← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 269

Sashe 65

Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Toh madam falmata
ta furta hakan tana murmushi jin yadda falmata ta zage tana bata umarni kamar dai ita ce babba .

Hanya ta miƙe tana tafe tana raba ido cikin fatan son ganin inda zata ɗan samu wani aiki ta je ta kama ko da ba'a sa ta ba , amma har ta kai kan gadar kasuwar bata ci karo da wani wajen da ake buƙatar ƴan aiki ba , hasalima yanzu ne ƴan kasuwar suke kan buɗe shagunan su , tare da fito da kayayyakin sana'o'in su ,"

Har ta yanke shawarar komawa wurin falmata ta ɗan jira zuwa anjima , sai idanun suka hango mata mattatarar masu niƙa a ƙwarin gadar ,

Sai ta yanke shawarar ta ƙarasa wurin ƙila ta samu aikin yi tun da ta hango wajen a cike ,"

Gangarawa tayi ta sauka wajen , ga mamakin ta masu injinan niƙa ne birjik ta ko'ina a wajen , ƙarar inji kuwa ba'a cewa kome domin ko maganar na kusa da kai baka iya ji sai fa idan yayi ihu ,'

Da gudu ta ga wasu Æ´an matasan yara maza da baza su gaza falmata ba sun nufo ta ,"

   Yaya ta niƙa ne ? Ki kawo na kai miki injin mu yau yau muka kai faifan injin washi , laushi luƙui za'a miki ,

Yaya ta injin su mutuwa yake ana cikin niƙa , anjin mu yafi lafiya kuma ga arhar niƙa ,"

Ita dai da ido take bin su da kallo ba sosai take fahimtar su ba , saboda ƙarar injin da ya cika mata kunne ,

Ita ma da É—an karfi ta amsa musu
   Ba niƙa na kawo ba , aiki nake nema ,
   Haɗa ido yaran suka yi suka kwashe da dariya , suka maimaita
   Wai aiki take nema ?  kut wannan ƴar na'u ce ita ma .

  Juyawa suka yi suka bar ta nan tsaye ba tare da sun bata ansa ba .

Har sun É—an yi nisa sai kuma É—ayan ya komo ,
aikin tankaÉ—e dusa kike nema ??
    Batare da ta kai ga fahimtar sa ba ta gyaɗa kai ,
    Zo muje injin abokin yayana jiya sun ɓata da mai yin tankaɗen dusar sa ,
    Da murna yakaka ta bisa a baya har wata ƴar siririyar hanya , bayan ƴar gajerar tafiya suka bullo a wani babban fili faffaɗa , saɓanin injinan da ta tarar a waje waɗannan manyan injina ne girkakku , ƙaran su mai matuƙar karfin gar diri yake a cikin ƙasa ,"

Gaba yaron yayi zuwa wurin wani da yake tsaye a gefen É—aya daga cikin injinan yana juye hatsi a cikin injin bayan ya gwamtsa shi da ruwa .

A kunne yayi masa maganar yana mai nuna yakaka da É—an yatsan sa ,"

Bayan sun gama magana ya dawo wurin yakaka ,' 
    Yace wai shi ba zai biya ki ko sisi ba dusar da zaki tara ita ce ladan aikin ki ," kin yadda ?

   Cikin sanyin jiki yakaka ta gyaɗa kan ta , "bata da zaɓi ! Amma cikin ranta tana tababar ta yaya dusa zata zama ladan aikin ta me zata yi da dusa toh ? Ko suna nufin ta ci ??

   Bayan yaron ya faɗa masa amincewar yakaka , da kan sa ya taso ya zo inda take ,
     Keh yane ƴar na'u ? Kin gane ne aikin yana da yawa dan haka zaki samu alheri , ina ga nima har sai kin ware min wani abu a ciki , ya ƙarasa zancen yana kwashewa da wata hautsinannan dariya ,
     Biyo ni na nuna miki aikin ,
Cikin wata babbar rumfa ya kai ta , wacce take cike da mata tsoffafi da ƴan mata irin ta da ma waɗanda suka fita , wasun su a tsaye suke suna faman zirta hatsi , masara , dawa , alkama , a manyan-manyan turamen da suke watse a cikin rumfar , wasu kuma suna zaune a ƙasa suna ta faman bushe abun da suka zirtan , suna tara dusar a buhun gefen su ,"

Wani babban buhun masara da na hatsi ya nuna mata ,"
  Ƴar na'u wannan ne aikin ki yau ake so , kiyi aiki mai kyau dan gaba a neme ki , kuma banda waskiya ai kin gane ?  idan masu shi suka kama ki kin waske musu abun su , suka ciya miki ni babu ruwa na ai kin gane ko ?

  Na gane

Toh ki zo mu je na baki aron faranti dan naga baki da shi , kuma waÉ—annan Æ´an ciki baki baya kwalta ne , ba baki aro zasu yi ba !

Zungui zungui ta bishi a baya ,'

Daka da surfe ba sabon abu bane wurin yakaka , toh bare wannan da zirtawa ne ba surfawa ba , manyan injinan su ke yin surfe ," nan take ta kama wani turmi da ta ga babu kowa akan sa , ta ɗauki wata ɓasgararriyar taɓaryar da take jefe a gefe ta kama aikin ta babu tsayawa hira , to ma wa ta sani a wurin da har zasu yi hira?? Babu !

