Sashe 162
Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Fatima mu tafi muyi sallar isha'i kiyi kwana (bacci ) dare yayi ,"
A sanyaye ta amsa da "To,
Har suka kwanta bacci babu wanda ya kuma magana kowanne a tsakanin su yana tunani,
Wayar sa ce tayi ƙara alamar shigowar ƙira , da azama ya ɗauka ganin wacce ke ƙiransa ya sanya shi miƙewa a hankali ya nufi ƙofar ɗakin , ya zo fita ya juya gami da kai kallon sa kanta da tayi lamo cikin bargo kamar mai bacci ,
ajiyar zuciya ya sauƙe ransa cike da tunaninnika barkatai ya fita gami da jaa musu ƙofar ,
Falmata wacce duk motsinsa a kunnen ta , ta miÆ™e zaune gami da yaye bargon , cikin ranta sam babu daÉ—i gani take kamar ta É“ata masa rai da maganganun ta tunda gashi daga lokacin bai sake cewa da ita kome ba , ko fushi yayi ?Â
Tashin muryar sa da yake magana kamar a gabanta "kasantuwar ta mai buɗaɗɗen kunne " ya sa ta saurarawa zagayayyar fuskarta na bayyana wani yanayi irin na wanda aka shammata lokacin da taji yana cewa ,
"bonjour ma princesse comment allez-vous aujourd'hui mon amour? ( Alo gimbiyata yaya kike yau masoyiya ? )
Cigaba yayi da cewa
"Je vais très bien et tu me manques aussi , ( ina lafiya lau nima nayi ƙewar ki )
 Ƴar dariyar nishaɗi yayi , kana ya cigaba da cewa ,
" wannan kalma ke kin ka faÉ—e ta , ni kouwa gurina ba haka ne ba , duk wani bigeren da babu ke cikin sa wajena daÉ—in sa ragagge ne , babu kome anan sai matsanancin sanyi tafe da tarin nawi da wahalwalu bisa kaina ,
 Murmushi yayi mai sauti ,
" a gida nake Yarima , ga gurin aikina kuma Mai muƙamin Major , nan kuwa ai ban wucce matsayin bawa dake hidima ga wassu rayukan ba ,
Gicciyewa yayi ya kishingiÉ—a yana me cigaba da sauraron ta ,
" ba domin yanayi da bashi yiwuwa na taho da ke ba, kin sani ban iya tafiya ga nissan duniya batare da ke gefena ba maimounatu ke ai sashi ce daga jikina ,
Falmata da take sauraran sa , sai ta koma ta kwanta tare da lulluɓuwa ta cure jikinta guri ɗaya ga barin sauraran zantukan sa , zuciyarta ke wani irin bugu da yake tafe da zallar tashin hankali ,
 Sunan wacce aka ƙira da Maimounatu tare da irin Kalmomi masu daraja da aka mallaka mata , sun gaftare tare da ruguza duk wani ɗan guntun tunanin banza da ta fara yi ,"Ah to na banza mana , tunda 'yar kulawar da yake bata ya sa ta hasashen hawa wani matsayi da bata kai shi ba a wajen sa ashe ita ɗin ba kome bace face tarin nawi da wahalhalu .
Hawaye masu É—umi suka gangaro daga idanunta suna É—iga bisa hular sanyin kan Mama .
Maiduguri Nigeria
Tun ranar da Doctor Hamza ya gargaÉ—i Yakaka akan kada ya sake ganin fuskarta bata sake bari sun haÉ—u ba ,
Ko muryar sa ta ji yayi Sallama da shi bai cika shigowa ma sashin nasu ba , da sauri zata nemi gurin ɓuya , duk cewa tun daga ranar duk lokacin da ya buƙaci abinci daga Rahima ita take girka masa , sai ita kuma Rahima ta kai masa .
Yau Asabar ya shigo gidan da safe misalin ƙarfe tara shirye yake tsaf cikin shirin sa na zuwa ɗaurin auren ƙanin Abokin sa .
Yana yin Sallama , Yakaka da take goge Falon bayan ta gama sharewa tayi saurin ajiye moper ( mofi ) ta tsallaka da ɗan gudu ta shige ɗaki ta rufo ƙofar ,
Hajja da take zaune a gefe tana karin kumallo ta harari bayanta ta wutsiyar ido kafin ta taɓe baki ,
" Ni hauwa'u naga abunda yafi ƙarfi na , ke kenan kullum a tsalle-tsalle da guje-guje ? Uwa wata tunkiyar da take rawar turke ? Allah ya kyauta .
Washe baki tayi tana dariya ,lokacin da Doctor Hamza ya shigo
" a ah kaga manya ɗiban farko , Babban likita ,
Fuskar sa É—auke da murmushi suka gaisa , ba tare da ya zauna ba yace
 "Hajja ina Rahima ?
 " Yanzu ta hau sama , a ƙira ta ne ?
" a ah yi zaman ki Hajja idan dai ta fito ace ta min girki kafin dawowata ta kai min É—akina .
" To babu laifi zan faÉ—a mata .
 " Nagode Hajja .
Ya juyawa da nufin fita idanun sa suka sauƙa kan Hoton Mama da tun ranar da ya fara ganin hoton yake son tambayar Rahima 'yar waye ? Ƙwarai hoton yarinyar yake fusgar hankalin sa ,
Dan haka ya dawo da baya yana tambayar Hajja ,
" Hajja wannan 'yar waye haka aka samu kyakkyawa ?
Da dariya Hajja ta amsa masa
" 'yar wajen Fatima ce , Mama sunan ta ai sun ma yi tafiya ne can Amurka ita da iyayen nata .
"Fatima ?
