Sashe 197
Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
gefe guda kuma yana jinjina Yakanah irin tata da bata taɓa furta masa kalmar so a gaban sa ba ko sau ɗaya , ta kuma yi ƙoƙarin dannewa ta ɓoye hatta ga shi kansa bata yadda cikin saninta ta nuna abunda ke binne cikin ranta ba , bare kuma ga ƙaunarta da yasan abadan baza ta taɓa bari ta fahimata , daga ƙasan ransa ya furta "Madallah da ƙarƙƙarfar kyakkyawar zuciyar da take iya danne tasirin So , ƙwarai ita ɗin ai jaruma ce . "
Ƙarfe uku na ranar ta yi masa a cikin Masarautar su inda ya tafi kai tsaye ga fada ya kai gaisuwa gurin Maimartaba wanda ya amsa masa fuskarsa ba yabo babu fallasa , sai dai saɓanin baya da idan har ya shigo fada ƙirarin da manyan fadawa da kansu ke yi masa har ya tashi , yau dai shiru babu wanda ya kambama shi da ƙirarin sai fa dogarai da suke tsaye daga bakin-fada .
Shiru yayi kansa a sunkui yana jiran Maimartaba yayi masa umarnin dawowa daga gefensa kusa kamar yadda ya saba a koyaushe , sai dai har ya kusan mintoci ishirin a zaune maimartaba bai sake duban sa ba , dan haka ya miƙe yana mai sallama da Maimartaba da sauran jama'a da suka amsa a sama-sama ,
Idanunsa suka kai inda yake mazauninsa ada kusa da ƙafafun Maimartaba , karaf suka haɗa ido da Mammadou da yake zaune a gurbin sa , wanda yake jifan sa da wani ɗan guntun murmushin ƙeta , ɗauke kansa yana ƙarasa barin Fadar .
A sanyaye ya taka yana yana nufar ciki sashin Hajiya Umma , a hanya babu abunda ya sauya na yadda bayu ke zubewa gaishe sa , sai dai yana lure da wani irin kallo da wasun su ke binsa da shi wasu kuma yana iya jiyo ƙus-ƙus ɗin su daga ya gota .
Ita ɗaya ya tarar da ita a falonta na ƙurya da yawanci sai zata yi ganawa ta sirri take shigarsa ,
Zama yayi a gabanta yana mai sunkui da kai cike da ladabin da yake halayyar sa ya gaishe ta , muryarta babu amo sosai ta amsa gaisuwar sa ,
Shiru ya É—an gitta kafin da murya mai kaushi tace da shi ,
  " Ina kouma itta ɗiyar da kake amren ?
Shiru yayi kaÉ—an kafin ya ce
   " sun tai ga ƙasar su baki ɗaya ,
Sake tsare shi da ido tayi , duk kuwa da ta ɗan yi farin-ciki da cewa da yayi "sun koma ƙasar su , sai ta ɗora da cewa " ka sau amren ta ko kuwa ?
  Shiru yayi cikin fargaba , yana tsoron kadda ta tilasta shi ya saki Fatima , wani sashi na zuciyar sa ya ji yana gargaɗin sa daga sake yin ƙarya ,
wani busasshen yawu ya haɗiye , ya ɗago da kansa ya dube ta , a hankali ya mayar da kansa ƙasa kafin yace ,
  "Ban sau amrenta ba sun tai gida ne kafin al'amura su dai-daita anan ,
"Youssouf ,
  Hajiya Umma ta ƙira sunan sa , a tsorace ya amsa "Na'am Umma , zuciyarsa tana mai tsananta bugu yauce rana ta farko a iyakacin sanin sa da ta taɓa ƙiran sunan sa kai tsaye .
 " na maka oumarni ka sau amren ɗiyar nan ka aika mata da shikan ta can zouwa ga ƙasar su , muddin kana ƙamnar da na yafe ma kouma Mahaifinka shi maka afouwa , idan kouwa ka ƙi bin umarni na Youssoufa , shiru tayi bata ƙarasa ba ,
  sai dai ya fahimcin munin abunda ka iya biyo baya ganin yadda É“acin rai ya Æ™ara hauhawa a kan fuskar ta bayan ta kawar da kai daga barin duban sa ,Â
 Gumi ne ya shiga keto masa kota'ina cikin jikin sa , ya sanya hannun sa yana share zufar goshinsa ,
  Muryarsa can ciki yace , " Na amshi oumarnin ki Umma, ki yafe min bissa ga kuskuren da na aikata .
Muryar ta da ɗan sassauci tace , " Laifin ka ga Allah kayi ka nemi Yafiyar sa , doumin shi mai yawan afouwa ne ga bayinsa , sannan ka kyautata tuban ka , ni kam abou ɗai nake so kayi shine sakin auren ɗiyar nan idan kayi hakka shikenan .
 Shiru yayi baice kome ba , saboda zallar tashin hankalin da yake ciki , duk wata ƙafa ta isar da saƙo a jikinsa jinya take da amsar umarnin Hajiya Umma .
 Ganin yadda ya zamto tamkar wanda aka zarewa lakka a gabanta yasa tayi gyaran murya tana mai ƙarfafa zuciyarta daga tausayi irin na tsakanin ɗa da mahaifiya daya soma mamayarta , musamman kasancewarsa mafi soyuwa a gareta cikin 'ya'ya ,
  " ka tashi ka tai ga matanka bayan ka tanadi kyawawan kalmomin da za ka yi amfani da su wajen tausasa zuciyar su doumin laifin ka mai nawi ne a wajen su .
