← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 124 OF 269

Sashe 124

Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba shi da masaniya akan tsawon lokacin da zasu iya yi a chan ,saboda harka ce ta neman lafiya , bai san yadda lamura zasu kasance ba , amma dai visa ta tsawon watanni shidda zai samar musu .

Ya ɗora da neman hajja ta masa bayanin duk wasu abubuwan da zata iya buƙata bayan kayan abinci da sauran abubuwan buƙata na rayuwar yau da kullum wanda zai iya kai ta watanni shidda ko fiye da haka ,

Da farko addu'o'in samun nasara akan abunda zasu nema tare da addu'ar nemawa mama samun waraka tayi ta jerowa , tana jin yadda tausayin su duk ukun ke kama ta ,

Babban soja , ni ba sai an min tanadin kome ba , saboda ka ga nima wajen shekaru biyu ake nema rabona da Æ´an uwa da dangi , dan haka idan har tafiyar ta tashi , bayan kun tafi a washegari nima zan É—au hanya zuwa nigeria nima naje na sada zuminci na ga Æ´an uwa da dangi , shekaru sun fara jaa , mutuwar nan ta yanzu kar ta gifta tsakani ba'a nemi gafarar Æ´an uwa ba , idan ya so bayan dawowar ku ko kuwa ma kafin ku dawo sai a sanar min nayi dawowa ta , ai ka ga nima na ribaci lokaci ko kuwa ?

Babu shakka hakane hajja , to babu kome idan har tafiya ta kama lokaci yayi sai ki tafi zouwa gida kafin dawowar mu , Allah ya saka da Alheri , ki min duk wasu bayanai na abubuwan da kike buƙata da zaki yiwa mutanen gida tsaraba don Allah .!

Toh madallah Babban soja , amma dayake nima a wajen nawa akwai Æ´an kuÉ—aÉ—e irin waÉ—anda kake min kyautar su ai ba ma sai na maka lissafin kayan tsaraba ba , idan tafiya ta zo ni da kaina zani nayo Æ´ar tsaraba ta ,
A ah hajja , don Allah kar ki ce hakka , irin Alherin da kika mouna a rayuwa ba zamou iya biyan ki ba sai dai Allah shi saka da Alheri , ƙwarai ƙwarai ina miki godiya , ki min lissafi abun da kike buƙata duk zan sa a kawo kome ranar da zaki tafi sai direban da ya kai ki wancen karon ya sake kai ki nagode !

Ni ce da godiya Babban soja ni ce da godiya , Allah dai ya ƙara buɗi , ya ba wa mama lafiya ,

Ameen ameen hajja ya amsa yana miƙewa ,

Sashin da suke ya mayar da duban sa , mama har tayi bacci fuskar nan a chakuÉ—e alamun fushi take ,

Bai yi mamaki ba saboda sanin ta da yayi da saurin bacci ,

A hankali ya taka zuwa gaban falmata wacce tayi shiru , tana É—an shafar kan mama da yake bisa cinyar ta ,

Fatima ni zan tafi bakin aiki zouwa le lundi zan dawo mu tai à muku passeport , ki kula da mama kar tayi wassa dayawa idan ta ji sauƙi sosai sai ta cigaba da zouwa école .

Toh Allah ya kiyaye hanya ,!

Ta amsa masa ,

Ɗan jim yayi a tsaye yana ƙure mata kallo da buɗaɗɗun idanun sa , hular ta shi ta karɓi yar zagayayyar fuskar ta me ɗan haske kaɗan , ji yake kamar ya bar mata hular a kan ta yayi ta kallon ta a haka ,

Jin yayi shiru kuma ta san da tsayuwar sa a wajen ya sa ta É—an dago kan ta , tana sake haÉ—e fuska ,

Gyaran murya yayi ganin yadda tayi kicin-kicin kamar zata fashe masa da kuka .

Fatima donne moi mon chapeau! ( miƙe min hula ta )
Ya furta hakan yana sake rage amon muryar sa ,

Falmata wacce tsayuwar sa akan ta da idanun sa da take ji suna mata yawo a jiki tamkar suna mintsinin ta ya sa ta diririce ta gaza fahimtar me yake cewa , ba wai dan bata jin yaren da yake yi ba ,

Mama bacci take .

ta ce da shi tana fatan ya bar kan ta

A hankali ya sunkuyo har tana iya jiyo hucin humfashin sa a fuskar ta  ya kai hannun sa guda ya zare hular sa dake kan ta , ya mayar kan sa .

Na tafi

Yace da ita yana juyawa ya bar wajen .

Wani irin yanayi ta ji a jikin ta uwa wacce aka zubawa ruwan sanyi , har ga Allah ta mance da hular sa da take kafe a kan ta ,

Runtse idanun ta tayi da ƙarfi tana jin yadda zuciyar ta ke bugu .

Hajja wacce duk abunda ya faru akan idanun ta tana iya hango su daga inda take .

auho ! aikin banza ihu bayan hari , da kike wani runtse ido kina wani kawar da kai ya ƙadangariyar gobara , ai wallahi ni dai na daina saki a hanya kan sha'anin auren ki , tsakani na da ke ido ,!

Ace wai tsawon shekaru fiye da biyar kin kasa zama cikakkiyar matar gida , ke kenan ɗaurewa miji fuska kina muzurai , zauna nan yarinya za'a yi bake lokacin da Babban soja ya gaji da halin ki ya sillo auren sa babu ni a masu yi miki dannar ƙirji , ko muƙamuƙi ba zan danna miki ba .

