← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 269

Sashe 53

Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Karaf suka haɗa ido da yagana wacce wannan ne zuwan ta na uku ɗakin samy baby neman yakaka wacce aka tabbatar mata da bata kwana a gida ba kuma babu wanda ya san inda take wanda hakan ya tashi hankalin yagana tare da falmata wacce tun da ta farka ta laluba gidan taji babu yakaka take ta surfa kuka babu ƙaƙƙautawa ,"

Kai kawo suke ta yi daga waje zuwa harabar gidan da kewayen sa É—aki-É—aki neman yakaka , wayam babu ita babu wanda ya ce ya gan ta ma sai mutum É—aya ne babasho yace tabbas ya ga fitar yakaka tare da wani mutum a daren jiya ,

Da sauri yagana ta ƙaraso

Yakaka ina kika je ? Daga ina kike ? Aina kika kwana ?? Sune tambayoyin da ta jero mata ,"

Na raka samy baby gidan su ne ! Ina falmata ? Mu ƙarasa ciki ,"

Tare da shakku yagana ta tsare yakaka da ido , domin sarai ta ga kuɗin da yakaka ta boye mata , uwa uba wani fitinannen ƙamshi da take ji yana tasowa daga jikin yakakar

Amma ganin yakakar taƙi nuna mata da kan ta sai ita ma ta bar batun .

Ki taho muje falmata taji muryar ki ko ta daina kukan da take ta faman yi tun farar safiya ,"

Bata ƙarasa rufe baki ba yakaka ta taka da gudu ta nufi cikin gidan ,

Zaune ta tadda falmatan ta haÉ—a kai da guiwa a inda ta saba aiki bakin fanfo ga tulin wanke-wanken kofuna da faranten sana'ar su a gaban ta ,"gefe guda kuma kwanan da ta saba sayo musu waina Æ´ar tsala da suke karin safe da ita ne , a rufe ga alama ko sayo wainar bata yi ba , "ta gaza yin aikin sai kuka ,"

Da sauri ta É—ago ta tare da rungume ta cikin jikin ta ,'falmata ki bar kuka gani nan na dawo ,"

Yakaka ina kika je kika kwana ? Meyasa baki faÉ—a min ba ? Kin sa hankali na ya tashi , yakaka ya zan yi a wurin da bakya nan ? Dan Allah duk inda zaki tafi kike tafiya da ni kin ji ?

Naji falmata kuma bazan sake tafiya na bar ki ba ," ta furta hakan tana mai bubbuga bayan ta sigar lallashi ,"

Yakaka ƙamshin meye ne haka a jikin ki ? Aina kika samu ƙamshi ko a gidan turare kika kwana ?

Eh__Ah ah
  Unm falmata muyi wanke-wanken kafin rana tayi sosai kin ga mun yi jinkirin fara aiki ,

  Toh ai duk ke kika jawo mana !
Madam saly ma ta zo tayi ta masifa tace wai kin fara yawo ,'

Tsam yakaka tayi da jin cewar madam saly tayi masifa ," a duniya tana tsoron madam saly , tana matuƙar gujewa bacin ran ta gani take ita ce gatan su ,"

Kafin rana ta take sun kammala aikin su da suka saba yi har sun fara hidimar abokan cinikayyar su kamar yadda suke a kullum ,"da hakan ya kwaci yakaka daga shan masifar madam saly , dan ita faÉ—an ta akan harkar ta ne ba wai dan rashin kwanan yakakar a gida ba ! Yo me ya shalle ta ?
Babu wanda ya bi ta kan yakaka akan rashin kwanan ta a gida yo bariki ce fa ! ?

Yagana ce ma ta so matsawa ta ji toh amma ganin yakakar taƙi bada haɗin kai ta gaya mata inda ta kwanan sai ita ma ta haƙura , har lokacin rabuwar su yayi suka kammala aikin su na yinin ranar ,

Yakakar ta rako yagana bakin titi kamar yadda suka saba kullum idan yaganar zata koma sansanin su ,"

Kuɗin da suke dunƙule a hannun ta ta kamo hannun yaganar ta danƙa mata su ,"

Ga shi yagana ki sayi wani abu nima bani aka yi ,"

Da sauri yaganar ta ce wa ya baki ? lokacin da take warware ƴan naira dubu guda biyu da yakakar ta miƙa mata su a dunƙule,

Wanda na taimakawa ne ya bani !

Taimako ? Wane irin taimako waye shi ?

Yagana yanzu ba lokacin hira bane kin ga an kusa rufe hanya kiyi sauri ki tafi sai da safe !

A sanyaye yagana tace
  Toh nagode !
   Sai gobe ," ta kaɗa kai tayi tafiyar ta zuciyar ta na shakkun ina yakaka ta samu kuɗi haka masu yawa ? Koma menene ita dai tayi farin ciki da kudin da yakaka ta bata koh banza ta toshe wasu daga cikin tarin matsalolin da suke kewaye da ita na talauci !

