Sashe 91
Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
  Nurse ɗin ta dawo tare da Baby wacce ɗumin tsaftatatcen ruwan da aka cika mata ciki da shi ya sa ta fara bacci ,"
  Miƙa masa ita aka yi ya karɓe ta , bai ce ƙala ba ya jiyo ya fito daga ɗakin ,"
  Wajen da ya bar Amne da Falmata nan ya dawo
  Mu tafi gida yace da su ,!
Ita Yakaka ta koma gida ne ? Meyasa ta tafi ta bar baby wanne irin shirme ne wannan ?
   cewar Amne ,
 Yaya dakta Ina yakaka ɗin ? Bata da lafiya ne ?
  Shiru yayi bai amsa musu ba , ya tsinci kan sa cikin ruɗani ,
 Â
Kai tsaye gidan Amne ya nufa da su , Amne riƙe da jaririya tare da Falmata suna baya a zaune shi kuma yana jaan motar ,"
  Takamaimai bai san tunanin me yake ba , abu ɗaya ne yake fata , shine ya je gida ya tadda ta tara da Rahima sun koma gida , wani tsoro-tsoron tabbatuwar bata gidan ya sa shi kin ɗaga waya ya ƙira rahima yafi so yaje gidan da kan sa ,"
 Ku shiga gida Amne zan je na duba ta wataƙila sun koma gida ita da Rahima , ya furta hakan ba tare da ya bari sun haɗa ido da Amne ba wacce take kallon sa
  Wai me su likitocin suka ce maka ne ? Cewa suka yi sun tafi gida ita da rahima ?
   Waigowa yayi ya dube ta , da hannun ya nuna mata Falmata tare da yi mata Alamun roƙon tayi shiru ta bar maganar tukun , " duba da yadda a halin yanzu ma Falmatan duk a hargitse take tunda suka hau motar bata ce uffan ba sai faman share ƙwalla take tana jaan hanci ,"
 Fita yayi ya buɗe mata kofar motar ,
 Amne bata sake magana ba ta kamo hannun Falmata suka fito tare da jaririyar zuwa cikin gidan ta ,"
Komawa yayi cikin motar ya zauna ya É—ora hannuwan sa bisa kan Steering motar yayi shiru , zuciyar sa na kai kawo ,"
  Ƙwanƙwasa gilashin motar da aka yi shi yasa shi ɗago kan sa ya sauke akan matashiyar yarinyar da ke tsaye a jikin motar sa ,"
  Murmushi tayi masa ya ga lokacin da bakin ta ya motsa alamun gaisuwa ,"
  Gyaɗa kai yayi kafin ya juyar da kansa ya fara ƙokarin tashin motar ,"
 Zaton sa irin ƴan matan unguwar ne take gaishe sa ,"
 Ƙara ƙwanƙwasa motar tayi da ɗan ƙarfin ta , tana masa magana ,"
 Tsaki ya jaa mai sauti kafin ya sauke gilashin motar ,"
 Â
  Kalaman ta suka doki kunnuwan sa da yasa ba shiri ya zuro kafafun sa wajen motar gami da miƙewa tsaye ,"
  Me kika ce ?
  Ɗan matsawa tayi baya kaɗan tana wani guntun murmushi tace
  Yakaka ce ta aiko ni , tace na sanar da kai ita ta tafi Abuja wajen Baban Ƴar da ta haifa domin a ɗaura musu aure , dan haka kar ma ka sha wahalar neman ta bayan auren su nan da watanni kaɗan idan sun gama moneehmoon zata dawo kuma tace wai......
   Marin da ya kwashe ta da shi ya hana ta ƙasara zancen ta ,sai da tayi taga-taga ta sunkuya , tana ɗagowa ya sake ƙara mata wani ,"
   Shoƙo gelen wuyan ta yayi ya maƙure ta , "
  Ina kuka kai ta ? Ke da su waye kuka haɗa baki kuka sace ta ? Zaki nuna min inda take ko sai na sada ki da jami'an ƴan sanda sun lallasa ki ,"
  Idanun YAGANA sun fiirfito tace wallahi gaskiya nake faɗa , yakaka ƴar uwa ta ce tare muka zo garin nan , tun a sansani muke tare , cikin shege tayi madam ɗin da muke yiwa aiki ta kore ta , shine yanzu bayan ta haihu suka haɗa baki ita da uwarɗakin ta ta gudu zata koma wajen shi suyi aure ,"
  Angaje ta baya yayi ,"
 Ƙarya kike yi ,"ƙarya ne noorie ƙaramar yarinya ce bata isa shirya wannan wasan ba , ban yadda da ke ba , dole zaki faɗi gaskiya idan kika ji duka a wajen hukuma , wayar sa yake ƙoƙarin zarowa lokacin da ya ji tace ,"
  Idan ƙarya nake bari na ƙira uwarɗakin nata ka ji muryar yakakar ma wallahi ,"
  Bata saurari amsar da zai bayar ba ta danna ƙiran number samy baby bayan ta saka wayar a hands free , wacce daman jiran ƙiran yagana take , "
  Dan haka ta rage gudun motar tare da gangarawa gefen hanya tayi parking sannan ta ɗauki wayar ,
  Hello Doctor tace da shi , bata jira amsa sa ba ta juya harshe zuwa turanci ,"inda take cewa
  Nasan zaka yi mamakin yadda abubuwa suka faru , wanda a zahiri ba wani abu bane na ban mamaki duba da yadda idanun ka suka makance basirar ka ta toshe , zuciyar ka kuma ta mace akan son yarinya yakaka , ita ma haka tata zuciyar ta mace , ta samu toshewar basira tare da makancewa cikin son wanda zuciyar ta ta zaɓa har ma ta daɗe da mallaka masa ruhi tare da gangar jikin ta baki ɗaya , " ba wani bane wannan illah uban ƴar ta wanda soyayya ta sa ta bashi kan ta , har kuma ta zaɓi rabuwa da ƴar ta tare da ƙanwar ta saboda ta tsira da shi , kana mamaki ko ? Ko kuwa zato kake ƙarya ne ," tunanin ka shiri ne koh ? To bari ka ji kasan daman waƙa a bakin mai ita yafi daɗin sauraro ,"
Juya harshe tayi ta dawo hausa ,
Yaks ,
Yaks ,
  Ke yaks
  A hankali ta ɗago kan ta da yake bala'in sara mata ta kalle ta da idanun ta da suke cike taf da hawayen tausayin kai ," duk da daman tana jin ta tana waya da turancin da ba fahimtar sa take ba , ba bacci take ba ,
  Na'am anty samy ,"
Ga Yariman naki ko kuwa me ma kike ƙiran masoyin naki ??
