Sashe 9
Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bin sa da ido hajiya umma take "tana lure sarai da sauyin da aka samu akan fuskar sa tun da ta ambaci sunan maimouna "cike da so ta fara kwarara masa addu'a tare da sake jaddada masa ya kula da kan sa sosai , har zuwa lokacin da ya karasa ficewa daga wurin da take ",
Sauke ajiyar zuciya tayi a lokacin da ya bacewa ganin ta ,lokaci daya ta ɗauke fuskar ta daga jikin bulin makullin kofar tare da miƙewa tsaye ta juyo fuskar ta wacce take " ɗauke da wani tattausan murmushin da a zahiri yake nuna zuciyar ta na cikin annashuwa " dan tsalle tayi tare da juyi kafin a hankali ta motsa laɓɓan ta cikin cewa " za'a ɗaga bikin auren hamma youssouf har zuwa nan da wata shekarar me zuwa ,' taku ta fara yi a hankali da ya dangana ta da jikin katafaren gadon da yake rufe ruf da kyakyawan labulen da iskar da take busowa daga jikin tagar ɗakin yake ɗan kaɗa shi a hankali " janye labulen tayi tare da zama a bakin gadon " ɗan rangwaɗa kan ta tayi cikin cewa "ɗaga ranar bikin hamma youssouf yana nuni da nasarar da na kan iya samu ,hakan yana iya yiwuwar samun wata sabuwar dama a gareni ".,
Lokaci ɗaya ta gimtse fuska domin tunowa da tayi da nisan da hamma youssouf ɗin zai yi mata wanda ya sanya ba shiri ta ji hawaye ya cika gurbin idanun ta ","hamma youssof zai tafi Nigeria har na tsawon shekara , zan rabu da ganin sa na adadin kwanaki ɗari uku da sittin " bazan iya ba " zuciyata zata iya samun matsala kafin cikar adadin kwanakin nan ya zama dole na samowa kai na mafita " ., zabura tayi jin ana ƙwanƙwasa mata kofa ,'
Cike da jin haushi ta ce "waye a nan ? Cikin ladabi hadimar da take durkushe ta bakin kofar tace '"Allah ya huci zuciyar uwargijiya ta sako ne daga " Babbar uwa (hajiya umma ) tace a sanar da ke lokaci yana tafiya " ., É—an jim tayi kafin ta amsa kina iya tafiya gani nan fitowa ., ki fito lafiya ranki ya dade,'
Miƙewa tayi tana me jin duk fitar ta yau ta fice mata daga kai "tana da tabbacin yau bata iya tsinana wani abun kirki a wurin aykin ta "saboda chakuɗuwar farin ciki tare da bakin ciki ! A lokaci guda cikin ran ta ,'
Sake ɗurkusawa tayi har ƙasa tana me daɗa yin sallama da hajiya umma wacce ta kafe ta da ido tana me yin nazarin ta ", har ta miƙe da shirin tafiya ta ji hajiya umma ta sake kiran ta "yaki nan ɗiya ta ', dawowa tayi tare da sake durkusawa ", babu dai wani abun da yake damun ki koh ?
Da murmushi ɗauke akan fuskar ta ta ɗago tana me kallon fuskar mariƙiya gareta matar da a da take mata ganin mahaifiya tun tasowar ta domin bata taɓa cin karo da wani abu wanda zai sanya ta kokonto akan zaman hajiya umma mahaifiyar ta ba ,' har sai da lokacin da ta shekara goma sha bakwai(ta kammala makarantar gaba da primary ) a lokacin ne hajiya umma ta shaida mata hakiƙanin gaskiyar matsayin ta a wurin ta "hakan kuma ya samo asali ne dalilin ƙin amincewa ta bi mahaifin ta na ainahi da tayi ," da ya nemi son tafiya da ita wurin sa tayi hutun kammala karatun gaba da primary da tayi ", yazo da buƙatar tafiya da ita gidan sa domin ta ga sauran ƴan uwan ta da ya haifa tare da matar da ya aura bayan rasuwar zainab ",
Sosai a ranar tayi kuka ,kukan maraicin ta kafin a hankali ta hakura ," ta bi mahaifin ta , ta kuwa ji daÉ—i sosai da wannan hutun da tayi tare da kannen ta da matar mahaifin ta da ta kasance matar kirki ,'
Sai dai tun bayan dawowar ta daga gida (daga wurin mahaifin ta ) ta tarar da hamma youssof shima ya dawo daga jami'a inda ya kammala karatun sa ,' Rana ɗaya ta tsinci yanayin ƙaunar da take masa a zuciyar ta tana sauya muhalli ,daga so irin na ƴan uwan taka zuwa wata irin zazzafar soyayyah ,' ta aure wanda take jin idan har bata mallaki hamma youssof a matsayin mijin auren ta ba zuciyar ta kan iya samun babban raunin da zai iya dangana ta da kushewar ta ",
Gyaran murya hajiya umma tayi bayan ta gama nazarin ta sosai ta ce "siyama ki kasance me tsananta addu'a a koyaushe akan dukkanin lamuran ki kin ji koh ? Gƴaɗa kai siyama tayi ,' to maza tashi ki je ɗiyar Albarka Allah ya tsare min ke ya dawo da ke lafiya ," cike da jin daɗi da wata irin kakkarfar soyayyar mariƙiyar ta siyama take amsawa da Ameen "umman mu" Alherin Allah ya isar miki umman mu" ,
Tsaf hajiya umma ta gama gano abun da yake nuƙurƙusar zuciyar ɗiyar ta siyama ,'domin tun ba yau ba dai take lure da duk wani motsin Siyama akan youssof ɗin ," a kuma bangare guda na zuciyar ta lamarin sosai yayi mata daɗi ganin yadda yayi kicibus da tsohuwar niyyar da ke kulle a cikin zuciyar ta akan siyama da youssof ɗin tana da tabbacin baza ta samu matsala daga bangaren siyama ba".
