rahima , kiyi hakuri bamu san kina neman mu ba ,! Har kun dawo ?
Mun dawo , daman big bro ne ya ce duk inda kuke na neme ku , kun ci abinci ne ?
Yakaka ta girgiza mata kai ," bamu ci ba ,"
Yauwaa toh ku zo muje ciki ga abincin ku chan na sa an É—ibar muku,!
Ta cikin falon suka shiga suna biye da ita , suka nufi ƴar hanyar nan da ta hau sama ," suka bi ta ƙafar benen suka haura cikin wani babban falo wanda ya ƙawatu da kayan alatu , da manyan kujeru da tsadaddun labulaye , ga ƙofofi birjik a cikin sa ,"
Nan ɗin ma dai duk tawagar ƴan matan ne wanda ga alama sun yi ƙaura daga ƙasan ne sun dawo saman ,"
Dararrakin su da shewa sun cika wurin banda É—an wani sassanya sauti da yake tashi a cikin falon ta cikin wasu mulmulallun sifika da suke a kowacce kusurwa na falon ,"
Daga bakin kofa su yakaka suka jaa tunga, rahima ta kutsa kan ta ciki ba tare da ta lura da sun dakata daga bin ta ba ,"
Kai tsaye ta nufi wata Æ´ar hanya sai ga ta ta bullo cikin É—an Kitchenette É—in duk da cewa babu wasu tarkace a ciki , amma Kitchen Cabinet É—in kan sa abun kallo ne , kwarai Kitchenette É—in yana da É—aukar hankali , kamar yadda kome na sashin yake da mataukar tsari da kyau , fiye da na ko'ina a gidan , kai tsaye ta É—auko Æ´an madaidaitan coolers É—in biyu ta fito da su ,'
", turis ta jaa ta tsaya lokacin da ta lura babu su yakaka a wurin ,"
Ina suke ??",
  ta furta a sarari .
Su waye ?
Hafsa ta tambaye ta daidai lokacin da ta kai hannu tana ƙoƙarin karɓar cooler ɗin hannun ta ,"
Ta janye tana bata amsa da ,"
su yakaka da fatima tare da su fa muka hawo saman , wannan ma abincin su ne da big bro yace na É—ebo musu tun É—azu ,"
Yamutsa fuska hafsa tayi ,"
Su waye kuma fatima ? Ita har ga Allah ta ma manta da sunayen su takamaimai ,"
C'mon bani abinci naci daman yunwa nake ji tun breakfast wani abun kirki bai sake shiga ciki na ba, "
nima wallahi yunwar nake ji cewar wata daga cikin ƙawayen su da take kishingiɗe a gefe ,"
Ƙanƙance idanu rahima tayi ,
Ki rufa min asiri malama kar ki jawo min fushin big bro , domin sai da ya daÉ—a jaddadamin na basu abinci...
Kewaye su tayi ta wuce
Bata saurari hafsa É—in ba da take bin ta da tambayar
Wai su waye ne waÉ—an da kike ta ambato ,"
Leƙawa tayi ta gan su a rakuɓe daga gefe ,"
Haa'ah ya kuka tsaya anan yakaka ?
Ku shigo mana ga abincin naku ,!
Toh !
Suka amsa suna masu sanyo kafafun su cikin falon ,"
A É—age hafsa take jifan su da kallon tuhuma ,"kallon ku kuma me kuka zo yi nan ??
Ku zauna ,' rahima ta umarce su tana musu nuni da kan haÉ—aÉ—É—iyar shimfiÉ—ar dardumar da take shimfiÉ—e tsakanin kujerun gurin ,'
 A ɗarare suka zauna falmata ta matsu da jikin yakaka a saboda ji da take idanu sun yi yawa a wurin ,"
  Yakaka ma kan ta a sunkuye yake saboda kallon banzan da sofi take jifan ta da shi a tun ƙarasowar su falon ,"
 Ba tare da karsashi ba suke chakalar abincin duk kuwa da uwar yunwar da taje sasuƙar ƴan hanjin su da kuma yadda abincin yake da matuƙar daɗi ya wadatu da kayan girki na alfarma ," amma idanun jama'ah ya musu shamaƙi da jin dadin abincin ,
  Ƙarar wayar rahima ita ta dawo da sofi duniyar tunanin da ta lula na son hasaso meye ne a tsakanin doctor hamza da waɗannan yakubayin talakawan ƴan gudun hijirar da har yayi musu matsauki a cikin gidan su ya kuma jiɓanci lamuran su da matukar muhimmanci haka ?? ,"
Hello big bro ,"
 Gasu nan muna tare ma ," cin abinci suke ,"
  Rahimar ta kai kallon ta ga yakaka wacce kan ta yake sunkuye ,"
  Eh tana ci sosai ma ," to idan sun gama zamu zo yanzu ,"toh !
