Sashe 173
Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
" an yi haka bai fi da wata guda ba , Rahima ta gama shan kukan ta akan wannan batun , Babban Al'amari ya afku,
"Ranar wata juma'a bayan Rahimatullah da Salman sun gama hira da rabin ta neman hanyar warwaruwar matsalar su suke tare da kaiwa ga cikar burin su ,
"ƙarfe biyu da rabi na ranar bayan sallar juma'a labarin Rasuwar Salman Dilmari matashin Saurayi, ya bazu tare da yin tambari a baki ɗayan birnin Maiduguri kasancewar sa matashin ɗan siyasa da ya yi suna a lokacin ,
"ya rasu a sakamakon mummunan haