Sashe 151
Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Girgizan da jirgin ya ɗauka shi yasa ba shiri Falmata ta sake ɗora ɗayan hannun ta akan na Youssouf tana ƙanƙame sa hannayen su suka cure guri guda , kamar yadda zuciyoyin kowannen su ke ƙoƙarin jawo kusanci a tsakani .
Idanun sa a kafe kan fuskar ta dake bayyana tsoro ɓaro-ɓaro .
Cikin ikon Allah jirgin ya samu dai-daituwa a sararin subahana ya shilla da gudun gaske cikin tafiyar gaibu bisa iska a tsakanin sama da ƙasa .
Nigeria
Tafiyar kwana ɗaya da yini biyu ta sada Hajja da birnin Maiduguri , da la'asar sakaliya motar da ta kawota ta dakata a ƙofar gidan Prof .
Kai tsaye ta sauƙa ta shiga gidan , tarɓa ta musamman ita da direban suka samu daga sabbin ƴan aikin gidan guda biyu tare da Rahima da daman duk ansan da zuwan su .
Bayan magarib ta nemi iznin zuwa gaishe da prof da zuwan su a ɗazu suka tadda shi tare da baƙi , hakan ya sa basu samu ganin sa ba sai yanzu .
Bayan doguwar gaisuwa tare da godiyar da akayi musayar su tsakanin Prof da Hajja , taƙaitatciyar hira suka yi wanda duk rabin ta akan Al'amuran da suka shafi taɓarɓarewar tsaro ne tsakanin Niger ɗin da Nigeria da har kawo yau Ƴan tawayen Boko Haram basu saduda sun bar yin kisan mimmiƙe tare da ɓarnannaki tsakanin ƙanana da ma manyan garuruwan Niger da Nigeria ba .
Sannan kuma har kawo yau gwamanatin ƙasar Nigeria ta gagara kawo ƙarshen hare-haren ƴan kungiyar duk kuwa da cewa cikin ƙasar tushe da MAFARIN kafuwar ƙungiyar da ta jefa Dubunnan rayukan Al'umma cikin HARGITSIN RAYUWA yake .
Shin yaushe ne kome zai kawo ƙarshe ? Yaushe ne abubuwa zasu koma dai-dai ? Yaushe ne za'a ƙira ƙungiyar Boko Haram da shuɗaɗɗan lamari da ya zama tarihi ? Allah Shine Mafi sani .
Hajja ta miƙe ta ƙarasa gaban Prof tana miƙa masa envelop ɗin dake ɗauke da hoton Mama ,
Alhaji ga hoton Amaryar taka ta Niger ka ga yadda ta girma duk da ƙarancin lafiyar ta amma ta miƙe .
Miƙa hannu yayi ya karɓa yana dariya , dai-dai da shigowar Doctor Hamza wanda ya dawo daga Masallaci .
To toh Masha Allah , Babu kome ai kowacce cuta Allah yayi maganinta , sai dai idan har sanin É—an Adam bai kai ga gano maganin ba .
Ƙwarai maganar ka dutse Alhaji .
  Cewar Hajja .
ya zaro hoton yana gyara zaman gilashin idanun sa , bayan sun haÉ—a baki wajen amsa sallamar Doctor Hamza ,
ka ga Babban Likita , Likita bokan turai , ƙarshen ƙwaƙƙwafi da bincike sai likita , lalle tafiyata bana me sa'a ce tunda naci karo da kai , shekaru fiye da biyar rabona da na ganka .
Murmushi yayi yana zama daga gefen ƙafafun Prof .
Hajja sannun ki da zuwa , da fatan kin samu isowa lafiya ?
Lafiya ƙalau Likita ,yaya bayan rabuwa ? Ya iyalin naka ?
Duk kowa lafiya hajja .
To Alhamdulillah .
Masha Allah wannan Amarya tawa ai tafi kama da Æ´aÆ´an nasara , ga dukkanin Alamu tana da wayo .
Prof ya furta haka yana mayar da hotunan cikin envelop É—in .
