Sashe 6
Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Amma ban yi zaton karyar taki da yauɗarar ki ta kai har haka ba , da har domin rashin hankali zaki yi irin wannan ƙasurgumar karyar da yaudarar a gidan sarauta, toh Maza sai ki tanadi ruwan wanke kan ki a idanun mai martaba da shi kan sa mijin naki , ki kuma tabbatar kin riga kin gama zubda ƙimar ki a idanun mutanen gidan nan ciki kuwa har da bayun da suke karkashin ki , haba saratu me ake da wannan irin karyar taki "
Saratu dai babu bakin magana sai sharar ƙwalla take "wanda hakan ya jaa hankalin malaman jinyar da suke gyara ta har ta kai su ga tambayar dalilin kukan ta "hajiya uwa" ta faɗe musu biri har wutsiya akan yaudarar da saratu tayi mata da kunyar da ta jefe ta " Malaman jinyar su da kan su sun ga rashin kyautawa, tare da mamaki irin karyar saratu sai dai sun bada tabbacin akwai irin na'urar a kasashen da suka cigaba ,"sai dai koh na'urar ma ba koyaushe take bada bayanin gaskiya ba"( Sanin gaibu sai Allah ) jin hakan ya sa "Hajiya uwa jin wani farin ciki ko ba kome sun samu hanyar da zasu fidda , kan su "
Haka aka gama gyara ta tare da jariryar aka tura su É—akin da zasu zauna "a lokacin ba'a sallamar mace daga haihuwar ta har sai ta zauna a asibiti kwanaki biyu zuwa uku domin tabbatar da karfin jikin ta "
Bayan isar su É—akin hutun kafin jama'ah su zo "Hajiya uwa ta sanar da Saratu shawarar da ta gama yankewa domin samun rufin asirin su ,nan take yanke "ba tare da jaa ba" Saratu ta amince .
Da zuwan yarima Abdoul-azizu "hajiya uwa ta sanar masa da É—iya mace aka haifa ba É—a namiji ba ta kuma É—ora da bayanin da malaman jinyan nan suka yi musu na cewa ana iya samun kuskuren inji wurin bayyanuwar jinsin abun da ke cikin mahaifiyar sa "
Ƙwarai yarima abdoul azizu yayi kokari wurin nuna rashin damuwar sa akan kuskuren na'urar da ya riga ya yadda akan cewa an samu " Amma cikin ran sa sam sam lamarin bai mar daɗi ba sun riga sun ƙwaɗaitar dashi son haihuwar ɗa namijin .
Bayan isar labarin haihuwar saratu "Fada " tare da sabon sauyin da aka samu daga haihuwar É—a namiji da ake sa ran haihuwar sa zuwa samun labarin haihuwar É—iya mace , Fada ta shiga Alhini da har hakan ya gaza boyuwa akan fuskar mai martaba ,
Haka aka yi bikin suna cikin rashin Armashi bayan dawowar su daga asibitin "inda yarinya taci sunan "hajiya uwa Asma'u " Sau É—aya mai martaba ya sa aka kai masa yarinyar turakar sa "a washegarin dawowar su daga asibiti" in da yayi mata huÉ—uba tare da bata suna " tun daga ranar bai sake waiwayar su ba.
Ga bangaren safiyyah har ila yau dai bata bayyana wani alama ba ta bangaren ta ,na farin ciki koh saɓanin sa akan sauyin jinsin abun da Saratu ta samu . Ita ma tana fama da nata cikin , da yayi wani irin mugun girma fiye da sauran cikin ta guda uku na baya , hakan ya sa da zainab ta zo bikin sunan ɗiyar Saratu "ta nemi da ta ɗauki Zainab "ubbo"(takwarar ta )
Kasancewar tun da aka mata aure a lokacin shekarun auren ta bakwai bata taɓa samun haihuwa ba "sai bari da take ta faman yi " ganin yadda cikin yayi wa safiyyah nawi ga kuma rigamar zainab wacce ba ta kai ga cika shekaru biyu ba a lokacin "sannan gata da jarabar ƙiuya bata yadda da tarin bayu da suke cike da bangaren nasu da ma gidan baki ɗaya "sai jikin uwar ta , ya sa ta nemi tafiya da ita nan take kuwa safiyyah da Abdoul azizu suka bata zainab ɗin ta tafi da ita "
Ranar goma ga watan biyu na shekarar alif dubu ɗaya da ɗari tara da tamanin da bakwai 10-feb-1987 ita ce Ranar da ta zamto ranar farin ciki ranar da baza'a manta da ita ba a tarihin masarautar maraɗi ranar da ta shiga jeru ranakun tarihi, Ranar da aka wayi gari gimbiyyah safiyyah tana nakuɗa , zuwa hantsi ta haihu lafiya " farin ciki ne ya wanzu akan fuskar gimbiya safiyyah a lokacin da malaman jinƴar da suka karbi haihuwar ta su ke tabbatar mata da ta samun Ɗan ta namiji 'Ƙato da shi jazir ya ɗauko hasken fatar ta irin ta fulanin usul yayin da tun kallon farko da tayi masa bayan da "malaman jinyan suka gama wanke mata shi tare da shirya shi cikin kayan jarirai" tana yi masa kallo guda ta hango tsantsar kamannin sa da kakan sa"mai martaba sarki youssoufa " kamar an tsaga kara , kakaf cikin ƴaƴan da ake haihuwa a gidan babu wanda yayi kama da Mai martaba irin wannan jaririn "Cikin nutsuwa ta dunga kwararo masa addu'ar kariya kamar yadda take jin matsananciyar kaunar sa tana kwarara cikin zuciyar ta da wani al'amari mai girma irin wada bata taɓa jin sa akan sauran ƴaƴan ta ba"cikin nutsuwa ta ɗaga shi dai-dai fuskar ta gami da sumbatar goshin sa , da kuncin sa dama da hagu,
Dai-Dai lokacin da yarima Abdoul azizu ya karaso ɗakin , farin cikin zuciyar sa ya kasa boyuwa daga zuci har zahiri bakin sa ya gaza daina furta kalmomin godiya ga ubangijin sa , ba tare da lura da wurin da suke ba ya haɗa su baki ɗaya ya rungume su , zuciyar sa tana buɗewa tare da sabuwar ƙaunar uwar da ɗan ta ,
Biki sosai aka dunga yi tare da yanke-yanke ana sadaka domin nuna farin cikin wannan haihuwar , har zuwa ranar da takasance ranar raÉ—in suna , É—aruruwan mutane suka hallarci wurin bikin raÉ—in sunan inda yaro yaci sunan "mai martaba "Youssoufa"
A nan wurin kuma mai martaba ya Sa aka yi shela akan bai amince ba a boyewa yaro sunan sa "laƙani " a kira yaro da sunan sa Yarima Youssoufa Abdoul-Azizou Baskore Sunan sa kenan .'''
