← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 269

Sashe 73

Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwanakin da suka biyo bayan zaman Su yakaka a gidan su doctor hamza , kwanaki ne mafiya jin daɗi da walwala agare su a bakiɗayan rayuwar su ,sun gyagije sun yi fes da su tamkar da ɗai basu taɓa shan wata wahalar rayuwa ba ,

Doctor hamza yayi bajinta sosai ta yadda ya ɗau nawin duk wasu lamuran su na yau da kullum babu gajiyawa babu ƙorafi ko tozarci irin na wasu mutanen, a gefe kuma ya gama shirin sa na sanya su a makarantu , inda ita yakaka yayi mata rajista da wata makarantar matan aure ta jeka/ka dawo boko zallah , zata fara zuwa bayan ta haihu ,

Falmata kuma yana fafutukar nema mata wata makarantar makafi mai zaman kan ta , wanda su a shekara mutane 70 kachal suke É—auka , yana sa ran za'a samu gurbin sanya falmata , '

Amma a halin yanzu su duk biyun ya ɗauka musu wasu malamai biyu mata   ɗayar tana zuwa da rana kamar karfe sha biyu bayan ta taso daga makarantar islamiyyar da take koyarwa , sai ta zo ta koyar da su karatun addini , zuwa karfe biyun rana , wacce take koyar da su boko kuma zata iso karfe huɗu na yamma zuwa karfe shidda take tafiya , ita falmata kome da baki ake koya mata tana saurara a halin yanzu tun da ba makarantar su ta makafi aka kai ta ba , yayin da ita kuma yakaka ake koya mata har da rubutu ,

Kuma babu laifi ƙwarai suna da saurin fahimta musamman ma falmata , ba'a maimaita mata karatu , daga an fadi ta haddace sa kenan,  ga ta da baiwar harce iya fidda lafuza Sam bata da tsamin baki, "hakan ba ƙaramin farantawa doctor hamza yake ba , da alama yaran baza'a sha wahalar sauya musu rayuwa ba !

Ta ɓangaren ƙannan sa ma basu da wata matsala , zainab da hafsa sune manya kuma sun girme musu sosai zainab tana da ishirin da biyar hafsa tana da ishirin da uku ,dan haka tsakanin su da su yakaka gaisuwa ce kawai bayan haka ko kula sabgar su basa yi , basu ma cika zaman gidan ba domin a halin yanzu ma shirye shiryen bikin zainab ɗin ake nan da sati uku inda zata auri wani babban sojin sama ,

ita kuwa hafsa boko yayi zafi domin yanzu ne take matakin ƙarshe a jami'a ga kuma taya ƴar uwar ta shirye shiryen biki da suke , tunda ba uwa bace da su a kusa , kusan su biyun suke duk wasu tsare-tsaren su na ƴan mata , sai kuma ƙannen mahaifin su uku mata da su kuma suke gudanar da sauran lamuran da yakamata iyaye mata suyi ,"

dan haka daga su sai rahima da ta zama ƙawar su su duka biyun suke gudanar da lamuran su , domin ta biye musu sosai tana kwasar duk wasu gidancin su da ƙauyencin su da suke yi sumfuri-sumfuri kuma dai-dai gwargodo tana iyakar yin ta wurin wayar musu da kai a duk lokacin da suka yi wata katoɓarar .

   A halin yanzu sun samu kusan watanni biyu kenan a gidan ,

Kamar kullum bayan dawowar sa daga aikin sa da ya wuni yana yi , ya shigo bangaren sa bayan ya baro bangaren baba inda ya daɗe suna tattaunawa mafi yawa muhawarar ta su akan sha'anin auren zainab ɗin ne , suna tsare-tsaren yadda kome zai tafi cikin tsari mai kyau , sai kuma  a ƙarshe kamar koyaushe idan suka yi zama irin wannan sai hamza ya shigo da batun mahaifiyar su ko da a fakaice ne , a yau ma nema yayi da mahaifin nasu ya amince a sanyo ta cikin lamuran bikin zainab ɗin kasancewar ta babbar ɗiyar ta mace da a karon farko za'a aurar , a wannan lokacin fiye da lokutan baya ya ga bacin ran baban su , inda ya rufe ido yayi ta faɗa a ƙarshe yace kar hamza ya sake sako mahaifiyar su cikin lamuran bikin zainab , shine mahaifin su shi Allah ya ɗorawa alhakin aurar da ƴaƴan sa , ba wata chan daban ba wacce ta zaɓi rayuwar kororo akan zaman aure ,"

Idanun sa taf da hawaye ya baro sashin yana jin zuciyar sa na ƙara bunƙasa girman laifin ta ,

Kai tsaye banɗaki ya shiga yayi wanka gami da ɗauro alwalar sallar magariba da ta gabato , ya zira jallabiyar sa tare da sanya ɗan silifa ya rufe sashin nasa ya nufi cikin gidan ,"  hannun sa riƙe da wata ledar da ya biya ya ɗauko a mota mai tambarin "down town" , tare da wata bakar leda .

