Sashe 36
Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin sanyin jiki ta kama hanya bayan ta biya ta sanarwa yakaka wacce take ta faman gurzar wanki ta gefen É—akunan su duk da duhun dare da ya riga ya shigo domin har an idar da sallar magariba ina shirye-shiryen yin isha'i amma su koh sallar magaribar ma basu samu damar yi ba kamar yadda a yawancin lokuta haka take faruwa sai dai su haÉ—a magariba da isha'i suyi tare , abincin dare kuwa ba kullum.suke samun damar ci ba saboda ana idar da magariba ake zubo shi a daka wawaso kamar yadda aka saba , su kuwa a mafi yawancin lokuta basu kammala aiyukan bautar da ake basu ba ,"dan haka zuwa yanzu sai rana É—aiÉ—aiku suke cin abincin sansanin kuma basu wani damu sosai ba sakamakon suna da Æ´an kuÉ—aÉ—en su a kulle ," kou yagana da take take da damar cin abincin ma bata cika shiga cikin turmutsutsun ayi kokawar É—ibar loma da ita ba , a cewar ta daman dole ne ta sa take cin wannan cinkusasshen abincin marar daÉ—in É—anÉ—ano ,"
Tafe take tana juya jikin ta a hankali kamar yadda yake halittar jikin ta , duk da ƙarancin shekarun ta da yanzu ne ta fara fidda alamun budurci ," amma haka halittar ta take irin matayen da suke da maɗaukakin kyaun diri da ɗan madaidaicin tsawo ," tafiya take cikin nutsuwa baza a taɓa zaton makauniya bace ," saboda yadda take tafe babu ɗan jagora kuma babu sanda sai dai lokaci-zuwa-lokaci ta kan ɗan lalubi hanyar wanda hakan yake babbar baiwar da Allah ya yi mata , tana daga cikin makafin da Allah ya basu ikon gani da zuci , wanda kai tsaye baza'a kira hakan da gani ba domin ba ganin suke ba sai dai wata irin baiwa ce da ɗaukakar ubangiji da ya yi musu daga kwakwalwa zuwa zuciyar su ,"
Ta tsakanin dattin ganyen bishiyar ta ratso har ta bullo a gaban tantunan da suke duk a rurrufe saboda ɗan sanyi sanyin damina uwa uba tsoron kar muggan ƙwarin damina su buwaye su , "
Tsayuwa tayi a dai-dai bakin tantin da take hasashen nasu saurayin ajus É—in ne tare da yin sallama cikin maÉ—aukakiyar murya ta kwala kiran sunan sa kamar yadda ta saba ,"
Daga ciki ya jiyo tare da shaida muryar ta nan take ya fito , nan ta isar masa da sakon ajus É—in da take tambayar neman sanin kou yau zasu haÉ—u su zanta ? Inda shi kuma ya faÉ—awa falmata ta sanar da ita shi yau bai jin daÉ—i .
Tana kammala jin amsar sa ta juya tare da nufar hanyar komawa , signal saurayin ajus yayi wa wani saurayi ɗan uwan sa da yake tsaƴe a gefe wanda kuma tare suka fito daga tantin ," shafa shukurkuɗaɗɗan daddauɗan gemunsa daya saurayin yayi lokaci guda suka yunƙura tare da rufawa falmata wacce ta ɗan fara nisa daga da'irar su ,"
Ta cikin takun su da yake sauka akan busassun ganyayyakin ta fahimci akwai mutane fiye da É—aya a bayan ta wanda bata kawo hakan a zuwan wani abu ba cikin ranta ,"
Cigaba tayi da tafiyar ta , sai dai kome ya tsaya mata ne lokacin da taji anyi sama da ita an ɗaga ta cak lokaci guda ana me sanya hannu a toshe mata bakin ta , kafin taji an zura da gudu da ita zuwa wani bigire da bata san ina bane duk kuwa da wuntsil-wuntsil da ƙoƙarin sauka da take daga kafaɗun wanda ya ɗaga ta da bata kai ga nasarar saukar ba ,," sauke ta aka yi akan wani abu da tashin hankalin bai bari ta fahimci menene ba , kafin kuma tayi aune taji an fara ƙoƙarin raba ta da suturar ta alhalin bakin ta yana danne cikin hannunwan wani daban , an hana ta damar ihu , wani irin bugawa zuciyar tayi tamkar zata fashe lokacin da ta fahimci mummunan nufin da suke son aiwatarwa a gare ta ,"
Bugawar zuciyar ta ya zo dai-dai da na yakaka da tata zuciyar ta fara sauya salon aikinta tun daga barin falmatan gaban ta zuwa yanzu da zuciyar tayi mummunan bugawa, " zuruf ta miƙe tare da zare hannun ta daga ruwan wankin ta kai hannayen nata duk biyu ta dafe kirjin ta ,"......!
#Fikrh
#umm'muaz
#son so
[6/24, 10:57 AM] +234 701 013 7848: Fikrah writers association
MAFARI ........
( Hargitsin Rayuwa....)
Umm'muaz
15
Dafe da kirjin ta da yake cigaba da bugu ta nufi hanyar da zata sada ta da ɗakunan kwanan mazan sansanin su , domin haka kawai ta ji hankalin ta bai kwanta ba da rashin ganin ɓullowar falmata har yanzu dan haka ta tafi domin ta taro ta su dawo tare,'
Sai dai har ta cimma ɗakunan bata ga falmatan ba , sai tsirarun mutane da suke giftawa ta cikin duhuwar ," turus ta jaa ta tsaya saƙe-saƙe ta fara yi a zuci ,"
  Toh ina falmata tayi ?