  Cikin sanyin muryar tace Bature kam silum ?
 Eh shine akan wayar riƙe kuyi magana ,"
  Anty samy kice masa kawai ina zuwa zan zo wajen sa zaki kawo ni , bana jin yin dogon magana , zuciya ta ciwo take min ban san a wanne hali Falmata take ciki ba ,"
   Cije baki samy baby tayi tana hararar yakaka da ta lura tana son ɓata mata shiri ,"
  Bana son kinibibi bake kika yadda zaki wajen nasa ba ko na mayar ki ne ?
  Shiru tayi bata ce e ba ko a ah
 Karɓi wayar ki masa magana ya ji ki ,"
  Alo Bature kam silum , gani nan zan zo wajen ka , anty samy zata kawo ni , amma gobe nake so mu dawo mu ɗauki su Falmata da mama , sai muyi aure mu zauna tare da su Dan Allah bazan iya zama babu su ba ina son ku ku duka sosai ka yadda koh ?
   Ƙarɓe kan wayar samy baby tayi tana murmushin nasara , ta koma turanci
  Sauran ƙarin bayanin da zai iya gamsar da kai yana cikin kayan ta tare da wayar ta da ta bari a gidan ku , da fatan zaka rungumi haƙuri , ka nemo matar da zata iya mallaka maka ruhin ta tare da sadauƙarwa irin wanda yakaka tayi ga masoyin ta ," idan kunne yaji .... ? Tace da shi tana sauke wayar a kunnen ta tare da latse ta ta kashe ta tada motar tana fincikar ta da ƙarfi ..
  Tun kafin ta gama furto zantukan ta yake jin wani abu mai kama da hayaki yana lullube masa zuciya wani irin ƙaƙƙarfan kishi da tsanar yarinyar suka tarwatsa masa rai da ya sa jin kan sa na juyawa , tabbas ta yaudare shi , yaudara mai girma , ta ha'ince shi ta kuma butulce masa ,"
Amma anya , toh Anya gaskiya ne anya ba tursasa noorie aka yi ba ,! Anya tana da wayo tare da hikimar yin mummunar yaudara irin haka , sashin zuciyar sa da soƴayyar ta tayi ƙarfi ta kafa rassa ke son kawo uziri ke son bata kariya ke son wanke ta , ke son fidda zargi a tsakani ,
Bai bi ta kan yagana ba ya faɗa cikin motar sa ya jaa da ƙarfi gami da nufar gida domin ganin shidar da aka ce akwai ,
Gyara gelen ta tayi wanda ya cukurkuÉ—e , kafin ta ce
  Wannan Banzan har mari na yayi akan wata banzar sokuwar yakaka , oho dai a yau zan yi kwanan farin ciki sanin cewa yakaka tayi nisa da garin maiduguri baki ɗaya , " babu ranar dawowa !
 Kai kuma marin nan wallahi bashi ka ɗauka , zan rama shi ta wata hanyar da baka yi zato ba a kuma lokacin da baka yi tsammani ba ,
  Wucewa tayi ta kutsa cikin unguwar da daman take ta su , tana hararar gidan Amnee inda take da tabbacin ciki jinin Yakaka suka yi bigire ,"
  Cikin ran ta ta fara saƙa da mummunar zaren da zai iya zargewa har da ita ,"
 Â
 Kusan da gudu-gudu ya shiga sashin su Rahima bai ko tsaya rufe ƙofar motar sa ba ,"
  Rahima , Rahima , Rahima yake ƙwalawa ƙira ,
 Da gudu ta fito daga ɗakin ta tana ƙoƙarin ɗaura ɗankwalin ta ta shirya tsaf domin zuwa asibitin wajen su Yakaka , jin shirun yayi yawa tun hantsi har ga shi ƙarfe uku ta ƙarato.ta tabbatar zuwa yanzu ta haihu ,"