Sashe 85
Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kewar da take binne cikin ran yakaka tare da tsananin son biyamuradi youssouf sune suka yi toroƙo suka hana ta sukuni tun bayan rabuwar ta da samy baby , har ƙamshin sa ta dunga jiyowa lokacin da ta sanya kafafun ta cikin sashin doctor hamza wanda yayi mata jagora har zuwa cikin falo , illahirin tsukin wajen ya ɗauki kamshin kakkarfan turaren biyamuradi youssouf wanda yayi tasiri matuƙa wurin ƙarasa lugui-guita rarraunar zuciyar yakaka ta ƙarasa narkewa cikin so da begen biyamuradi ,
Hatta Falmata da Rahima sai da suka fahimci tana cikin damuwa , juyin duniya suka nemi sanin meke damunta ?? Tace musu babu kome a ƙarshe da ta ga sun damu ,musamman Falmata da ta gaza cin abinci dare na kirki , kamar yadda ita ma yakakar ta gaza ci , sai kawai tace kan ta ne ke ciwo , " nan ma dai wani sabon tashin hankali ne ga Falmata domin kuwa kalmar ,"sannu," bata yanke daga bakin ta ba har bacci ya ɗauke su !
WashegariÂ
Misalin ƙarfe 8am Hamza ya ƙira Rahima a waya inda yake sanar da ita su buɗe masa ƙofa zai shigo ya shirya , " daman sun riga sun jima da tashi dan haka.saƙon nasa kawai ta sanar ga su yakaka su dukkanin su suka miƙe ,
A bakin kofar sashin nasa suka haÉ—u da ladabi suka gaida shi ya amsa cikin gaggawa yana amsar É—an mukullin sa da yake hannun rahima,'
 Ku jira ni anan na gama shiryawa yanzu na fito , kar ku tafi ko'ina ," ya furta hakan yana shigewa ," har yayi ciki sai kuma ya kira Rahima suka shiga tare ,"
   Hankalin yakaka ya kai ga manyan rumfunan da ta gan su a kakkafe a harabar gidan birjik wanda bata san lokacin da aka samar da su ba , ana ta faman shimfiɗa manyan dardumai da kilisai a ciki , babbar ƙofar gidan a wangale take ana iya hango kai kawon da ababen hawa suke akan titin da ya bi ta gaban gidan , wata mota ƙirar bus ce ta tsaya a ƙofar gidan ,
Manyan Mata ne su rai shidda suka fito daga motar sai kuma ƴan mata sun kai su biyar , dukkanin su suna yanayi da juna farare ne sol-sol dogaye , mafi akasarin su lafaya ce a jikin su wacce bata ƙarasa ƙasa ba iyakar sangalalen kafafuwan su, hannun su zuwa kafafun su da manyan zanen lalle , jazir "
Manya-manyan jakar bacco sun kai guda biyar suka kinkimo zuwa cikin gidan , waccen da wannan sun kama wannan ma da waccen sun kama , uku daga cikin manyan matan ne basu sa hannu ba wurin É—aukar kayan ,
Daga gefe suka tsaya tare da ajiye kayan hannun su ,
Ɗayar da ta tsaya biyan direban motar itace ƙarshen shigowa ,
Magana tayi musu kafin ta nufo sashin Hamza kai tsaye , su kuma suka dakata daga inda suke , duk abun da suke idanun yakaka yana kan su ta nacewa kallon su , yanayin su ya mata daban da na mutanen da ta saba gani ,
Idanun ta ya sauka akan matar da take nufo su , wacce ita ma hankalin ta ya kai kan su yakaka , sosai suke kallon juna ita da yakaka lokacin da take ƙarasowa gurin ,"
Da wata irin murya da ta fito da sauti sosai tace RAHIMA ,
  Dai-dai da fitowar Rahima wacce jin sautin muryar da ko a mafarki baza ta mance ta ba tana ƙiran sunan ta ya sa ta ƙarasa takowa da gudun gaske ta rungume ta bakin ta na kiran ,
 Amne ! Amnee !
  Rungume Rahimar itama tayi idanun ta na nacewa kallon yakaka wacce ta sunkui da kai tare da riƙo hannun falmata , saboda wani irin yanayi da take hangowa a cikin idanun matar mai kama da idon wata wacce tayi wa farin sani ,"
A hankali ta zare Rahima wacce take ta murna tana dariya daga cikin jikin ta ,
Abnatay wacece wannan ? Ta furta hakan tana nuna mata yakaka da hannun ta da ya sha awarwaro da jaan ƙunshi ,
Yakaka da Falmata ne ,
Su waye su Æ´an uwan ku ne ?
Da É—an murmushi tace , " Æ´an gudun hijira ne yayan mu ya kawo su ," ta É—ora da jawo hannun yakaka ,
  Yakaka ga maman mu ,"
Nan take yakaka da falmata suka buɗe haƙoran su suna dariya kafin duk su kai guiwowin su ƙasa ,
 Mama sannu da zuwa ina kwana , suka haɗa baki wajen gaishe ta ,"
 Da sauri ta ɗago yakaka ,
 Tashi - tashi yarinya ta babu kyau durƙuso a halin da kike ciki , sannun ku kuna lafiya ?
  Lafiya lau duk su biyun suka amsa ,"
ÆŠauke idanun ta tayi daga kan yakaka tana saita nutsuwar ta tace ga Rahima
Ina yayan ku ??
