Sashe 204
Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan sun gama ɗokin ganin juna , Maimounatou ta kasa ɗauke idanun ta daga kan sa duk wani motsin sa ƙara burge ta yake yana sake nutsar da ita cikin ƙaunar sa ,
Yadda yayi shar da shi yayi gayu ya sake fiddo tsantsar kyaun sa , da cikar zatin sa na matashin Namiji , kasa jurewa tayi ta tambaye shi ,
  " Ghaddafi ina ne ka samou dukiya hakka mai yawa har ka sai moto ta hawa , ka gan ka kouwa yadda kayi gayu tamkar ɗiyan saraki wallahi ka burge ainun ,
 Ƴar dariya yayi ,kafin yace da ita
  " cikin dukiyar amren mu da na fara taru na ɗauki kaɗan na sayi suturu doumin nayi kwalliya na burge ki , kadda samarin jami'a ƴan gayu su kwace min ke ,
Ba tare da ta damu da ta tambaye shi wacce sana'a ya fara yi ba ta washe ƙaramin bakin ta tana cewa
  " Duk faɗin babban birnin Niamey babu namijin da zai iya kwace maka ni Ghaddafi ,
Â
Da murmushi a fuskar sa ya buÉ—e kujerar motar sa na baya ya shiga fiddo manyan kwalayen da yayi mata birthday gift yana jera mata a gaban ta ,
Zuciyar ta tana sake bunƙasa da ƙaunar sa take bin sa da kallo bata ƙi ba ace cikin wata mai kamawa a ɗaura auren su .
*****
Cikin shekaru huɗu na karatun ta Ghaddafi ya bunƙasa ya zama hamshaƙin attajiri , ya ma ɗauke iyayen sa da ƙannen sa daga Niger ya mayar da su can ƙasar su Mali ya gina musu sabuwar rayuwa ya ƙere musu gida na zamani .
Zuwa lokacin ita da kan ta Maimounatou tasan Ghaddafin ta ya sha kwana , ana kuma damawa da shi a harkokin masu dukiya , sai dai ita da kan ta ba zata ce ga takamaimai sana'ar sa ko aikin sa ba , baza ta ce ga inda yake samun kuÉ—aÉ—en da yake mata wasa da su cikin kyautuka na bajinta ba da har wasu lokutan takan yi masa faÉ—an kuÉ—aÉ—en sun yi yawa , amsar da kullum yake bata shine
    " wannan kaɗan ne dagga cikin dukiyar Amren ki da nake biɗa ina tarawa Maimounatou,
Soyayyar su kuwa sai abunda yayi gaba kusan kowa da yasan Maimounatou yasan da soyayyar ta ga Ghaddafin ta , idan aka cire iyayen ta amma hatta Æ´an uwanta makusanta kowa ya san sunan sa , sun kuma shaida wasu daga cikin manyan kyautukan da yake yi mata ,
Haka shi ma ta ɓangaren Ghaddafi tun daga kan iyayen sa da ƴan uwa zuwa abokanan sa tun na farko da suka riga daman suka san da Gimbiya Maimounatou har zuwa kan sabbin abokan sa babu wanda bai san labarin Gimbiya Maimounatou ba ,
A cikin shekarar ne kuma gwamnatin ƙasar Niger tayi hoɓɓasa kan gagararrun ƴan fashi da makamin da suka addabi baki ɗayan kusurwowin ƙasar ta Niger ta kan kowacce boda guda bakwai da kasar ke da su ta Nigeria, Chad, Algeria, Mali, Burkina Faso, Libya, da Benin. sun hana duk wani ɗan kasuwa shan ruwa ya tsirga masa cikin ƙasa da shekaru biyar , da har suna ne da su na musamman da ake ƙiran su da shi escouade de lions .
escouade de lions sun gagari kananun sojoji su waye kuma ƴan sanda ? bare kuma ma'aikatan hana safara da miyagun kaya , ƙananan ƙwari a wajen su kenan ,
Kisa suke tare da ɓarna yadda suka so suka ga dama , gwamnati ta rasa yadda zata yi da su , dayawa daga cikin su ɓoyayyun fuska ne da su babu takamaimai wanda ya san fuskokin su , sannan an gaza gano takamaimai madakatar su da za'a iya taƙile su ta nan .
Youssouf Abdoul-Azizou Baskore ,shine sojan da babban hafsin soja na ƙasar Niger ya wakilta a matsayin wanda zai ja tawagar aikin da zai kawo ƙarshen waɗannan gungun ƴan fashi da makamin , lokaci kaɗan bayan dawowar sa daga ƴakin da aka tura su Libya.
Cike da zuciyar jarumta da son kare hakkin ƴan ƙasar sa Youssouf ya karbi aikin da aka ba shi , inda ya nemi taimakon haɗin guiwar ƴan sandan ciki da dole sai da taimakon su za'a kai ma nasarar cafke ƴan fashi da makamin .
A dai-dai lokacin rayuwa ta yiwa Ghaddafi da Maimounatou daɗi domin watanni uku kaɗai ya rage mata ta kammala karatu baki ɗaya ta bar makaranta , abu na gaba shine ta gabatar da Ghaddafi ga iyayen ta , a ɗaura musu aure daga nan su shilla zuwa ƙasar France da suka zaɓe ta a matsayin kasar da zasu barji amarcin su a can.