Bayyana irin bacin rai da bakin cikin da hajiya uwa da saratu su ka shiga bai kwatantuwa "domin a ranar da labarin haihuwar ya iso musu kwana suka yi basu yi bacci ba suna jimami da taya junan su bakin ciki " Amma da yake dukkanin su sun ƙware a harkar kissa da kilbibi , sai suka shafe , hajiya uwa tayi ruwa tayi tsaki akan harkar mai jego da jaririn ta , tayi ƙabe ƙabe akan harkar kome , "ta nuna jika dai nasu ne "
Haka ita ma saratu take wuni a sashin safiyyah tana taya ta raino "a cewar ta " sosai ta sake a cikin jama'a ana ta hidima da ita "yayin da take nunawa mijin ta da ma ita safiyyar cewa youssoufa ita ma ɗan ta ne " (cikin rashin sanin su saratu da hajiya uwa suna nan ƙudurce da mummunan ƙudirin su da su kadai suka barwa kan su sanin sa , Sai kuma Allah wanda yake masanin kowa da kome )
kwance tashi youssoufa yana girma har zuwa lokacin da ya cika shekaru biyu a lokacin ne babban rashi ya samu birnin maraÉ—i , in da mai martaba sarkin youssoufa ya amsa kiran mahaliccin sa bayan Æ´ar gajeruwar jinya ,
haka aka gudanar da zaman makoki cikin alhinin rashin wannan adalin sarki nasu , bayan an share makoki akayi bikin naɗi inda "Yarima Abdoul azizou ya ɗare kujerar mulki "ya zama sarki " a kuma tsukin kwanakin Saratu ta sake haihuwa inda ta sake samun ɗiyar ta mace "wacce taci sunan mahaifiyar ta Maryam" bayan watanni biyu safiyyah ita ma ta ƙara haihuwar ɗan ta namiji ,"da aka sanya masa sunan lamiɗo "
Lokacin da Biyamaradi youssoufa ya cika shekaru biyar da watanni a lokacin ne wani babban rashin ya sake samuwa , Allah ya yiwa zainab kanwar mai martaba rasuwa a wurin haihuwa , ta mutu ta bar ƴar jaririyar ta da ta haifa wacce koh samun damar ganin fuskar ta bata yi ba mai rabawa ta raba " bayan share zaman makoki An samu saɓanin ra'ayi akan wacce zata yi rikon jaririyar zainab da ta ci sunan kakar ta ta wurin uba "siyama " A karshe an tsaida shawarar "safiyyah ita zata yi rikon siyama tare da jaririn ta da ta haifa kwanaki arba'in da suka wuce "Aminu " a dalilin sanin da kowa yayi cewar akwai aminci tare da ƙauna mai karfi a tsakanim marigayiya zainab da kuma safiyyah " domin tun ranar da akayi rasuwar ma jaririyar take karkashin kulawar safiyyah ita take kula da ita ,"take shayar da ita maɗarar da aka tanada domin jarirai sabuwar haihuwa "
Dan haka aka miƙa rikon siyama ga safiyyah tare da mayar mata da ƴar ta hannun ta zainab karama "ubbo" wacce a lokacin take da shekaru bakwai tana aji biyu na primary amma sosai ta shaƙu da uwar goyon ta , babar ta ,kuma takwarar ta marigayiya zainab a saboda rikon gaskiya soyayyah da amana da tayi mata " hakan ya sa ta ɗauki son duniya ta ɗora akan wannan jaririyar da take yi wa kallon ƙaramar kanwar ta take kuma son ta fiye da kannen ta da suka fito ciki guda "
Cike da ƙauna da tsaftataciyar soƴayyah safiyyah ta karbi riƙon siyama "gefe guda na zuciyar ta kuma ɗauke da wani babban burin da take fatan kasancewar sa , wanda ta riga ta ayyana shi akan jaririyar da aka bata amanar ta "
Bayan maryam ita ma saratu ta sake haihuwar É—iyar ta mace "da ta amsa sunan hauwa"u " , kuma ita ce aka yi goyon su tare da su siyama da aminu "
Zuwa lokacin saratu kakaf ta gama bin gidajen bokaye da Æ´an bori akan su taimaka mata ta samu haihuwar É—a namiji "wanda ita ma zata É—aga tace wannan É—an ta ne namiji amma shiru ake ji "wai malam ya ci shirwa " akan cikin 'hauwa'u babu irin tsubbace tsubbacen da basu yi ba ita da hajiya uwa wacce har zuwa lokacin bata saduda ba .
A gefe É—aya suna nan suna shirin kaddamar da mummunan aikinsu ,