 Â
  Yakaka wai inji yayan mu idan kun gama cin abincin muje yana ƙiran ku ,"
  Toh suka haɗa baki wurin amsa mata ,"
   Ba'a kai mintuna uku ba falmata ta zare hannun ta tare da faɗin ta ƙoshi , ita kuwa yakaka daman ba wani na kirki take ci ba ," dan haka ita ma ta miƙe bayan ta tattare ɗan abincin da falmata ta zubar ,"
  Ƙarƙashin rakiyar kallon rainin da mafi akasarin ƴan matan wurin ke bin su da shi suka ƙarasa barin falon suna jin su wasai tamkar an cire musu wani mugun dafi da idanun jama'ar suka zuba musu ," daga yakaka har falmatan ba masu son mutane bane ,"
rahima ta jagorance su zuwa wurin da doctor hamza ya ce su same shi ," daga kusa da kofar sashin sa ,"
  Tun kafin su ƙaraso ya nacewa kallon fuskar ta , da ita kuma ta shagaltu da kallon haɗaɗɗun motocin da suka cika harabar gidan wannan tana wace waccen a haɗuwa ,",
 Suna ƙarasowa suka gaishe da shi , ya amsa tare da haɗa musu da tambayar babu dai wata matsala ko ? Kuma sun ci abinci sosai ko ? Suka tabbatar masa da basu da matsalar kome sannan a ƙoshe suke ,"
  Manyan ledojin da aka zubo musu kayayayyakin su da ya saya musu na fitar bikin ya miƙa wa rahima , gami da wata madaidaiciyar leda mai ɗauke da tambarin ', down town, "
  Ungo rahima wannan kayan nasu ne na fitar biki , ki dunga taya su shiryawa ,
  Ta sanya hannuwan ta biyu ta karɓa tana ƴar dariya ,"
  Eyeeh gobe su fatima za'a chanchare gaskiya fatima kin kwace min fada wurin big bro ," ta ƙarasa zancen da sigar zolaya , tana kashe idon ta ɗaya ,"
   Ɗan murmushi su duk biyun suka yi cikin ran su suna jin daɗin kulawar da yake basu tare da kyautatawa , hakan ke ƙara sa yana sake girma da ƙima a idon su ,"
   Ba tare da ya kula da zantukan ta ba yace ,"
  Ga shi
tare da miƙa mata ƴan mukullayen sashin sa , daga yau zuwa lokacin da za'a kammala bikin ku dunga kwana ke da su a sashi ne , daga ke sai su , bance ki haɗo min gayyar ƙawayen ki su ɓata min waje ba , ki kiyaye ,"
   Ya ƙarasa zancen da sigar gargaɗi fuskar sa babu alamun wasa ,"
  Toh
  Kai kuma aina zaka dunga kwana ?
 Tare da baƙi a sashin baba ya amsa mata yana barin wajen ," bayan ya basu umarnin su tafi su kwanta dare ya soma shiga ,"
  Da zumuɗi rahima tayi gaba suka bi ta a baya ,
  Tab lalle yakaka ku ƴan gatan big bro ne , baya fa son kowa ya shigar masa sashi , kana shiga zai fara korar ka kar ka kai masa datti , daga ka fita kuma sai yayi shara ya goge kujerun sa , bala'in tsafta ce da shi kamar mai aljanun tsafta ," ta furta hakan daidai lokacin da ta sanya mukulli ta buɗe ƴar babbar kofar mashigar sashin nasa ,"
   Suna sanya kafafun su ciki ," kowaccen su tana gaskata kalaman rahima da ta ce yayan ta mai bala'in tsafta ne , saboda tuno haɗuwar su ta farko yadda ta kaya a tsakanin su , ta yadda ya fututtuke ya ci mutuncin su akan ƙazantar da falmata tayi masa a ofishin sa , wanda a lokacin da za'a faɗa musu doctor hamza mutumin kirki ne mai tausayi da kyautatawa irin yadda yake musu a yanzu zasu ce ,"ƙarya ne ," to ashe aljannu tsafta ne da shi , kamar yadda suka ji daga bakin ƙanwar sa ,"
 Ƙamshin furanni tare da sanyin ban ruwa da aka yi a wurin zuwa wani ƙamshi na musamman da yake tashi a ƴar harabar sashin nasa suka haɗu suka bayar da wani irin yanayi mai daɗi tare da samar da nutsuwa ga zukata , "
  Lumshe idanun ta yakaka tayi ta buɗe tana mai yawo da idanun ta a kowanne kusurwa ta wurin , ƙwarai yanayin wajen da tsarin sa suka burge ta ,"
  Ƴar barandar da take ɗauke da ƙofar falon nasa rahima ta taka ta buɗe kofar tare da tura ta ta sanya kai tana cewa su yakaka ," su shigo ,"