← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 194 OF 269

Sashe 194

Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" Au to to ashe ma musaƙa ce , to babu laifi , ai daman irin ki ake so marasa idon yarinya yau makantar ki ta miki rana , ko kuwa ?

Ya juya ga mutanen da suke bayan sa yana tambayar su ,

amma babu wanda yace ƙala a cikin su , biyu daga ciki suka matsa jikin motar tare da fara ɗaga cikin ramukan kujerun motar suna fito da wasu ƴan madai-daitan kwalaye da basu cika girma ba ,

Falmata da ta durƙusa tana ɗan murƙususu saboda marar ta da take mata ciwo , ta cikin hijabinta tana iya hangen kwalayen da bata san da su ba a motar  kafin zuwa wani lokaci an tara su da ɗan yawa ,

Ɗaya daga cikin mutanen da fuskar sa ke naɗe da mayafi ya sunkuya tare da ɗaukar Ammo box ya buɗe ya zazzago wasu alburusai da suke ciki a jere , hannu ya miƙa na gefen sa ya miƙa masa tocilar hannunsa , ya haska harsashin sosai yana jujjuya shi a hannun sa ,

Cikin Falmata ya bada wani sautin ƙululu lokacin da ta ga an miƙo masa bindiga ya zura harsashin a ciki , wani irin tsoro mai girma ya ziyarceta , meye yaje shirin faruwa da ita ? aina ma wai take ?

Magana suka fara yi bayan sun É—an yi gaba kaÉ—an da inda take tsugunne ba tare da wani ya kulata ba daga cikin su ,

Tsantsar tsoro yasa ta daina fahimtar me suke cewa duk kuwa da cewa da yaren da tafi fahimtar sa bisa ga sauran yaruka suke magana  , idanunta sun fir-fito , bindigogin hannuwansu kawai take bi da kallo da zuwa lokacin ta lura fiye da rabinsu suna riƙe da bindiga .

Da É—aya-É—aya suka jide kwalayen , tana ganin lokacin da suka É—aga kujerar da take baya suka maida wata jakar bacco gurbin da suka cire kwalayen ,daga haka ta ga sunyi musabaha tsakanin Ahmadou Gayu da wasu daga cikin tawagar ,

Da gudu-gudu suka hau bayan motocin su ,suka tada tare da nausawa cikin daji .

Amadou gayu ya ƙaraso kanta lokacin da yake cewa ,

" 'yar dindimi sai ki tasso mu tai na sauƙe ki daga bakin hanya inda zaki iya samun motar da zatta sada ki da cikin garin Maiduguri ni iyakatai bakin daji kome da kin ka ji motsi nai anan ki manta da sautin anan muddin kin biɗarwa kan ki lahia , kin ji kou ?

GyaÉ—a kai Tayi da sauri , ta shiga motar suka sake nitsawa cikin daji , sai lokacin ta lura babu kowa a motar sai su biyu , ko ina sauran mutane huÉ—u na bayan motar ? Ta tambayi kan ta .

**

Ƙarfe sha ɗaya na safe yayi mata a cikin babbar tashar garin Maiduguri , bayan Ahmadou gayu ya sanya ta a mota daga ƙaramar hukumar Mobar da ta kawo ta cikin garin .

Duk tayi busu-busu da ita ta fita hayyacinta , yunwa da firgici sun maida ita firka-firka , amma duk da haka .

Hamdala ta dunga yi lokacin da ta samu tabbacin tana cikin garin Maiduguri ne ta samu ƙubuta daga hannun mutanen da tun-tuni ta fahimci ko su waye su .

tunanin inda zata dosa kuma ya rufe ta , domin ita dai bata san takamai-mai sunan unguwar gidan Prof ba , duk rayuwar ta cikin garin ta yi ne a halin tana makauniya ,

Wata rumfa ta hango ana tuyar doya da ƙwai a bakinta,  ta ƙarasa ta zauna daga ƙasa tana kallom mutanen wajen da fiye da rabin su maza ne hatta mai tuyar da mai rabawar duk samari ne ,

Da zamanta a wajen , wani matashi da ya ciko ɗan farantin roban hannunsa da soyayyar doya mai kwai , ya mata duban ƙasƙanci , kafin ya ajiyewa wani mutum doyar a teburin gaban sa , ya ƙaraso inda take

"Ke baiwar Allah ki tashi daga nan , idan bara za kiyi ki shiga cikin tasha ko kuwa ki nemi wani wajen amma ba nan ba wajen sana'ar mutane .

'kayi haƙuri dan Allah hutawa nake yi , ga kuɗina ka bani abunda kuke sayarwa na duka ,

Ta miƙa masa kuɗaɗen da bata san adadinsu ba da ta zaro daga cikin jakar hannunta ,

Kallon kuÉ—aÉ—en da bana Nigeria bane ya yi , kafin yace

"waÉ—annan takaddun fa ? KuÉ—in ina ne ?

Kafin ya rufe baki ubangidansa ya ƙwalla masa ƙira

   " Bashari wai kana ina ne ?wannan wanne irin tsagoron zunzurutun walaƙanci ne zaka tafi hirar banza ka barni da ayyuka , to wallahi idan har ƙazar nan ta ƙone a mai , na rantse sai ka biya ni dan ni da asara kullum saɓani muke .