Kafin cikar watannin wani irin liƙewa Ghaddafi ya yiwa Maimounatou koyaushe yana sintiri tsakanin garin da yake da Niamey ,
Duk da cewa Maimounatou tana jin daɗin yadda yake yawan ziyartar ta a ganin ta ƙaunar da yake yi mata ne take sake hauhawa a zuciyar sa da daman take tantamar kamar ƙaunar da ita take yi masa yafi wanda yake yi mata yawa ,
Sai dai yadda yake yawan taɓa ta tare da bayyana mata cewa shi fa a sarari a matse yake da ita yana da muradin ta , lamarin yana damun ta , domin ita ta san bata cika ƙarfi ba muddin akan ƙaunar Ghaddafi ne , sannan.ta ɓangaren gangar jikin ta ma rarrauna ce .
Cikin haka abunda take ƙoƙarin gujewa ya auku , shaiɗan tare da tsantsar son da take yi masa ya sa ta bashi kan ta a wani dare ,
Daga lokacin kuma sai gurɓacewa ta shigo cikin soyayyar tasu domin tamkar busa ake musu ko umarni , koyaushe suka haɗu sai sun yi ta'asa kafin su rabu , a hakan daga zuciyoyin kowannen su niyyar auren juna bata sauya ba , a ganin su zinar da suke ba kome bace tunda aure zasu yi illa ƙarawa juna so tare da ƙoƙarin kiyaye juna daga zuwa ga waɗansu mutanen daban ( abunda matasa dayawa suke ta'alaƙa ƙazamtatciyar rayuwar su akai , ba kome bane illa tsagoron son zuciya da rashin shan tsabga da ace ana zane matasan mazinatan da duk aka kama da laifin zina a nahiyar mu kamar yadda addini ya tanadar da abun ya ɗan ragu ) .
Daren yau bayan sun gama fasiƙancin su a ɗakin otel ɗin da musamman Ghaddafi yake da ɗakin sa ,
  Yake sanar da Maimounatou kan cewa tafiya ta kama shi zouwa Benin da zai iya kaiwa tsawon kwanaki goma kafin dawowar sa da zuwa lokacin kwanaki biyu kachal ya rage tayi jarabawar ta, ta ƙarshe .
  Ba domin ran ta ya so ba suka yi bankwana washegari da safe da alƙawarin zasu dunga yin waya koyaushe , ya kama hanya bayan ya ajiye ta a bayan makarantar su .
Sun cigaba da yin waya har kwanaki uku bayan tafiyar sa kafin daga baya kuma ta daina samun wayar sa , shima kuma bai ƙira ta ba , ta damu ainun saboda hakan ɓakon lamari ne a gare ta su shafe tsawon wasu kwanaki ba tare da sun yi magana a waya ba ko da kuwa baya ƙasar .
Wasa-wasa sai da suka shafe tsawon kwanaki shida babu waya a tsakanin su zuwa lokacin hankalin maimounatou ya kai ƙurya wajen tashi , jarabawar ta ma sai tayi da gaske take iya rubutawa ,
Bata da aiki sai gwada ƙiran layukan sa da duk take da su , cike da fatan ko Allah zai sa ta same shi ,
Bayan ta fito daga jatabawar ta ta yau waje ta samu daga can gefe ta zauna tana cigaba da lalubar layin Ghaddafi , amma kamar koyaushe cikin kwanakin duk layukan sa basa tafiya ,
Tsumu tayi a zaune idanun ta cike da ƙwalla , hirar da ta ji wasu matasa na yi daga gefen ta ta ɗan ɗauki hankalin ta , inda ta ji suna labari akan jajirtatcen sojan ƙasa Youssouf ɗa a wajen sarkin Maraɗi wanda cikin watanni da basu cika uku ba , a kwanaki biyar da suka wuce tawagar sa da yake jagoran ta ta tarwatsa gungun ƴan fashi da makamin da suka yi mafaka akan tekun rairayin saharar tenere da yake boda tsakanin Niger da Chad ta yankin Bilma dake ƙarƙashin jahar Agades.
An kashe mafi yawa daga cikin ɓarayin manya daga cikin su kuma sun gudu , ciki har da shugaban su da ba'a kai ga sanin cikakken sunan sa ba amma bayanai sun tabbatar da cewa ɗan asalin ƙasar Mali ne .
Kalmomin yabo iri-iri suka dunga yiwa Biyamuradin maraɗawa , bayan sun gama tsinewa ƴan fashi da makamin suna kuma fatan Allah yasa a kai ga samun nasarar kashe sauran da suka rage ko Al'umma sa yi kai-kawo a tsakanin ƙasashe cikin kwanciyar hankali ,
Ita bata wani ji abun burgewa ba , idan ba lalacewa ba me yakai É—an sarki Yarima a yadda ta ji sun faÉ—a , yin aikin soja bauta ?wannan ai shine a aiki kare ya aiki wutsiya .
Miƙewa tayi tana nufar wajen da ɗakin kwanan ta yake sai dai kafin ta ƙarasa ta ji wayar ta na kiɗan shigowar ƙiran Ghaddafi , cike da ɗoki ta daga wayar tana ajiyar zuciya tamkar wacce tayi gudu .
Cikin abunda ke ƙasa da mintoci goma sha biyar tayi shiri cikin doguwar ɓakar rigar ta ta rufa hula baƙa a kan ta tare da rufa ɗankwalin rigar da ta kare rabin fuskar da shi tundaga kan ta , ta nufi babban wajen hutawar da Ghaddafi ya sanar mata yana jiran ta a wajen ta je ta same shi .
Yadda ta gan shi duk a firgice da ƙananun raunika a fuska da hannuwan sa da suke sarari ya duƙushe tasirin farin-cikin ganin sa da tayi , sai ta shiga tambayar sa kan ko hatsarin mota yayi ? Ko kuwa ƴan fashi ne suka tare sa akan hanya ,?