Cikin rashin kulawa da zantukan hajja wanda falmata ta riga ta saba da jin makamantan su , tace

Hajja ta me kika ce ?

Abunda wancan yace , shi nace

Ta amsa mata tana shirin miƙewa daga inda take tana cigaba da mita ,

Ƙatuwar mace kamar ki ace wai har yau tana da miji amma bata san amfanin sa ba sai rainon ƴa ,?

Ai ni ina kamar ki nayi aure na na biyu ma ,

Ki ka ce me hajja ta ban ji da kyau ba ??

Na ce gidan ku !

Ta amsa mata tana ƙarasa barin wajen

Murmushi falmata tayi domin ta san ta ƙular da hajja ,

Cikin ran ta tana juya maganganun hajja ,
Ban da abun hajja shi mutumin da kullum.take kumfar baki akan a kula da shi ɗin , shi ya taɓa nuna wata alama ne na kasancewar ta matar sa ? Tsawon shekarun auren su a tun bata san me takamaimai kalmar auratayya ke nufi ba ,

har ta zo ta san me ake nufi da aure ta hanyar malamar da take koyar da ita wacce a farkon fara ɗaukar darasi a wajen ta take yawan yi mata bayani akan auratayya a addinance da yadda mace zata kula da kan ta da mijin ta ta fuskar auratayya ba tare da kunyar kome ba cikin rashin sanin ta hajja ce ta yiwa malamar bayanin ƙarancin ilmi da wayon falmata ta kuma roƙi da ta dunga mata darasi na musamman akan auratayya ,

A hankali yau da gobe ta fahimci manene aure , matsayin miji a gun matar sa da matsayin mata a wajen mijin ta ,

Ta shiga ruÉ—ani na sosai da har kawo yau bata fita daga cikin sa ba , " yaushe yakaka da Baban mama suka yi aure ?? Ita ba ta san lokacin ba kawai jin yakaka tayi da cikin mama .

Akwai tsoro me tafe da son bada kariya tare da kyautata zato ga ƴar uwar ta yakaka , haɗi da son tsaftace mama shi yasa a duk lokacin da tunanin hanyar da aka bi aka samar da mama ya taso mata , take yaƙar tunanin da ƙarfi da yaji , bata son wani abu da zai aibata yakaka ya raɓi tunanin ta ,

Kewa tare da ƙaunar ƴar uwar ta bai ragu ba ko kaɗan a cikin ran ta sai ma zurfafa da yake sake yi yayi mata ƙaton miƙi a cikin rai .

Rashin son suyi zaman auratayya irin na sauran ma'aurata da Biyamuradi ya nuna tsawon shekarun bai taɓa damun ta ba ,

Hasalima ta fi son hakan .

Zaman mama take , tana rayuwa ne a ƙarƙashin sa kaɗai domin mama , za kuma ta cigaba da tsayawa ɗauke da auren sa a kan ta har abada muddin tana tare da mama .

****

Daga niamey kai tsaye maraɗi ya wuce , bayan isar shi faɗa ya kai gaisuwa , kai tsaye ɓangaren sa ya nufa ba tare da ya shiga cikin gidan su wajen hajiya umma ba , yasan yanzu tana tare da jama'a masu neman taimako da ƴan barandar ta , sai zuwa yammaci zai shiga wajen ta zuwa lokacin ƙafa ta ragu a sashin nata ..

Tattaki yayi zuwa sashin sa da yake bigire guda na gidan , bayun da suke kai kawo a fada su na ta kai gaisuwa bayan waɗanda ke take masa baya tun daga ƙofar fada .

A bakin sashin sa suka jaa tunga saboda a tsarin sa bayi maza basa shiga ɓangaren gidan sa da matan sa ke ciki .

Yana sanya ƙafar sa a cikin gidan ya ji wani yanayi marar daɗi na lullubar sa , hakan kuwa yana da nasaba da rashin daɗin zama a gidan da yake ji har kullum ya kuma rasa dalili .

Taku ya fara yi da nufin isa sashin gimbiyar ta shi maimouna .

Sai dai ƴan hannuwan da ya ji sun riƙe masa ƙafafun sa su suka sanya shi ya maida ganin sa ƙasa ,!

Yumna

Ya furta yana ƴar dariya tare da kai hannu ya ɗauki ƴar yarinyar da take ta yi masa dariya , ya ɗaga ta sama ya cilla ta tana ɓangala masa dariya .

Rungume ta yayi a jikin sa lokacin da yake maida duban sa kan mamar ta wacce take ƙarasowa wajen fuskar ta ɗauke da murmushi , a shirye take tsaf , ba wata shahararriyar kwalliyar fuska tayi ba illa jikin ta da yake kiruf a rufe da babban mayafi tun daga wuyan ta da ya sha ado da tufafi irin na alfarma ,wanda ya amshi zubi da tsarin jikin ta na samɓaleliyar mace me zubin matan fulanin usul .

Janye idanun ta tayi daga cikin nasa kamar koyaushe da bata iya jurar ganin cikin idanun sa duk kuwa da tsawon shekarun da suka shafe a matsayin ma'aurata ,

Barka da zouwa Baban Yumna , da fatan ka isso lafiya ?
Chapter 124 · 0% Book details