Damuwar ta akan youssof ɗin ne wanda tun farko ta lura youssof ɗin bai wani cika kula lamarin siyama ba tun suna yara "kusan ma za ta ce jinin sa bai ɗauki siyama ba domin tun suna yara kullum faɗan sa da yayar sa 'ubbo' akan siyama ne ,' yana dukan siyaman kasancewar ta yarinya me tsinannen rawar kai a lokacin kuruciyar ta ,"shi kuwa youssof mutum ne marar son hayaniya hakan yasa garin sa bai jiƙuwa ƙoƙo guda da na siyama 'nan take zai bige ta ' wanda hakan yake haɗa sa faɗa da yar tasa domin duk duniya idan aka ɗauke hajiya umma da mahaifin siyama na ukun su a ƙaunar siyama ubbo ce ,sam bata ƙaunar abun da zai taɓa siyama ,' sosai take gwadawa siyama soyaƴyah da gata fiye da ƴan uwan ta da suke ciki guda ma, ' har dai zuwa lokacin da ubbo tayi aure a birnin Niamey gidan ta shine wurin hutun siyama a duk lokacin da ta samu hutun makaranta ,har kuma yanzu da siyama ta kammala karatun ta a shekaru biyu da suka gabata daga Université médecine- medical school ( makarantar horar da likitoci ) in da ta karanci fannin likitar haƙora ( Dentiste-Dentist ) ta kuma fara aiki a asibitin gwamnatin tarayya ta ƙasa reshen jahar maraɗi watanni sha tara da suka wuce , siyamar bata da zancen da ya wuce wurin da zata rubuta hutu musamman ta je da ya wuce gidan addar ta ta ubbo ,wacce mijin ta a yanzu ɗan majalisar tarayyah ne na ƙasa baki ɗaya ,"
A lokacin da youssof ya zo tare da batun ya samu matar aure a shekarar da ta gabata "dai-dai lokacin da ita kuma take gaf da fiddo manufar ta na son haɗa youssof da siyama aure ta shaida ga mai martaba "wanda ta san zai fi kowa farin ciki da wannan lamarin sanin da tayi lokacin marigayiya zainab tana raye suna da kyakyawar mu'amala ita da mai martaba duk kuwa da cewa shi mai martaba ya girmewa kanwar ta sa da tazara sosai domin mutane uku ke tsakanin sa da marigayiya zainab " , sai dai kuma youssof ɗin ya riga ta tada maganar auren in da yazo da murnar sa yake sanar mata da samar mata da suruka da yayi,' tun a lokacin ta so ta rusa maganar ta kuma fiddo masa da ainahin nata ƙudirin na son haɗa su aure shi da siyama,'
Sai dai jin wacce ɗan nata yake da zummar aurowa a matsayin surukar ta ya sanya ta yin laƙwas "ba wata bace wacce youssof ɗin zai auro illah maimouna ɗiya ga mai martaba sarkin AGAƊES , Maimouna ita ce ɗiyar sarkin agades mace ɗaya tal 'ƴar da ta samu gata da kulawa irin na bada kwatance .' Maimouna kyakyawar yarinya "ƴar buzaye" wacce ake kwatancen kyaun ta har ta kai sunan ta da kyaun ta ya shiga jerin abun kwatance a bakin al'umma " haka za'a ji budurwa idan ta ƙure wanka da gayu za'a ji masoyan ta na kururutata " wance kin kou ga kan ki sai kace gimbiya maimouna '? " ko kuwa idan budurwa ta cika feleƙe da yanga dan ita ɗiyar masu akwai ce nan za'a ji ƴan adawar ta suna faɗin" yo ai mu munga gimbiya maimouna ma karshen gata dai kenan" a taƙaice dai gimbiya maimouna ɗiyar gata ce gaba da baƴa ,
Sanin duk wani wanda ya kwan ya tashi ne cikin ƙasar Niger ", Sarautar birnin Agades shi ke da suna har karfin mulki fiye da dukkanin sauran manyan masarautun gargajiya da ke ƙasar Niger , sanin hakan da hajiya umma da mai martaba sarkin maraɗi suka yi ya sanya nan take zuciyoyin su suka cika da farin ciki ganin ɗan su zai auro ɗiya mafi soyuwa ga Sarkin agades ", wanda sun san hakan ba ƙaramin babban nasara tare da samun sabuwar ɗaukaka gare su da ma jahar maraɗi baki ɗaya ba ne ,"
Nan take hajiya umma ta ajiye zancen auren siyama da youssof a gefe wanda a da take jiran kammaluwar karatun ita siyama sai ta tado maganar kuma a wancen lokacin siyamar ta riga ta kammala karatun tun watanni biyar da sun ka wuce ", jinkirin da aka samu na son ta sake tsananta addu'ar neman zaɓi ne sai kuwa ga shi jinkirin ya zama Alkhairin da ya sa dole ta ture maganar siyama gefe ba kuma domin ta hakura ta janye zancen baki ɗaya bane "sawun giwa ne ya take na rakumi "sannan cikin ranta tana maimaita ai youssof mijin mace huɗu ne ", da wannan ta ajiye batun gefe , tare da bayyana tsantsar farin cikin ta da batun maimouna ,