Wayo kuwa na sosai Alhaji ai Mama sai godiyar Allah ba shakka tana da kaifin ƙwaƙwalwa da saurin ɗaukar abu
Allah shi rayata , ya bata lafiya , yayi Albarka cikin rayuwarta ita da sauran yaran musulmai baki É—aya !
Ameen Ameen Alhaji
Hajja ta amsa tana sanya hannuwanta biyu ta karɓi envelop ɗin da yake maida mata , ta miƙe tana yi musu bankwana tare da barin falon ta koma cikin gida .
Baba , wacce yarinya ce hajja ta kawo maka hoton ta ?
Doctor Hamza ya tambayi Prof .
Ya buÉ—e baki da zummar bashi amsa shigowar É—aya daga cikin dattijan unguwar da suke cin abincin dare tare da Prof ya katse musu hirar .
Abuja
Yakaka ce a zaune kan hannun kujerar falon Malama Maryam gabanta kuwa babbar jakar kaya ce da take shaƙare taf da kaya , daga gefen ƙafafunta ma wata ƴar matsakaiciyar jakar ce .
tana shirye tsaf cikin dogon hijabinta da yake har kusa da idon sawun ta , fuskar ta fayau babu ko kwalli , ramar da tayi ta fito sosai akan fuskar ta da idanunta da suka É—an zurma ciki .
daga gefe a cikin falon Lubna ce a zaune tayi jugum tana kallon Yakaka wacce idanun ta ke kallon ƙasa , tayi shiru tamkar ba sune masu yin dararraki ba muddin suna waje guda .
Malama Maryam ce ta fito itama shirye take , ta kai dubanta ga Yakaka tana jin yadda tausayin ta ke sake narkar da ranta tabbas Yakaka tana buƙatar majiɓanci cikin Rayuwar ta .
Yakaka tashi mu tafi , lubna taya ta É—auko kayan ku kai cikin mota Abban ku yana jiran mu , kar mu rasa motar farko ko ta biyu , saboda mu samu isa da wuri tafiya daga Abuja zuwa Maiduguri da tazara gara muyi sammako .Â
Jikin Lubna babu kuzari ta miƙe tana gyara zaman hijabin jikinta ta sunkuya ta ɗau ƙaramar jakar tare da kama gefen babbar ta taya Yakaka riƙewa ,
Sun zo tsakar gida Lubna ta jaa ta tsaya da hakan ya sa Yakaka waigowa .
idanunta cike taf da ƙwalla tace
Sahiba irin rabuwar da zamuyi kenan babu bankwana ? Shekaru biyar ba kwana biyar bane Sahiba ban so ba zaki tafi tare da maÉ—aukakiyar damuwa .
É—an guntun murmushi Yakaka tayi ,
Sahiba kin san har abada kina cikin mutanen da bazan iya mantawa da su ba cikin rayuwata , cikin kowanne irin hali na tsinci kaina , nima zanyi kewar ki Lubna , ta ƙarasa zancen siririyar ƙwallar da bata shirya zubowar ta ba na sauƙa bisa ƙuncin ta .
Idan kika tafi a yanzu waye zata maye min gurbin ki ? Waye zata zama babbar ƙawata a bikina ? Da ke muka tsara kome Yakaka .
Idan Allah ya yarda zan dawo Lubna , zan halarci bikin ki na ɗau Alƙawari , amma dole na tafi a yau shekaru biyar Falmata tayi cikin rashina ,
Hon ɗin da aka matsa da ƙarfi shi yasa suka fara taku cikin hanzari ba tare da sun sake musayar wata kalma ba a tsakanin su .
Ƙarfe takwas da rabi na safe motar da su Yakaka tare da Malama Maryam suka shiga domin tafiya Maiduguri ta ɗau hanya ɗoɗar .
