← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 269

Sashe 11

Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hanyar da mutumin nan ya gwada mata ita su yakaka suka kama," suna tafe basa jin motsin kowa sai kukan tsuntsaye ," É—an turus yakaka tayi ganin hanyar bakin jeji sosai ta kawo su ," jin sun tsaya ne ya sanya falmata wacce ta fara gajiya tace yakaka har mun kawo Maiduguri ne ? Cikin sanyin murya yakaka tace falmata gani nayi hanyar da muke tafiya a kan ta ta kawo mu bakin jeji ," jin batun jeji ya sanya falmata sake cukumo rigar yakaka tare da cewa mu koma kawai yakaka ," na faÉ—a miki daman kar mu taho ,"

Jin takun tafiya tare da hayaniya kamar har da kukan yara da suka ji shi ya sa su saurin juyawa " wasu gungun mata (sun fi su goma ) tare da yara da namiji guda É—aya suka hango ," bisa ga dukkan alamu su ma a jigkace suke daga su sai kayan jikin su ," wucewa suka yi ta gaban su ba tare da sun ko kula da su ba ," cikin sauri yakaka ta saki hannun Falmata tare da cewa ", bari na tambayo su koh su ma maiduguri suka nufa ," da É—an gudu ta cimma su saboda saurin da suke zabgawa cikin harshen su take tambayar su ," ko maiduguri za su ?" Ba tare da sun waiwaye ta ba É—aya daga cikin su ta bata amsa da ",Eh ",

Da gudu ta koma baya gami da kamo hannun ƴar uwar ta tana jaan ta tare da cewa zo mu tafi falmata mun samu abokan tafiya waɗan nan mutanen su ma maiduguri suka nufa ,' ita dai falmata bata ce ƙala ba ta bi yakaka suka faɗa jeji tare da bin bayan mutanen nan da har sun fara yi musu nisa cikin duhun ciyawa ,"

Doguwar tafiya suka yi sosai cikin ƙungurmin dajin nan da yake cike da itatuwa da ciyayi gami da ƙayoyin da suke ta faman huda musu takalman su suna sukar kafafun su, ba sa cewa ƙala a tsakanin su ," har zuwa lokacin da rana ta ɗan gota tsakiya alamun azahar ta yi ", namijin ciki shine ya basu umarnin tsayawa a dai-dai wani wurin da ruwan sama ya ƙwanta yayi kamar ƙaramin kududdufi " , cewa yayi a huta a sha ruwa sannan ayi sallah a cigaba da tafiya ,"

Yaraf ,'duk suka zazzauna wasu ma kwanciya suka yi warwas a ƙasa ,kallo ɗaya za'a yi musu a fahimci tsabar gajiya da yunwa a tare da su ," yaran ciki kuwa daman tuntuni suke kukan yunwa da kishirwa dan haka ko da su ka ga ruwan nan , nan take suka nufi wurin wasu suka sa tafukan hannayen su biyu suna ɗebo ruwan suna sha wasu kuwa bakin su suka sa a kan ruwan suna sha ",

Yakaka da falmata suna cikin waÉ—anda su ke shan ruwan da hannayen su ,É—auro Alwala su ka yi bayan sun sha ruwan ," su ka kuma jira sauran matan su ma su ka zo sha ruwan tare da É—aura alwala ," namijin ya jaa su jam'i haka a cikin dajin ,"

Ƙarar wucewar wani abu me tsananin karfi da matsanancin ƙara da yake barazanar kashe musu dodon kunnuwa shi ya sanya a firgice ! Su dukkanin su, su ka ɗaga kai sama ba tare da sun sallame sallar da su ke ba ," yaran ciki kuwa nan take su ka fasa kuka tare da ƙanƙame iyayen su

Shawagi wannan abun da wasu daga cikin su , su ka ce "jirgi ne " ya cigaba da yi ," yayin da su kuma su ke tsaye carko carko , kawukan su a ɗage suna hango jirgin da yayi ƙasa ƙasa da har su ke iya ganin launin sa da yake koren kala , ruwan madara da kuma ruwan hanta "(coffee),"

Falmata lalubo hannun yakaka tayi tare da riƙe ta gamgam cikin karkarwar murya tace yakaka menene shi jirgin ?

Basu yi aune ba kawai su ka ji an saki wani abu kamar bom ," wanda ya faÉ—o kurkusa da mutumin nan da yake jagorar tafiyar su tare da wasu mata biyu da suke tsaye ,' nan take su ka tarwatse jinin su ya watsu a jikin sauran su ,"

wani irin kururuwa su ka yi a tare da yake nuna tsantsar firgicin su ," karo suka fara yi da juna cikin gigicewa suna masu neman hanyar gudu jin yadda jirgin nan ya sake sakin wanna abun da basu kai ga fahimtar harsashi ne ko kuwa bom ?,"

Fisgar hannun Falmata, yakaka tayi wacce take ta faman waige-waige tare da ihun tambayar yakaka me yake faruwa ? Ba tare da yakaka ta bata amsa ba ta fisge ta cikin ihun kukan da ƙarar jirgin nan ya dusashe ƙarfin sautin take cewa mu gudu Falmata idan ba haka ba zamu mutu ,"

Takawa su ke da matsanancin gudu suna jefa ƙafafun su wanda ko takalma babu "domin basu samu damar sanya takalman su ba " wurin da duk suka tsinci kan su nan suke jefa kafa basa duba gaban su bare su waiwaya baya ,"wasun su kuka da ihu suke yayin da tsiraru daga cikin su suke addu'a ," gudun ceton rai suke cike da tsananin tsoro tare da tashin hankalin jin kamar ƙarar jirgin nan na bin su  ,"