Ya maimaita ,
" wacce Fatima Hajja ?Â
" Ƙanwar wannan yarinyar Yakaka take ko wa ?
 'okay ,
Ya amsa yana barin wajen ba domin ya gane wacce ake nufi ba kai tsaye sai dan ƙiran sunan Yakaka da Hajja tayi .
ƙarfe biyu na rana suka shirya tafiya gidan Amne su Uku Rahima , Yakaka da kuma Hajja da itama tace zata je .
Shatar shatar adai-daita Rahima ta ɗaukar musu wanda ya tokare daga bakin hanya yaƙi gangarawa kwarin unguwar a cewar sa gargadar cikin unguwar zai ɓata masa mashin , dan haka dolen su suka sauƙa Rahima tana ta mitar wahalar tafiyar da zasu yi a ƙafa kafin isar su gidan .
Da wani tasowar sabon yanayi a zuciyar Yakaka take bin unguwar da kallo , unguwar da ta zama tushe na hargitswar rayuwar ta da bata tsinci kome a ciki ba illa wahalhalu da tarin abubuwan ƙi , unguwar da suka sha gwagwarmaya a cikin ta ita da ƙanwar ta da ƙawarta Yagana ko ina yagana take a halin yanzu ? Wataƙila ita rayuwa tayi mata kyau , tayi aure ta fara ginin rayuwar 'ya'yan ta .
tunaninta ya katse lokacin da Rahima ke cewa su gangara ,
Tana bin layin tana tuno da haÉ—uwar su da Doctor Hamza a bakin layin ana ruwan sama ,taimakon da yayi mata a ranar da ba domin shi ba da ta faÉ—a babbar kwatar taji mummunan ciwo ko ma ta rasa ranta ,
"Allah sarki yaya dakta ,
Ta furta hakan daga ƙasan ranta lokacin da suke miƙawa cikin layin .
Daga nesa ta fara jiyo hargowar sa muryar sa a sama yana rantse-rantse , domin ta tabbatar da shi É—in ne ? Tayi saurin É—aga idonta ta É—ora a kan sa shi da wata matar da kallo guda tayi mata ta gane yanayinta na matan banza ,
Da sauri ta É—auke kai tana É—an jawo hijabinta gaba kaÉ—an , zuciyarta cike da fatan Allah ya rufe masa ido ya wuce bai ganta ba bare ya gane ta.
cikin rashin sa'a hasken da take da shi ya riga ya É—au hankalinsa kasancewar sa kawali idanun sa koyaushe akan wankakkiyar mace yake babu ruwansa da matsayinta na matar aure ko akasinta .
Sun ƙaraso gaf da juna ya jaa ya tsaya , kafin ya ɗau salatin da Hajja ta ƙarasar masa ,
Sauri yayi ya zagaya ta sashin ta ya dogare , yana kallon fuskar ta da taƙi yadda su haɗa ido ,
Dariya ya kwashe da ita yana tafa hannuwan sa alamun mamaki yace ,
"Ahayye nanaye ke duniya mai abun mamaki ? Yanzu duniya da gaskiya Yaks kÆ´a ga ÆŠanliti ki É—auke ido ki kawar da kai ? Lalle Yaks kin zama kaza ci ki goge bakin ki , Ko da yake ai kome kika yi ba mamaki tunda baki da shayin kowa .
Yakaka ta saci kallon Hajja wacce tayi saƙare tana bin Ɗanliti da kallon banza ,
" ÆŠan-ÆŠan liti ya kake ?
" Ras nake Yaks .
Yayi fari da ido kafin ya É—ora da
"Ke kuma fa ? Ya na ganki haka da Bargo yaro-yaro kina yawo kadda dai kice min kin yi ƙarkon kifi , ? Kin fito daga ruwa kin faɗa wuta ? Yo ai kuwa da kin ɗibga asara a duniyar nan Yaks ace dai wai mace hamshaƙiya kamar ke kina yawo a ƙuɗunɗune cikin hirami yake ko hijabi ko jallabiya ? Bani sunan sa ɗaya .
" Ubanka yake nace Ubanka yake shashasha , wofin wofiyo banzan banza , yau ga É—a ya zama lalatatce bayan an kashe ragon suna , to Allah ya shirye ka , ke un-un Yakaka wuce muje .
Hajja ta furta hakan tana huci tare da yiwa ɗanliti daƙuwa da hannuwanta duk biyu , ta ƙarasa zancen da fusgar hannun Yakaka ,
BuÉ—e baki ÆŠanliti yayi da mamaki ,
," Ke tsohuwa , ki kiyayeni ki kiyayen nace da zaki zo ki shiga cikin maganata dake nake ? Nace da ke nake ? Yo Allah na tuba ke a zamanin ki waye ya san irin tsiyar da kika shuka ta rawar banjo da kiɗan gurmi daga ke sai ɗan kanfai ? Ko da yake wannan baƙin naki uwa shuni ba wani tasiri kika yi ba ko a wajen su garbati mai kalangu . ,
",Na rantse kin ci darajar yaks domin ni na falle tsohuwa da marin da zai sa ta ga star abune mai sauƙi a wajena , gaba ki kiyaye kin ji na gaya miki .
tsaki Hajja tayi suna barin wajen ,
" Allah ya shirya ka zindiƙi .
Shima ya rama Hararar da tayi masa ,
" waye yake ta taki tsohuwar guzuma , Yaks Ki samu lokaci ki leƙo mu akwai labarai da hanyoyin arziki masu tarin yawa , af na manta na faɗa miki uwarɗakin fa bata da lafiya...
Bai ƙarasa zance ba yayi shiru ganin sunyi nisa ,
" ji min tsohuwar nan zata yaɓan magana wai nine zindiƙi ? Tsohon ki ne dai zindiƙi aikin banza .
****