Sashe 34
Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Direban sa yayi niyyar kira amma sai youssouf ɗin ya dakatar da shi tare da faɗa masa shi yana bukatar sirri ne dan haka so yake su tafi su biyu kawai ', a cikin ran sa yana ƙudurtawa zai sanya ido sosai ya gane hanyar domin duk lokacin da ya bukata kawai ya tafi shi ɗaya ya shaa abar sa ba tare da rakiyar kowa ba , ba kuma tare da kowa ya sani ba. ( mai kowa me kome ya sani kuma yana ganin ka youssouf amm )
Haka suka kama hanya tare nuhu shi ke jaan motar suka keto titi tare da bullowa ta bayan kasuwa suka gangara zuwa cikin unguwar BULABURIN wacce kaf cikin garin anan kaÉ—ai ake iya samun giyar gargajiya gangariya Æ´ar asali ,"
Suna yin fakin a harabar wurin da ya cika ya tumbatsa da mutane zuwa ababen hawan su sakamakon yamma da tayi ," kiÉ—a yana tashi ta cikin manyan sifikokin da suke a kusurwa huÉ—u na zagayen filin ,ga matan banza da shigar fitsara burjik suna kai kawo cikin sigar tafiyar tallata baiwar jikin su , kowacce taci bilicin tare da izgar doki a tume a kan ta yayi tozo kamar na tsohon rakumi ,"
Juyowa nuhu yayi tare da kallon youssouf da ya lura yana ƙarewa matan wurin kallo , cikin yanayin da shi nuhu bai kai ga fahimta ba ,"amma sai ya fassara kallon da na tsantsar zalama da nuna muradi ,"
Abokina duba waÉ—annan ba irin naka bane waÉ—annan duk ajawos ne na kananan yara ," daina ma kallon su irin naka suna daga ciki a adane ba kowa ke hayar su ba sai ire-iren mu manyan yara ,"
Yana kammala faÉ—in hakan bai jira cewar youssouf É—in ba ya balle murfin motar gami da fita ,
Kutsa nan bulla ta chan suka bullo ainahin wurin da ake sayar da burkutun da mashayan ta suka tabbatar da tafi ta ko'ina inganci a cikin da'irar wajen watau ( burkutun madam saly )
Suna doso wurin youssouf ya shaƙi ƙaƙƙarfan warin burkutun ya lumshe idanu yana sake jin nutsuwa tare da matsuwar ya ji ya kwankwaɗa , dan haka ya sake sauri ,inda suka tadda mutane akan kujeru gaban tebura ,
Ɗaya daga cikin ƴan matan wajen da suke da alhakin rabawar ga masu saya wacce take raƙube a gefe ita ce ta zaburo ta nufo wurin su ,'
Tun da ta nufo su nuhu yake mata kallon sheƙeƙe , saboda sam ba ita yayi zato ba , ba kuma ita ya so gani ba ," budurwar sa ko kuwa ace farkar sa samy baby , yarinyar da take tashe a da'irar ta su ita yake son ganin kamar yadda ta saba taryar sa kaf ƴan matan wurin sun san shi kwastoman samy baby ne ,
saɓanin ta sai yaga wata yagwalgwalalliyar ƴar yarinya tana tahowa gare su hasalima shi tun da yake zuwa rumfar madam saly bai taɓa ganin wannan ƴar ƙwailar ba ,"
Da zuwan yakaka wurin ta É—an rage tsawo tare da tambayar su kofi nawa zata kawo musu ," É—auke kai nuhu yayi yana wani hura hanci domin shi gaba É—aya ma ransa ya gama baci ,"
Biyamuradi youssouf da yayi baya da jikin sa akan kujera tare da yin ƙasa-ƙasa da idon sa tamkar dai yana gudun wani ya gan shi a wurin ",alhalin nan kuwa shauƙin burkutun ne ke kwasar sa da kamshin ta suka haɗu suka samar mishi da mutuwar jiki ," shine ya amsa mata cikin hausar shi ta bamarɗe ,"
 " Ki ɓido min mai auki kawai "
Kasaƙe yayaka tayi a tsaye cikin rashin fahimtar abun da ya faɗi ," hasalima hausar da ake yi cikin maiduguri ma da bata da nisa ba gane ta take yi sosai ba bare fa wannan gangariyar hausar sam bata tsinci koh kalma guda ba ,"
Sake rusunawa tayi tana me sake maimaita tambayar da tayi masu cikin gurbatatciyar hausar ta ,"
 Wannan karon nuhu ne ya amsa mata a fusace ,'ke dallah cewa aka yi ki kawo dayawa ,"
Sum-sum yakaka ta juya da nufin zuwa ta kawo musu,
'conole youssouf ya bi takun kafafun ta da kallo yana saƙe ƙagauta,"
" dai-dai tahowar samy baby wacce shigowar ta kenan wurin aka yi dace idanun ta suka sauka kan yakaka tana abun da ta ayyana shi a taɗi da gwarzon ta na wannnan wattanni "conole nuhu" wanda a yanzu kaf samarin ta babu kamar shi a kuɗi da shi take tinƙaho ,"
A take wutar kishi ta ruru a ƙarƙashin ran ta ," wata irin bangaza tayi wa kafaɗun yakaka tare da sanya tsinin dogon takalmin kafar ta , ta take mata kan yatsun ta biyu tare da tsayuwa akan yatsun kafar sannan cikin raɗa bayan ta kawo bakin ta kusa da kunnuwan yakakan wacce ta ɗimauce cikin jin azabar takun da samy baby tayi mata tace
," yarinya ki kiyaye wannan ɗan itacen marmari nane zan iya kashe wacce ta shiga gona ta har tayi gigin taɓa ɗan itaciya ta ,'