Yana ciki ta bata ansaÂ
Janye idanun ta tayi daga kan su falmata ,lokaci guda ta miÆ™a hanya zuwa ciki wajen Hamza ,Â
zuciyar ta na cigaba da kambama mata wasu kamanni masu karfi dake tsakanin yakaka da Rahimar ta , da a tashin farko da ta ɗaura idanu akan ta ta firgice , ƙewar ƴar uwar ta na mamayar ta har idanun ta suna tara ƙwallar tunowa da ita a take taji gidan ya fara mata duhu ,
kome yana da sanadi kome yana da mafari , nan gidan , nan sashin shine mafarin kome , nan inda dugadugin ta ke takawa a yanzu shine mafarin tarwatsewar rayuwar Rahimar ta da yayi sanadin rabuwar su , ko tana ina ?? Allah shi kaɗai ya sani ..
sai dai jikin ta na bata Rahimar tana raye kuma zasu haɗu zata dawo gare ta , abu ɗaya ne fargaban sa ke guiguiyar ran ta kullum wayewar gari shine Rahimar zata dawo mata ne a matsayin Rahimar ta ƙanwar ta , ko kuwa zata dawo ne da ƙudirin ɗaukar FANSA ,...... ?
******
Nan sashin Hamza , mahaifiyar sa tare da ƴan uwan ta da tsirarun ƙawayen ta , 'tayi bigire daga yau zuwa gobe da zasu yi tafiyar su !
tsakanin ta da dangin mahaifin su Hamza kallon nesa-nesa ne ko gaisuwar fatar baki bata haÉ—u su da kannen mahaifin su hamza ba ,tamkar ma gudun haÉ—uwa da junan su suke ,
saboda ta riga ta ƙullace su irin ƙullata mai tsanani domin tana musu ganin sune SANADIN KOME , kowanne daga cikin su su rai shidda yana da tabon sa a idanun ta idan aka cire UNCLE SALMAN wanda shi kuma a halin yanzu baya raye a duniyar ,...
Su ma a ɓangaren dangin mahaifin nasu kowannen su ya ɗarsawa ran sa tsanar AMINA AL-ARABI SHUWA , saboda wasu manyan dalilai nasu ,"
Cikin awa ɗaya jal da haɗuwar ta da su yakaka , ƙaunar yaran ta gauraye zuciyar ta , dan haka bata jinkirta ba wurin tambayar su labarin su da na iyayen su ,
Cikin sakewar da suka yi da ita suka bata labarin su tirÆ´an-tiryan , kafin su gama tausayin su ya sa zuciyar ta tayi laushi , sau uku tana maimaita musu tambaya game da mahaifiyar su akan menene sunan ta ,
  Amsar su ɗaya ce , su basu san ana kiran ta da wani suna ba bayan maman Yakaka , su kuma suna kiran ta Mama ,!
   Ta jinjina da jin cewar mahaifiyar ta su kurma ce bata magana, ta kuma tausaya , sannan ta cire tsammanin da take ko yaran suna da wata alaƙa ta kurkusa da ita/da Rahimar ta , tasan Rahimar ta ba naƙasasshiya bace ba cikakkiyar lafiyayyar mutum ce , dan haka ta danganta kamannin da take gani na rahima tare da yakaka a matsayin kawai halittar ubangiji ,"
Karfe 10am aka ɗaura auren zainab da angon ta colonel Tahir Ma'aji , inda aka zarce da walima wanda mahaifin Amarya ya shirya ƙarƙashin jagoranci tare da kulawar Hamza ,
A daddafe Biyamuradi Youssouf ya tsaya aka É—aura auren tare da shi , saboda hankalin sa da yake a tashe da son tafiya gidan madam saly dan jin ko an kai ga samun ta ,? "Â
A gurguje yayi wa ango gaisuwar taya murna , sannan ya jaa Tafeeda gefe ,
ÆŠan ouwa ni zani koma bakin aiki ,ils ne me donnent que quarante huit heures , zuwa lokacin da nake issa bakin aiki , awanni sun kai ga cika ,"
Bai damu da kallon tuhumar da Tafeeda ke bin sa da shi ba , ya miƙa masa hannu suka yi musabaha ,
Idan ka cimma gidaa ka kiraye ni ɗan ouwa ,' Allah shi kiyaye hanya ,saduwar Alheri
Zame hannun sa daga cikin na Tafeeda yayi tare da juyawa ya fara taku domin barin wurin ,"
A takaice Tafeeda yace da shi ,"
me zan ce ga hajiya umma tare da mai martaba idan sun ka tambayeni halin da na riske ka ciki ??
 Juyowa yayi da wani guntun murmushi a fuskar ka kace da su ,"
  Yarima na a halin lafiya a bigire mai tsaro ,! Sannan ina miƙa gaisuwa ta a gare su tare da fatan Alheri !
Gyaɗa kai Tafeeda yayi yana mai juyawa ya shige taron jama'a cikin ran sa ya ƙudurce dawowa ya cimma youssouf su fuskanci matsalar sa tare , yanzu ma domin yana cikin ujila ne shi da kan sa awanni arba'in da takwas ɗin aka ba shi , dan haka su dukkanin su basu da isasshen lokaci a halin yanzu !
Motar sa ya jaa da gudun gaske ya É—auki gwadaben da zai sada shi da unguwar madam saly ,
Bai ko rufe motar ba ya taka ya shiga gidan , " a ƙufule ," sai dai tun daga bakin rumfar ya fara fahimtar sauyin da yake wurin domin dai babu kowa a cikin rumfar hatta kujerun cikin rumfar a tattare suke a gefe , da alamu yau ba'a shirin yin aiki ,"