Kamar jira yake tace ya tafi , sai ya miƙe a hankali bayan ya mata bankwana ya fito daga falon , baya sanin takamaimai ina yake jefa ƙafarsa ya nufi shiyar gidan sa ,
Sashin Siyama ya tasarwa ba tare da ya haƙiƙance meye zai je ya sanar da ita ba ,
Da shigar sa Yumna ta taso da gudunta daga inda take wasa a tsakiyar falon da tarin kayan wasanta ,
 Da sauri ya sunkuya ya ɗauke ta yana matse ta a cikin jikin sa kewar Mama marar adadi na taso masa ,
  "Papa ,
  ta ƙira shi da ƴar muryar ta ,
"Yumna , ya amsa yana ɗora idanunsa akan Siyama da ta miƙe tsaye daga kan kujerar da take kishingiɗe Rakiya na mata tausar ƙafafunta ,
Da sauri Rakiya ta miƙa gaisuwar ta kafin ta bar falon zuwa can waje sashin su na ma'aikata ,
A hankali Siyama ta tako gaban sa bayan ta ƙirkiro wani guntun murmushi akan furskar ta ,
"Sannu da zouwa Biyamuradi, da fatan ka iske mou lafiya ?
 Tana ƙarasowa ta kama hannun sa guda , kafin ta cigaba da cewa ,
  " Mu tai kayi wanka Baban Yumna kafin a samar da abinda zaka taɓa ,
Yanayin rashin kuzari bai bar shi ba ya bi bayanta zuwa sama É—akinsa ,
Bayan ya yi wanka ya shirya , cigaba yayi da zama akan kujerar ɗakin ya zurfafa cikin tunanin umarnin Hajiya umma , da kowacce daƙiƙa guda tashin hankalinsa daɗuwa yake , gefe guda ga rashin sanin takamaimai halin da ita kanta Fatima ke ciki tare da ɗiyansa dake maƙale a marar ta ,
  Ƙarar wayar sa ya sanya shi janye tagumin da yayi ya ɗau wayar ganin mai ƙiran nasa daya daga cikin manyan kwamandojin sojin su ne na yankin Diffa ,
Magana suka sake yi kan tsaron da zasu daɗa a tsakanin boda saboda motar da take ɗauke da matarsa da zasu bi ta Boda zuwa Nigeria , bayan ya gama wayar da bai ɗau lokaci yana yi ba ya ajiye wayar a gefe yana baya da kan shi ya ɗora kan bisa allon kujerar ya ɗora dogayen ƙafafunsa akan ɗan teburin gilashi da yake gaban sa ,
Idanun sa ya runtse yana jin yadda kansa ya ke sara masa musamman ta goshin sa ,
  Siyama wacce ta ji shirun sa yayi yawa bayan ga abinci ta haɗa masa a shiyar cin abincin su , sai ta miƙe ta hau saman , cikin ranta kuwa ƙoƙari take tayi aiki da shawarwarin da Rakiya ta bata na danne kishinta daga barin bayyana shi a sarari ,
Tana murɗa ƙofar ɗakin ta hango shi a kujerar ya dafe kan sa da hannunsa guda , wani irin yanayi na zallar tausayi da ake samu ga abunda ake ƙauna ta gaskiya , shine ya tsigar mata , babu shakka a tun shigowarsa ta fahimci tsananin tashin hankalin da yake ciki .
Bai ji shigowarta ba har zuwa zaman ta a gefen sa , sai da ya ji hannunta mai tsananin taushi ta É—ora akan nashi hannun da ya dafe goshinsa da shi ta janye shi ,
 "Baban Mama , ta ƙira sa , ɗas ! Zuciyarsa ta buga da jin sunan Mama da ta masa inkiya da shi da Falmata kaɗai ke ƙiransa da sunan , sai ya dawo da ganin sa kanta ,bayan ya gyara zamansa yana jin wani irin yanayi mai tasari matuƙa ,
  "Baban Mama ina miƙa ta'aziyyata kan rashin da muka yi na ɗiyar mou , Allah shi jikan Mama shi sa ta ceto mou .
Sai tayi shiru tana neman dai-daita nutsuwar zuciyar ta daga tarin baƙin-cikin da yake bijiro mata na zallar kishin Falmata , ta ɗora da cewa ,
  " Ina ƙamnata Fatima ? Da fatan ka baro ta lahia ?
Da wani irin yanayi ya matse hannunta dake cikin nasa , cikin muryar dake cike da rauni yace
  " nagoude sai dai a halin yanzou Fatima ta gudou ta barni zuwa kan hanya mai matuƙar haɗari , Hajiya Umma kuma ta min oumarni na sau amren Fatima , ki min addu'a Siyama lamura agareni sun tsaurara , kowa ba shi fahimta ta bisa jarabawa ta rayuwa .
Ƙwalla ta ji sun tara mata a ido , tunda take bata taɓa ganin Biyamuradi cikin halin ɗimuwa tare da rauni makamancin haka ba , sai fa yau ta dalilin ɗiya Mace , babu shakka wagga ɗiya Fatima ta kai ayi gangamin tafiya kallon ta .
Gagara cewa kome tayi illa kanta da ta kwantar bisa ɓarin jikinsa , cikin tausayin kai tace , " kayi haƙouri da ikon Allah lamura zasu dai-daita maka a tsakanin hakka nayi Alƙawarin taya ka da addu'a , Allah shi dawo maka da Fatima-zahra .
Hannunsa duk biyu ya sa yana rungumeta tsam a jikin sa , ransa cike taf da ƙauna ta musamman gami da ƙarin ganin ƙimar ta a idanunsa , babu shakka shi masoyi na gaskiya abun riƙo da hannu biyu ne .