A zaune ya tadda su , suna sake biya karatun su da malamar su ta boko ta yi musu yanzu ta tafi ,' Rahima na yi musu gyaran ƴan ƙananun kalmomin english da ma'anonin su da aka fara koya musu bayan sun gama haddace Alphabet ,"..
  Cikin idanun yakaka ya fara jefa kallon sa,  lokacin da ya ƙaraso cikin falon ,
   Da sauri rahima ta miƙe gami da karɓar ledar hannun sa suna masu haɗa baki su ukun wurin yi masa barka da zuwa tare da gaishe shi ,"

  Yana daga tsaye yana ɗaura agogon da ya zaro daga aljihun wandan sa yake amsa gaisuwar su , "
         Da fatan suna muku karatun yadda kuke ganewa ?
   Ya tambaye su yana mai nacewa kallon fuskar ta ,
  A tare suka haɗa baki su biyun wurin amsa masa ,"
   Muna ganewa sosai yaya dakta ,"
Toh madallah a cigaba da dagewa ,"babu dai wata matsala ko ?

Babu matsalar kome yaya mungode,!

Daga haka ya fice jin an fara kiran sallah ,

Da zumiɗin su suka buɗe ledar da ya kawo musu duk da sun riga sun san abunda yake ciki , ilai kuwa shawarma ce naɗi biyar , kowaccen su ta ɗau ɗaya suna murna, ɗaya ledar kuwa agwaluma ce manya-manya nunannu har cikin ledar , ai kuwa yakaka tana ganin agwalumar ta ajiye ƙunshin shawarmar ta gami da sunkutar ledar agwalumar baki ɗaya ,
    da sauri ta yunƙura tana tura cikin ta wanda zuwa yanzu har ya shige watanni shidda , kitchen ta je ta wanko musu , ta miƙawa rahima da tace zata sanya musu a firiji ta ɗan yi sanyi kafin su idar da sallah ,

Bai shigo gidan ba sai bayan sallar isha'i , kamar yadda yake ka'idar sa idan ya shiga masallaci sallar magariba bai fitowa sai yayi isha'i muddin ba wani aiki ne mai girma a gaban sa ba , zama yake yayi ta karatun Alqur'ani .

Rahima , yakaka da hafsa ya tarar suna zaune a ainahin babban falon suna hira tare da kallon wani shirin larabawa da ake nunawa a tv , hannun kowaccen su riƙe da agwalumar tana shaa ,

Da murmushi a kan fuskokin su suka masa sannu da shigowa , hafsa ta miƙe ta shiga kitchen ta fito hannun ta riƙe da babban faranti wanda aka jera kuloli bisa ,

     Miƙa masa tayi ,ya karɓa tare da maida ganin sa sashin da yakaka take zaune ,"

    Ki shirya gobe ne ranar komawar ki asibiti su duba ki , da safe zan kai ki saboda ina da aikin safe ,"

Charaf hafsa ta karɓi zance ,"
   Big bro kayi tafiyar ka kawai aikin ni zan kaita , ko ba Galaxy hospital ba? 
     Nan ne , amma nafi son na kaita da kaina saboda akwai wata matsala da muke kan tattaunata da likitan ta ,"
    Ki ƙira min zainab ku zo sashi na tare inason yin magana da ku ,!

    Daga haka ya juya yana barin wurin ,

   Ya bar hafsa nan tsaye da tarin wasi-wasin da take yi akan alaƙar yayan su da wannan ƴar gudun hijirar , kulawar da ta lura yana bata yayi yawa ya wuce na taimako ," meye a tsakanin su ? Tasan yayan su kamili ne kuma managarci bata zargin zai aikata wani mummunan abu , tunanin ta yafi karkata akan wani yanayi da take hangowa a kan fuskar sa a duk lokacin da ya ga yarinyar da kuma tsantsar kulawar da yake mata duk a sunan taimako ," ko ma menene a sannu zata kai ga fahimta fatan ta Allah ya sa ba abun da take zato bane , ,"

Cikin sati biyun da suka biyo baya shiri ake gadan-gadan na bikin zainab shi da kan sa hamza bai zauna ba , shirye shirye suke ka'in da na'in kasantuwar wannan ne biki na farko da za'a yi a gidan nasu , ƴan uwan su na nesa nesa duk sun fara isowa , haka ma wasu ƙawayen zainab ɗin sun fara sintiri ganin cewa an shigo satin fara bikin sam ƙafa bata ɗaukewa a gidan  , ƴan aiki huɗu mata doctor hamza ya kawo amma duk da haka aiki da aike chakuɗe musu yake ,'

Yakaka da Falmata duk a takure suke , ko falon basu cika son fitowa ba suna ƙunshe cikin ɗaki sai fa idan rahima ta tuno su tazo ta ishe su da surutu tare da mitar meyasa basa son fitowa cikin jama'a ," ??

   Yau ya rage saura kwanaki uku ayi ɗaurin aure kuma a yau ne za'a fara gabatar da shagulgulan bikin , inda a yau ɗin ne suke shirin yin arabs day dan haka gidan danƙam yake da ƴan mata kawayen ita amaryar da yawancin su daga nesa suke , sun yi guzurin manyan jakankunan su da suke cike da suturun su zuwa kayan kwalliyar su da takalma , dukkanin su gogaggu ne kuma wayayyu , kuma ƴaƴan manya irin ta, yawan su ya sa ɗakin ta ya gaza ɗaukar su , dan haka suka rarrabu wasun su suka samu wuri a ɗakin hafsa , da rahima , sauran ukun kuma suka sauƙa a ɗakin su yakaka ,

Tashin farko lokacin da suka shiga É—akin da suka ga su yakaka , É—aya daga cikin su ta tambayi zainab É—in da ta rako su É—akin da kan ta
Chapter 73 · 0% Book details