Duk tsayuwar samy baby akan ƙafar yakaka biyamuradi youssouf yana ankare da hakan saboda idanun sa da suke wurin daman ," ji yayi tausayin wacce aka takewa kafar ya ɗan kama shi wanda tun daga kan kafafun nasu ya fahimci banbancin da ke tsakanin su ,ganin kafar yakakan duk dadbare-dadbaren datti ,ga manyan tsagun faso da datti ya samu mazauni na dindin-din wanda idan aka kwatanta da kafar samy baby da take a wanke a goge sumul-sumul tashin farko za'a fahimci baiwa ce da uwargijiyar ta , dan haka yayi tunanin yakakan wani laifi tayi wa samy take hukuntata ," sai dai duk da haka yaji haushin samy saboda shi mutum ne wanda sam baya son zalinci ," take yaji ya tsane ta ,
ÆŠago idanun sa yayi ya sauke su akan fuskar samy baby wacce idanun ta da hankalin ta baki É—aya yake kan "É—an itaciyar ta nuhu "ðŸ˜
da sauri yakakan ta wuce lokacin da ta ji samy ta janye kafar ta tare da yin gaba ,"Â
Kichibis tayi da madam saly wacce ta sawo kai kallon ta sama da ƙasa madam.saly ta jefa mata,"
yanzu yaks dan ubanki ban baki kayayyaki nace ki daina yawo cikin waɗannan shegun tsunmokaran ba , ace tsawon sati kenan yau da kuka fara zuwa min nan amma shegu ƙazaman banza kullum da daƙalkalallun kaya ɗaya? Kalen ku dunga sa min kostomomi amai ? Kuna yawo yarkace yarkace uwa sabbin mahaukata ? A haka waye zai karbi abun hannun ki ya shaa ? Aaa ah ku ji min shegiyar yarinya zata min kashin kasuwa ta janyo min hasara ? Toh dan uwarki wuce maza ki je ki sauya kayan nan kamar yadda ƴar uwar ki ta sauya nata ,'idan ba haka ba a bakin aikin ki kin ji ko baki ji ba ?
Da sauri yakaka take gyaɗa kai daga inda take rakaɓe ,"
Sake ɗaga kayan yakaka take tana jujjuya su tare da ɗora su a jikin ta tana gwada tsawon rigar wacce take ƴar ɗigil da kaɗan zata rufe mata cibiyar ta da ƴan guntayen hannu maƙale hammata , tare da ɗan siririn siket ɗin da ya shaa tsagu a gefe da gefen sa har fiye da rabin tsawon siket ɗin ,
Niyyar ta ta kaiwa falmata a ɗinke mata wuraren da suka yayyage a tunanin ta ," sakamakon ganin kayan ƙanana ne tunanin ta sun ɗangale mata , dan haka ta yanke shawarar kaiwa ƙanwar ta ," duk da tayi tunanin kayan zasu matse falmata kasantuwar ta ɗan fi ta kaurin jiki ," gefe guda na zuciyar ta tana jin zata fi samun farin ciki idan falmata ta samu sauyin sutura fiye da karan kan ta ,"
Zabura tayi tare da fara kokarin zare kayan jikin ta sauya , jin motsi da tayi yana nufo É—akin da yake zaman mallakin Æ´an aikin madam saly a nan masu kwana a gidan suke kwana su kuma da suke yini su tafi anan suke cin abincin su , ita da yagana da suke duddungura sallalolin su suyi sallah a É—akin ," domin bayan su babu wacce ta damu da sallah cikin sauran ma'aikatan manyan su da yaran su da tsoffin su ,"
Juyowa tayi bayan ta sanya rigar a zaton ta madam saly ce ta leƙo ta ga koh ta shirya ,"
Karaf suka haɗa ido da ɗanliti wanda ya ɗaga labulen bayan ya tokare hannayen sa da jikin kofar yana ƙare mata kallo da jajayen idanun sa da suke cikin maye ,"
A firgice yakaka ta rarumi chukuikuyayyen hijabin ta ta suturta jikin ta ", tsaki ɗanliti ya jaa tare da ƙarasa shigowa ɗakin .,'
  Aikin banza da wofi toh yarinya meye zaki boye min iyee ? Baya koh gaba ?? Baya dai kin san nima ina da shi , gaban ma idan naƴi niyya zan taso su ehe ,"
  Jin tayi shiru ya sa ɗanliti buga tsaki dai-dai lokacin da yake zama a gefen wata yamutsatsiyar tsohuwar katifar da take yashe cikin babban ɗakin ,"
  Ƙwaila ma irin ki me zan gani a wannan busasshen jikin naki da bana zaton koh nonon kirki kina da shi ," duk abun da zan gani na riga na gani a jikin jigajigan manyan mata ƴan uwana ," ya ƙarashe zance yana wani jijjiga da girgiza gwangonin kirjin sa da yake a bushe ƙaranbau,"
Raɓar jikin bangon yakaka tayi bayan ta sunkuya ta ɗauki tsohuwar rigar ta da sabon siket ɗin , ta suɗaɗa ta fice a ɗakin tare da nufar bayan gida domin ta sa siket ɗin ,"
Bayan ta ya bi da kallo ,"
  Wai sunan wata kalma", Luwai ," yau naga ƴar kauye da lafiyayyar farar fata luwai-luwai,"ji yadda fatar ta take sheƙi da wani ɗan uban su fari na ainahi babu algus irin na su madam saly ," yarinyar nan idan ta samu hutu tabbas zata jaa gayu ahaayyee ,"gwara da babu ni a harkar ƴan maza ai da ganin da nayi wa bayan yarinyar nan da ace ina harkar maza da yau babu zaman lafiya,."