Da sauri Bashari ya bar kan Falmata ba tare da ya karɓi kuɗin da take miƙa masa ba ,

Ya ƙarasa da gudu wajen ogan sa ,

"kayi haƙuri oga wata mata ce kamar mahaukaciya dai haka ta zo da wasu kuɗaɗe kamar na landan a hannunta wallahi oga wai ta miƙa min su na bata doya , kuma kuɗin dayawa oga

Da sauri ÆŠanliti ya saki matsamin da yake hannunsa acikin mai ba tare da ya tsame doyar ba ,

"kai Bashari na fa sanka da sakin ƙwai , kuɗin landan fa kace ? Dala fa kenan ? Yau a masu sayen doyar tawa har da masu Dala ? Ina take ? Nuna min matar ?

Nuno masa Falmata yayi da har lokacin take takure a zaune ,

Cikin ƴar marairaicewa Ɗanliti ya kwararo mata sallama , da sauri ta ɗago kanta jin muryar wanda ta taɓa sani a baya ,

Suka yi arba da fuskokin juna, shirun ƴan wasu daƙiƙoƙi suka gifta kafin Falmata ta miƙe tsaye da sauri tunowa da tayi da ko wanene Ɗanliti.

' wa nake gani haka kamar un-un Ɗankachallari ?  Wai kece ko kuwa kamanni ne ? Ah ai babu zancen kamanni ma ga ƙwala-ƙwalan idanun nan daga ina kike ƴarkachallari haka kamar 'yar bina ?

Muryar ta na É—an rawa , tace

" Ba sunana ba kenan , sunana Falmata ,

' haka fa ashe sunan ki kenan , to dawo daga nan a kawo miki doya ki ci ki sha ruwa ko kya samu nutsuwa , na ga yunwa na tanɗar bakin ƙirshirwa a fuskar ki .

A ɗarare ta zauna a inda yake nuna mata kan wani benci , aka kawo mata zazzafar doya da ƙwai har da dafaffen ƙwai guda biyu da aka soya su da ƙwai ,

Tas ta cinye ta sha ruwan leda biyu , tayi hamdala

ÆŠanliti da yake gurin suyar sa ya bari tare da sake dawowa yana sake tambayar ta daga ina take ?

A takaice ta faÉ—a masa daga inda take , daga haka tayi shiru

ÆŠan jimm yayi yana kallon ta , kafin yace

" wai , tabÉ—i yanzu nan daga Niger kike ? shiyasa mana na ga kin koma busu-busu , ashe rairayin hamada ne ya turbuÉ—e ki , ai kin ma kaima barka da sahara bata haÉ—iye motar ta ku ba kamar yadda nake ji ana labari wai-wai , koda yake da kuma kun yi mutuwar shahadar nan da kowa ke nema ,

" nima kin ga ai yanzu duk na tuba na daina abunda yake jawo min tsinuwa , na kama Æ´ar sana'ata da nake rufawa kaina asiri da ita , aure ma nake shirin yi , O ni ÆŠanliti mutuwar Saly Fara ta zamanto min alherin da na samu shiriya a domin ta ,

  Ya ɗaga hannun biyu sama , yana ƙara cewa
      "Allah na ƙara gode maka da ka kashe Saly Fara ni kuma ka shiryar da ni .

Shiru Falmata tayi tana sauraren bayanin da bata nemi jinsa ba , ji tayi ya cigaba da cewa ,

" ai Æ´ar danginku ma zan aura wallahi kuwa ,

ÆŠago kanta tayi ta dube shi ,

"Æ´ar dangin mu ? Tambaye shi da mamaki ,

" eh Ƴar uwarku Yagana ba , ni kuwa ina Yakaka wallahi habibiya tana nemanta ruwa a jallo tace tayi ta zuwa gidan da kuke bata samun ku , can gidan wani mutum mai kuɗi wai a Danboa road ko ina ?

Da sauri Falmata tace ,

  "Ina Yagana take ? ta san gidan Prof ? Ka kaini wajenta ta kaini gidan Prof ,

Kwantar da hankalin ki indai habibiya kike nema kin same ta tunda kika ganni , nan da mintoci talatin ma zaki ganta anan ta zo , ai tare muke sana'ar mu , ita take yi mana wanke-wanken farantan kayan sana'a , kinsa rayuwar nan cuÉ—anni na cuÉ—eka ne .

****

Yagana ita ta sada Falmata da gidan Prof da misalin ƙarfe biyu na rana , har falon prof ta so shiga da ita sai dai aka hana su saboda yana tare da baƙi , amma an musu iznin shiga ciki sashin matar gidan domin su jira shi .

"Falmata ai tunda na kawo ki ni zan iya tafiya ko ?

Yagana take neman iznin Falmata bayan sun kawo ƙofar sashin su Rahima ,

"Yagana , Nagode , Nagode zaki iya tafiya ,

"Babu kome Falmata ai mun zama Æ´an uwa banda sharrin shaiÉ—an da ya rinjayeni a baya na aikata kuskure , Dan Allah idan Yakaka ta dawo zan zo na nemu gafararta ta yafe min .

Nan suka yi sallama ,ba tare da Falmata tasan wanne kuskure Yagana ta aikata ba da take neman yafiyar Yakaka ,

Jikinta babu ƙarfi ta nufi cikin gidan , a zuciyarta tana saƙa yadda zata yi ta tunkari Prof da zancen ya raba aurenta da Youssouf batare da ta bayyana mummunan laifin da suka aikata ba shi da Yakaka ,

Saboda bata so wasu su dubi Yakaka da wannan mummunan laifin , zata zama abun aibatawa a wajen Al'umma ,

A hankali ta tura ƙofar falon ta shiga sanyi da ƙamshi mai daɗi ya buso ta , daga ciki kaɗan ta tsaya tayi sallama da zazzaƙar muryarta ,
Chapter 194 · 0% Book details