Sashe 202
Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
 " Hakane , to amma tun da daman nan da ƙasa da sati huɗu ya rage bikin ita Rahima ƙarama kuma a halin yanzu ita da Zainab ɗin duk basa ƙasar suna can Dubai ko da an sanar da su dawowar ƴan uwan nasu sai a bar batun haɗuwar su har zuwa nan da sati biyu da duk zasu hallaru domin bikin Rahima .
  " to shikenan Baa Alaji bari yanzu zan ƙira idan mun koma ciki idan ma ya kama a haɗa su a waya su fara gaisawa ,
  " to babu laifi , ya zarce da cigaba da cewa,
   " Rahima baku da wata damuwa ko ? Da sauri Khaalty Rahima ta amsa ,
 " babu damuwar kome Yaya , Allah ya saka da Alheri ya ƙara nisan kwana .
 Amin yace yana Gyaɗa kai ya mayar da ganin sa kan su Yakaka ,
   " Yarana kuma babu wacce take da wata matsala ko ,? Idan kuna da ita ku sanar da ni , ni tamkar Mahaifi nake a wajen ku Mahaifiyar ku ƙanwata ce ,
  Girgiza kai Yakaka tayi , a hankali tace "Baa babu matsalar kome mun gode , Falmata wacce kan ta yake sunkuye ta ɗago kai kamar zata yi magana sai kuma tayi shiru tana sake sunkui da kai ,
  Prof da duk yake kallon su yace ,
 "Fatima akwai matsala ko ? Meye kike son ki faɗa min , ina jinki ƙaramar 'yata ?
 Dukkanin su sai suka mayar da ganin su kan Falmata wacce kan ta ke sunkuye ,
 'Baa so nake Dan Allah ka raba auren mu , bana son cigaba da zama da shi ko kaɗan Dan Allah Baa ka sa ya sake ni .
  Muryar Falmata ta ratsa wajen cikin alamun da take gaf da fashewa da kuka ,
Shiru ne ya ratsa falon , tamkar ruwa ya cinye su , kafin Prof yayi gyaran murya yana karantar yanayin ta yace ,
  "Fatima shi mijin naki laifi ya yi miki ? Ko kuwa wani abu aka miki daga danginsa ? Ko kun samu saɓani ne da shi ?
 Shiru tayi bata amsa ba , sake maimaita mata tambayar yayi nan ma tayi shiru , Khaalty Rahima zata yi magana ya dakatar da ita ,
  Ya sake cewa
  "ko kuwa kawai daina son shi kika yi ? Ko gajiya da zaman ku tare kika yi ? Ko kuma can ƙasar tasu ce bakya so ?
 Da sauri ta gyaɗa kai ,
murmushi mai sauti yayi , cike da tausasawa yace " to babu laifi , ki ƙira shi kice na ce ya zo ina son ganin shi , idan ya zo sai a yi miki yadda kike so kin ji ko ?
" to Baa nagode .
Murmushi yayi bai ce ƙala ba .
   ****
Niamey Police nationale
Maimounatou wacce take zaune daga kan wani ɗan dandamali da aka tanada shi musamman domin zaman waɗanda ake tuhuma da laifi a cikin babban ofishin 'yan Sanda na ƙasar Niger baki ɗaya .
Ta muskuɗa tana cigaba da wasa da awarwaron hannun ta , tayi kunnen uwar shegu da duk wasu manya da ƙananun tambayoyin da babban ɗan Sanda da yake tsaye daga kan ta yana jefo ma ta ,
Ganin taƙi yin magana ya sa ɗan Sandan ƙutawa cike da kaiwa maƙura a jin haushin ta , ya mayar da ganin sa kan Mammadou bayan ya ɗaga takun sa zuwa gaban sa ,
  " Mammadou ko za ka iya faɗa mana dalilin da yasa ku ka ciyar da ɗan ouwan ka guba ?
   Da sauri Mammadou ya ɗago da kansa ,
  " Wallahi ni bani da wata masani kan abunda yake faruwa a shiyar gidan Youssouf , matar sa ita tayi ƙira na kan cewa na zo fa ga ɗan ouwana ya faɗi yana biɗar taimako na , shine na runtuma da niyyar kai masa ɗauki , da shigata na tadda shi a halin da ku ma kun ka zo ku ka taddo shi , wallahi ni iyakar abunda na shina kenan ban.....
Wata dariyar mai sauti da Maimounatu ta sanya , ita ta katse masa jawabin sa ya mayar da ganin sa kan ta yana ƙif-ƙifta ido , ba tare da ta dube shi ba tace
  " Mammadou wallashi cikkin ragwaye kai na ƙurya ne , yo me kake tsoro idan ya tabbata gubar da shi wannan Azzalumin ya ci ta hannun ka ta fitto ? hukuncin kisa ta hanyar rataya ko kouwa ɗaurin rai da rai muddin rayuwa ?
   " Burina labarin mutuwar sa ta jishe ni , daga nan koume shi faru dai-dai ne , ai hukuncin wadda ya kashe a kar shi , shi da kansa bisa turba nasa hukuncin yake , fansar ran Ghaddafi tare da gudan jina na da na rasa na ɗauka bissa kan sa , kai gudumawa ka bada bisa turbar naka cikar buri ko kouwa ?
   Laɓɓan bakin Mammadou har rawa suke cikin in'ina yace ,
  " kadda ki mini ɓakin sharri ɗiyar nan , ni yaushe na kawo miki gubar da kika ciyar da ɗan ouwa na da itta ? Ki yiwa Allah kadda ki tunkuɗa ni cikin masifa ,
  Wani kallon banza Maimounatou ta wurga masa , idanun ta jajir tace .
  " Yau ba rana ce ta yin wassan ƴar boye ba Mammadou ka daina yin kamar baka san kome ba , kamar kai da Mahaifiyar ka baku taya ni ba , bana son muyi rabuwar tsiya doumin kun bani taimako wajen biya hakkin Ghaddafi tukuici ya kamata na baku .
  Ɗan sanda da yake rubuta duk wasu kalamai da suke yi , ya ɗan karkato ga Maimounatou , ganin kamar ta shirya bada wasu bayanai ,
 Â
  " Wanene Ghaddafi menene kouma alaƙar sa da kashe Mijin ki da kika yi ta hanyar ciyar da shi guba .
 " Ghaddafi masoyina ne .
****
Ghaddafi Yacouba Dango asalin iyayen sa ƴan ƙasar Mali ne da suka hauro sahara suka shigo ƙasar Niger , suka yada zango a yankin Agades , inda suka yi mazauni cikin wani kongon gida da yake daga baya sosai da Babban gidan sarkin Agades ( fadar Maimartaba sarkin Agades ) .
Bayan shi iyayensa suna da wasu 'ya'yan sai dai tsantsar talauci ya sanya su fantsama a cikin gari yin barace-barace , duk kuwa da cewa a lokacin shi Ghaddafi saurayi ne mai kimanin shekaru ashirin da É—oriya ,
Lokacin da ya fara bara sai ya fahimci babu mai kula shi bare har a ba shi , dayawa daga cikin mutanen da yake roƙo ma ƙorar sa suke da zagi kowa na faɗin ya tafi ya nemi sana'a .
Ganin haka ya sanya shi daina bara ya koma tsince-tsincen matattun ƙarafuna a kan bola yana kaiwa yana sayarwa ,( jari bola ) babu laifi yana tallafawa iyayen sa da hakan .
a wannan yawon ya haɗu da wasu kangararrun yara sa'o'in sa da suke jeruwa bisa tsohon hanyar wucewar jirgin ƙasa wajen da aka mayar sa bola su kuma suka mayar da shi matattarar ƙananun shaye-shayen su da yin karta .
Su suka jawo sa cikin su ba ɗau lokaci ba ya zama ɗaya daga cikin su ya kangare , tsince-tsincen ƙarafunan ma ya daina , basu da wani aikin yi sai zaman banza a bakin layin jirgi ko kan katagun kwangayen gidaje , suna ƴan shaye-shayen su , babbar sana'ar su ita ce ƙananun sace-sace , daga sun ga gidan da ake barin sa galala sai su faɗa su yashe mutanen cikin sa , ƴan ƙananun dabbobin mutanen unguwa basu tsira ba , akuyoyi ,talo-talo kaji , agwagi , a taƙaice dai su Ghaddafi sun addabi mutane sun hana su sakewa .
Â
Ganin haka yasa Mutane suka yi ɗango suka kai ƙarar su wajen Maimartaba ,
Da kansa Maimartaba ya sa aka kamo su , aka basu horo tare da haÉ—a su da aiyuka a cikin gidan sarkin mai wahalarwa na tsawon satika biyu duk saboda a hora suÂ
Ghaddafi yana cikin samari huÉ—un da aka tura bargar dawakai domin kula da su da share musu waje gami da basu abinci .
Kafin kwanaki huɗu Ghaddafi ya saba da aikin yana kuma jin daɗin aikin saboda ko babu kome yana ci ya ƙoshi fiye da sau uku a rana
Ranar da yake cika sati a kan aikin sa , Babban bawan da ainahin kula da bargar yake ƙarƙashin sa , ya danƙa masa linzamin wani kyakkyawan matashin jan doki ,
Yace ya kaÉ—e jikin sa da kyau dokin gimbiya ne , yau zata É—an hau ta kewa akan sa nan cikin filin dake gaban bargar .
Zuwa la'asar sakaliya , gimbiya Maimounatou tare da bayunta biyu suka iso
Ba ɓata lokaci ya jaa limzamin dokin zuwa gaban ta yana mai tsare ta da kallo ganin ta da yayi yarinya ƙarama da bata wuce sa'ar ƙanwar sa ta uku ba ,
Gimbiya Maimounatou tana ɗago kai ta sauke ganin ta a kan sa , zuciyar ta ta wani irin bugawa , a iyakar shekarun ta goma sha shidda alokacin bata taɓa ganin wani ɗa Namiji mai kyaun sura irin sa ba , kasancewar Ghaddafi kyakkyawan balarabe ne na sosai jazur da shi .
Tun daga wannan lokacin sai ta faɗa jarabar ƙaunar sa , bata da aiki sai zuwa barga dan kawai ta kalle shi , a lokacin ita tana hutun kammala makarantar ta ta secondry ,
Sai dai kamar ɗaukewar ruwan sama sai ta rabu da sake ganin sa bayan wasu ƴan kwanaki , duk yadda ta so ta daure ta manta da shi , ta gagara a hankali damuwar rashin cigaba da ganin sa ta fara duƙushe walwalar ta , saboda wannan ne karo na farko da zuciyar ta ta fara son wani ɗa namiji ,