Cikin tsananin gudun da su ke ne yakaka taji hannun falmata da take riƙe da shi gam-gam suna gudun tare ," hannun ta ya fisge daga cikin nata lokaci guda kuma taga falmata tayi ƙundubala ta tafi gaba ɗaya ta faɗi ta gaba fuskar ta ta bugu da ya sa ba shiri ta saki wani irin ihun azaba tare da ƙwalla kiran sunan Allah ,"

Cikin kaɗuwa yakaka wacce har ta yi gaba saboda matsanancin gudun da suke ," ta dawo da baya da gudu gami da durƙusawa ta tallafo falmata wacce hancin ta da bakin ta ke fidda jini ," sai dai wata ƙarar da falmata ta sake saki a lokacin da yakaka take koƙarin ɗago ta ya sanya babu shiri ita ma yakaka ta fashe da matsanancin kuka ,"
Falmata sannu Dan Allah ki tashi
" ta furta hakan tana me gogewa falmata jinin da ya bata mata fuska da É—ankwalin kan ta da ta zame lokaci guda kuma tana me É—aga kanta sama tare da yawata idanun ta a sararin samaniya cikin tsammanin ganin jirgin sojojin nan ,"
Ƙafata yakaka ƙafata ta maƙale a rami wayyo Allah na yakaka zan mutu ,"
Falmata ta furta hakan a lokacin da ta ruƙo ɗayar ƙafar ta, take ƙokarin zaro ƙafar daga wani ɗan ramin da yafi kama da na "ƙurege" ko kuwa dai kananun dabbobi dangogin sa ",

Cikin tashin hankali yakaka ta sake fuskar falmata gami da miƙewa ta koma ta wurin ƙafafun ta ,"kokarin zaro ƙafar ta fara yi ,"idanun ta suna zubar hawayen tausayin kanwar ta da ya sa ta kusan mance halin tsaka mai wuyar da suke ciki ,"

A gigice ta É—ago kan ta ganin wani hannun da tayi ya kama kafar falmata "cikin taya ta kokarin zaro kafar ,"

ÆŠaya daga cikin abokan tafiyar su ce ," ita ma yarinya ce wacce zata iya girmewa yakaka da kadan ",

Da karfi su ka samu nasarar fusgo kafar falmata wanda hakan ya sa yakaka tayi faɗuwar ƴan bori akan ciyawar farar ƙayar da ta soki bayan ta ya sa ba shiri ta sake zabura ta miƙe gami da rugowa ta ɗaga kafar falmata wacce tayi futu-futu da ƙasa," ta ɗora akan cinyar ta ,"lokaci guda tana tambayar falmata kafar bata ji ciwo ba koh ," ?

Yakaka kamani na tashi mu gudu," Falmata ke furta hakan a lokacin da take laluben hannun yakaka fuskar ta tana bayyana tashin hankalin da take ciki ," da sauri yakaka ta miƙe bayan ta sauke kafar falmata daga jikin ta ,"yunkurawa tayi tare da ɗago ta ," ganin haka ya sa yarinyar da take tsaye a gefe tana kallon duk abun da suke ta matso gami da kai hannu ta kamo ɗayan hannun falmata da nufin taya yakaka ɗaga ta ,"

Wani irin zamiya falmata tayi tare da warce hannun ta daga jikin yarinyar wanda hakan yayi sanadiyar komawar su ƙasa da ita da yakaka ,a lokaci ɗaya ta kanƙame jikin ta wuri guda tare da cewa ,"
Yakaka waye a wurin nan tare da mu ? Aljanu ne koh ?

Falmata wacce ta taya ni muka zaro kafar ki daga rami ce É—aya daga cikin abokan tafiyar mu ........,"

******************

Kika ce kin san hanyar Birnin Maiduguri Yagana ? Tambayar da yakaka ta jefawa Yagana (abokiyar tafiyar su ) kenan lokacin da suke cigaba da tafiya ," sai dai saɓanin ɗazu yanzu a nutsen su suke tafiya ,"samun nutsuwar su ya samo asali ne daga fahimtar da suka yi jirgin nan ya tafi ya daina bin su ,"

Sai dai fa a yanzu zuciyoyin su cike take taf da tsoron ganin su uku ne rak a ayarin tafiyar su sauran duk sun watse kuma basu sake cin karo da ko guda daga cikin mata takwas da kananun yara biyar É—in da suka rage a ayarin nasu a bayan mutuwar namijin cikin su tare da mata biyun ba ",

Eh nasan maiduguri yakaka mun taɓa zuwa tare da yaakura na ( yayar mahaifiyar ta )

Sau goma kuka taɓa zuwa koh sau ashirin ," da a yanzu kika ce zaki mana jagora ? cewar falmata wacce take ɗingisa kafar ta gefe-da-gefen rigunan su ita da yakaka a ƙulle da na juna ,.

Sau ɗaya dai na taɓa zuwa tun lokacin ina shekaru biyar na taɓa yin rashin lafiya wai wasu kuraje suka fito min shine aka ce sai a Babban asibitin cikin Maiduguri za'a ban magani ," ta karasa zancen tana me ɗaga zanin ta zuwa gwaiwa ," kin ga taɓon kurajen nan yakaka wannan tabon da kike gani tun ina shekaru biyar a duniya,"

Waiwayawa su ka yi jin Falmata ta jaa ta tsaya lokaci guda suka dawo gefe da gefen ta suka tsaya ," yagana tana cewa kin gaji ne falmata ?
Falmata wani wurin yana miki ciwo ne cewar yakaka ?
Chapter 11 · 0% Book details