Kafin la'asar yakaka ta zirce hatsin da masarar tas , ta hau bushe dusar har da gyarawa , la'asar lis ta gama ta tara dusar daban-daban fiye da rabin buhu kowannen su , iyakar gajiya ta gaji , ga yunwa ga kishirwa , nan gefen ɗan buhun ta samu ta zauna tana mayar da numfashi ,  dayawa daga matan sun gama aiyukan su suna zaman hutawa ,'

Ba'a jima ba masu kayan suka zo ɗauka ƙarƙashin jagorancin "ubangidan ta "mai surfen , nan suka duba kayan su ," yakaka ta jawo buhun dusar ta nuna musu ,

  Ɗan saurayin da ya zo ɗaukar kayan ya ciro naira ɗari biyu ya miƙa mata ya ce ta haɗa da dusar ta riƙe kamar yadda suka saba ,

Da murnar ta ta sanya hannu biyu ta ƙarbi kuɗin , cikin ran ta tana tambayar kan ta toh ita kuma me zata yi da dusa ? Ina zata kai ta ?

Tunanin ta ya katse lokacin da ta ga wasu dattawan maza da mata sun fara shigowa , da gudu ta ga kowacce mace tana surar buhun dusar ta tana kaiwa gaban su ," wannan tace tata ta masara ce , wannan ta ce ta hatsi , wannan ta dawa , alkama , su kuma suna tambayar kwano nawa ne ?? ko kuma daro nawa ?? Sai ta ga an fara cinikin dusar , ita dai tana tsaye tana bin su da ido cikin son fahimtar abun da suke ,

Kafin kace meye wannan tas mutanen sun gama saye dusar nan har sun fara lodawa a wulbaro ana jide musu , fahimtar da tayi masu sayan dusar ne , ya sa ta janyo nata buhun-hunan ta kawo gaban su ,"

Cikin tsanaki ɗan dattijon yake kallon ta duk alamun gajiya da yunwa sun bayyana a gare ta fatar bakin ta har ta bushe , jikin nan busu-busu da ƙurar dusa ,"

  Kwano nawa ne ƴan mata ?
Nima ban sani baba

Ungo wannan daron hashimu juye ka auna dusar yarinyar nan kwano nawa ne ,"

Tana tsaye aka auna kwano biyar biyar ne , ta masarar da ta geron ,

KuÉ—in ki naira É—ari huÉ—u ne Æ´an mata kowanne kwano murtala biyu muke sayan sa idan dusa mai nawi ce irin taki , idan kuwa faya-faya ce naira ishirin da biyar ne kowanne kwano ,

Ɗari biyar ya miƙa mata tare da buhun ta ,'
    Bari na nemo chanji baba ta furta hakan tana jin wani zallar farin ciki kamar tayi tsalle ,"

Ki bar chanji yarinya ki sayi abinci da ruwa ki sha , ki daina zama da yunwa a wannan halin da kike ciki babu kyau , Allah yaye mana talaucin da ya addabi ƙasar mu !

Har ƙasa yakaka ta sunkuya tana jero kalaman godiya kamar zata kwanta ,"

Sauri sauri ta wanke jikin ta tare da ɗaura alwala da ruwan randunan ƙasa da ta gani birjik a filin wajen , ta lura har babban bayan gida ne a wajen wanda ake shiga a yi wanka da kama ruwa bayan an gama aiki ,

Gudu-gudu tayi sallolin ta na azahar da la'asar , ta ninƙe buhun ta ta cusa shi a ɗan wani lungu , ta fito tana kallon rana yadda ta tafi tana gaf da faɗuwa , hankalin ta baki ɗaya yayi kan falmata ,

A haka ta kama hanyar kasuwar busu-busu da ita sai cin karo take da mutane waÉ—anda su ma suke cikin sauri domin su bar bakin kasuwar ,

A zaune ta tarad da falmata inda ta ajiye ta tayi shiru da ita ta sunkui da kai , mafi yawancin mutanen da suke hada-hadar su a wurin duk sun watse hatta baba mai kayan miya baya nan,"

Cikin sauri ta dafa falmata ,"
   Falmata na dawo ,
Yakaka kin dawo sannu da zuwa , baki gaji sosai ba koh ? Baki yi aikin wahala ba ko ? Kin ci abinci ? Ya jikin naki ?

    Ƴar dariyar ƴake tayi , tana mai jin yadda jiri ke kwasar ta , ƙarfin hali kawai take wurin tsayuwa akan kafafun ta ,

  Falmata tashi mu ƙarasa rumfar da zamu kwana kin san fa mutumin nan cewa yayi kar mu wuce karfe huɗu da rabi , yanzu kuma ina ga kamar biyar ma ta ɗan wuce kin ga kar ya fasa taimakon mu da yace zai yi mu dunga kwana a bakin shagon sa ,:

A tSaye suka tadda shi a gaban rumfar shagon sa sai faman duba agogon hannun sa yake ," ba dan yadda yake jin tausayin yaran ba da tuni yayi tafiyar sa domin a ka'idar sa baya wuce karfe huɗu da rabi a kasuwa , sai ga shi yau har biyar da wajen minti ishirin , cikin ran sa ya aiyana ya ƙara musu mintoci goma idan basu zo ba zai yi tafiyar sa .
Chapter 65 · 0% Book details