Akan hanyar komawar ta gida yakaka take tuhumar kan ta meye yasa ta boyewa kowa abun da ya gudana tsakanin ta da mutumin da ta taimaka  ? Oho ita da kan ta bata san dalili ba  , abun da ta gane kawai shine tana jin kunyar bada labarin yadda suka kasance tare ,"

Dai-dai ta shawo kwanar layin su ƙamshin balangu Barde mai nama ya daki hancin ta ,  tun ba yau ba tasha haɗiyar mugun yawu akan ƙamshin balangun da kullum take wuce wajen da tunanin ina ma ina ma Allah zai kawo wani tsautsayin da zai gifta ya sa tukubar balangu barde ta tuntsira ita kuwa ta daka wawaso ,! Saboda ba ƙaramin ran ta biyawa yayi da balangun nan ba ,! Rabon ta da nama shekarun da ƴan yawa ,' to su da suke ta abinda zasu ci su kori yunwa ina su ina nama ,"kayan wadata "

Yau da take jin ƙugun ta danƙam da kuɗi , tana shaƙar ƙamshin ta saki hannu ta bishi , har cikin ƴar rumfar barde ,

Cikin nutsuwa ta gaida barde
Ya amsa mata haba-haba irin na Æ´an kasuwa ,"

Ta miƙa masa gudar ɗari biyar ɗin da ta ciro daga ƙugunta ,

Na nawa za'a yanka miki Ƴan mata ,?"

Na dukka ! yakaka ta furta hakan tana mai gyara tsayuwa jin kan take a sama ," naman É—ari biyar ai ba kusa ba ,"

Take barde ya washe baki ya fara yanko naman daga gefe-gefe yana kachal-chala shi akan Æ´ar takarda neÉ—e nama ,'

Da sauri yakaka tace a ah ba nan zaka yanka min ba nan nake so wuri mai nama-nama da mai ɗin ," ta nuno wurin da yafi ko'ina sheƙi a jikin naman yana ta nason mai da yaji ,"

Au to toh bari a yanko miki nan ɗin,"( kuturu da kuɗin sa ai alkaki sai na ƙasan langa )

Ƙarbar balangun tayi bayan ya naɗe mata yaji a wata ƴar takadda daban ya haɗa ya sa mata cikin leda ,"

A ci daÉ—i lafiya Æ´an mata !

Tun a harabar gidan ta fara ƙwallawa falmata kira wacce take zaune daga gefe a babban filin , inda ɗan asharalle ya baje gangunan sa da shi da yaran sa suna ta bugun ganguna ," kalmomi ne na batsa ake rera waƙar da su , mata Sun shiga layi kowacce tana nuna ƙwarewar ta a fannin girgiza kwankwaso tare da juya sassan jiki ,' mazan da suke zagaye da su suna kallon su tare da yin eho har wasu suna faɗawa filin su yi wa budurwar su ko wacce ta birge su liƙi ," 

Ta ko'ina jama'a ne birjik a harabar masu cha-cha da karta nayi masu hira  musun ball suna fama ,!

Kamo hannun falmata tayi suka shiga daga ciki sashin madam saly inda babu yawaitar mutane sosai saboda mafi yawa suna filin chasu ,"

A gefe ta zaunar da falmata kan wani ɗan dutse , ita ma ta zauna gami da warware ƙunshin naman ta ɗauko ƙatuwar tsoka bayan ta ɗan ɗangwalo yaji ta nufi bakin falmata da shi , wacce tun da aka buɗe naman ƙamshin sa ya buge ta yawun ta ya tsinke ,"

Ungo falmata buÉ—e bakin ki kici nama ,"

Unm unm yakaka waye ya baki wannan naman mai daɗin tsiya  ?, cewar falmata a lokacin da take ƙoƙarin haɗiye na bakin ta ,!

Ni na sayo mana falmata ,

Yakaka ta furta hakan tana mai sake nufar bakin falmatan da wani yankan

Chak falmata ta tsaya da taunar wanda yake bakin ta .

Aina kika samu kuÉ—i yakaka ?

Wanda na taimakawa jiya ne ya bani !

Waye shi , ?

Wani ne baki san shi ba falmata nima kuma ban san shi ba , taimakon sa kawai nayi ya tafi kuma yace ba zai sake dawowa ba , ta furta hakan tana jin wani yanayi marar daɗi yana taso mata kalaman sa na ƙarshe suna mata amsa kuwwa cikin kunnen ta ," Bana son na sake ganin fuskar ki ,"
       Kenan ba zai dawo ba ,
     zuciyar ta ta aiyana haka!

Kai amma yana da kirki ! Cewar falmata lokacin da zaƙin naman yake ratsa ta ,"

   yakaka bata samu zarafin amsa mata ba saboda zuciyar ta da tayi ƙunci ," a take ta ji ta daina jin garɗin naman dan haka ta miƙe gami da cewa falmata tana zuwa ," ta ci naman iya cin ta .

Shagon sayar da kayan masarufi da amfanin yau da kullum ta tafi wanda bashi da nisa sosai da gidan su ,

Ta miƙa dubu ɗaya tace a bata manyan jakar bacco guda biyu , da sabulun wanki guda uku da na wanka sinki ɗaya da kuma omo babbar jaka ,"

É—an jim tayi tana tunanin bayan su kuma me yakamata ta saya ?
  
Har zata ƙarbi sauran chanjin ta idanun ta suka sauka akan jerin ƴan mukullaye da suke jikin wani ɗan karfe ," wani tunani ne ya faɗo mata

A bani ƴan mukulli ƙanana guda biyu ,"

Ta haÉ—o sayayyar ta ta komo gida kai tsaye ta wuce É—akin da su falmata ke kwana , ta jawo yagaggen jakar bacco wanda suke tara kayan su a ciki ita da falmata ,

Ta fiddo dukkanin suturun su ,"babu laifi yanzu suna da Æ´an kaya ,"

Ta warware sabbin bacco , ta ware kayan falmata ta jera mata su tsaf a ciki bayan ta gyara ninkin ta ɗauki ɗaya daga cikin ƴan mukullin ta kama bakin zif ɗin ta sarƙafa shi ta bame ,"
Chapter 53 · 0% Book details