Tafiya ce me nisa ta tsawon fiye da awanni takwas tsakanin Babban birnin tarayya Abuja da Birnin Maiduguri dan haka a saboda yawan tsaye-tsaye akan hanya daga jami'an kula da hanya da suke gudanar da bincike , ya sa dare ya fara shiga har ƙarfe shida na yammaci ta gota , wanda hakan kuma ya sa dole su yada zango a garin Damaturu saboda lokacin dokar hana zirga-zirgan motoci ya shiga ( curfew) ala tilas suka kwana a tasha ,
Washegari da hantsi ƙarfe tara suka shiga garin Maiduguri , a idanun Yakaka babu wani sauyi da garin ya samu tsawon shekaru biyar ɗin ko kuwa dan hankalinta bashi kan duban yanayin garin ne ? Baki ɗaya ta ƙagauta ta ɗora idanunta akan ƙanwarta da ƴar ta .
Tsawon lokacin rabuwar ta da garin bai sa ta manta da sunan unguwar da ta bar Falmata ba , dan haka bayan sauƙar su a tasha kai tsaye ta shaidawa direban taxi da ya ɗaukesu da kayan su unguwar da zai kai su .
tafiyar mintoci 15 kachal ta sada su da unguwar , layi bayan layi ta kwatantawa direban har zuwa gaban gidan da a koyaushe yake yawan samun gyaran da yake sake fiddo kyaun tsarin ginin dai-dai da na zamani .
Bayan sun sauƙe kayan su a gefen hanya daga jikin katangar gidan Yakaka tace ga Malama Maryam
Ummi bari na shiga na nema mana iznin shiga da kayan mu .
To Yakaka .
taku ta fara yi tana jin yadda zuciyarta ke bugu da fargabar da ta rasa takamaimai dalilin samuwarta daga ƙasan ran ta ,
ta kawo kusa da ƙofar gidan aka buɗo Babbar ƙofar ya danno hancin motar sa yana ƙoƙarin fitowa ... !!!!
Assalamu Alaikum wa Rahamatullah ta'aala wa barkatuhu .
Yan uwa masu karatu Maza da Mata, ina mika sakon gaisuwa ta tare da fatan Alkhairi a gareku.
Sannan ina mika godiya ta ga dukkanin daukacin Mutanen da suka samu damar kirana a waya da wadanda suka bar sakonni su na gaisuwa tare da addu'o'in samun waraka ga 'ya'ya na, har ma da wadanda Allah bai basu dama ba, kalmar nagode ai tayi kadan wajen bayyana muku jin dadina , sai dai nace Alherin Allah ya isar muku a duk inda ku ka yi bigire .
  Â
Ehen Uhum uhun-hun
Kai daga jin wannan guntattakin sautukan da suke tasowa daga kasan maƙoshi ka san da su nake, o'e da o'e ko kuwa dai a takaice na ce ghost r-r-readers 😂
Ba kome , Ba kuma zance kome ba , amma ku saurari haɗuwar ku da ɗanliti , Ah to meye ? Ai shine zai rama min irin cin tuwo a ƙoƙon da kuke min 😢.
A cigaba, eh nace a cigaba da labewa a bayan labule . 😂 😂
Nagode .
 Â
MAFARI
( Hargitsin Rayuwa )
Umm'muaz
35
Doctor hamza ba tare da ya dubi sashin da Yakaka take tsaye ba yayi wucewar sa yana waya da 蓷aya daga cikin abokan aikin sa na nan Asibitin Maiduguri wanda ya masa 茩iran gaugawa sakamakon neman sa da ake a asibitin jahar saboda wani aiki na gaugawa da za'a yiwa wata mata da take halin bu茩atar taimako ,
Kan ta a 茩asa tana satar kallon gefen fuskar sa , zuciyar ta cike taf da addu'o'i iri-iri , ta wuce ta 茩arasa wajen maigadi wanda ya tattara dukkanin hankalin sa akan ta ,
Sama-sama ya amsa gaisuwar ta ya è“·ora da tambayar ta wajen wa ta zo ?
Wajen Rahima na zo .
tace da shi tana fatan kar ya hana ta shiga gidan saboda wannan maigadin ba茩on fuska ne ba wanda ta sani a da ba neè½