  Koh dai ta koma ɗakin su ne wurin ajus ?
Ganin bata ga koh alamar ta ba kuma ga shi babu wadatar kafafun mutane a wurin bare ta cigita , ga kuma duhun dare da take tsorace da shi , sai ta juyo gami da kamo hanyar komawa da nufin zuwa ta duba É—akin su falmata ,
A sanyaye take taku saboda har yanzu zuciyar ta bata bar tsinkewa ba sai ma ƙara dukan uku uku da take yi ,"
Bata yi nisa ba ta tsinkayo wani rishi da alamun fitowar kukan da aka ƙi bada dama ya fito ,' kiƙam ta jaa ta tsaya tare da sake kasa kunne lokacin da ta sake jin irin rishin ," a firgice ta juya laɓɓan bakin ta suna furta sunan ,"Falmata"
Tayi diri-diri cikin rarraba idanun ta a kewayen wurin ,tana neman inda zata gan ta domin tabbas kunnuwan ta muryar falmata suka jiye mata ,"
Cikin rashin sanin gaba zata yi ko baya ta taka da gudu tare da hawa kan barandar wasu tsoffin ajizuwan da suke gefe da ita waÉ—anda kou rufi babu a kan su ta wasu wuraren ma sun fara zaftarewa da alamun sun zama kango ,"
Da gudu take shiga cikin ajizuwan tare da kwala kiran sunan falmata , sai dai bata tarar da kome cikin ajizuwan sai tarin bola tare da yanar gizo-gizo da tayi dafifi a ciki , cikin tashin hankali ta jaa ta tsaya daga karshen barandar da take daf da katangar makarantar , daddagewa tayi ta sake ƙwala kiran sunan falmatan , sai dai bata kai ga rufe bakin ta ba taji an ɗauke ta da wani kakkarfan mari , kafin ta farga taji an shatile kafufuwan ta , ta tafi ta baya ta faɗi ƙasa tare da bige ƙeyar ta da katangar makaranta ,
zuruf ta miƙe bata koh ji alamun zafi ba lokacin da tashi sautin muryar falmata ya fito tar cikin wani irin kukan wahala tana ambaton sunan ta a kurkusa da ita ,"
Taku biyu ta ƙara ta ci karo da ita a kwance cikin tarin busassun ganyayyakin da ake sharewa a tara a wurin ya zamto tamkar bolar zuba ganye ,"
ÆŠago ta tayi ta tarairayo ta tare da rungumo ta zuwa cikin jikin ta tana yi tana waige-waigen jin ta inda waÉ—an da suka bige ta zasu bullo wanda take da tabbacin sune suke shirin cutar mata da falmata cikin ran ta tana jin karfin yin É—auki ba daÉ—i da ko su waye domin ta tseratar da falmata ,"
Tunanin ta ya tsaya chak ! Lokacin da ta ji gaba É—aya kukan da falmatan take yi ya gauraye da wani irin numfashi tamkar na me shiÉ—ewa , jijjigata ta fara yi tare da kokarin tayar da ita tsaye ,tana cewa
    "sannu falmata me suka yi miki ? Duka ? Kin ji ciwo ne falmata tashi muje ki shaa ruwa ,"
Rinjayar ta falmatan tayi a domin ta gaza tsayuwa sakamakon numfashin ta da yake sarƙewa , su duka biyu suka zube ragwaf a ƙasa kafin falmata tayi baya lau ta tafi zata kwanta cikin sauri yakaka ta riƙo ta kwakwalwar ta na son fahimtar me ke shirin faruwa da ƙanwar ta ?
Jijjigata ta fara yi cikin zubar hawayen da suka balle sakamakon tashin hankalin ganin falmatan a kwance bata motsi sai wani irin shiƙar numfashi take ,"
 Cicciɓar falmatan take son yi amma ta kasa saboda tayi mata girma da nawi baza ta iya ba , kwantar da ita tayi ta taka da nufin zuwa ta kira mutane su taimaka mata , har ta yi taku biyu a gigice ta sake juyowa , zuciyar ta na bijiro mata da hoton gawar mahaifinta da ta bari a wuri makamancin wannan cikin "gona babu kowa ,"
Da gudu ta taho gami da sake durƙusawa tare da ɗago falmatan da dukkanin karfin ta , ta rungumo ta a kirjin ta , ta yunkura da kyar ta miƙe gami da ciccibar falmata da jikin ta yake a sake bata motsi , kiki-kiki ta fara kokarin jaan ta ta tafi da ita , sai dai kou taku uku mai kyau bata yi tayi tuntube da wani ɗan kankanin dutse ta baya kafar ta ta zame takalmin ta ya tsinke , suka tafi baki ɗaya suka faɗi ta baya kan falmatan ya bigi haɓar ta nan take hakoranta suka datse laɓɓan ta na ƙasa ya fashe ,"
Da hanzari ta sake sunkuyowa kan falmata hawayen ta na ɗiga akan fuskar falmatan ta ɗago ta ta fara jaan ta cikin sautin kuka ta fara ƙwalla kiran naiman taimako , domin zuwa yanzu ta fahimci mutanen da suka jefa ƙanwar ta cikin wannan mummunan yanayin da zuciyar ta taki aminta da falmatan ta mutu kamar yadda ta ga alamu , mutanen sun gudu basa wajen ,"
Da faÉ—uwa da tashi ta fiddo ta tsakiyar hanyar da ake wucewa , sunkuyowa tayi tare da tallafo kan falmata tana cigaba da girgiza fuskar ta ,"
   Meƴe ya same ki falmata ?
  Falmata ki tashi dan Allah
  Ki tashi falmata ? Ki tashi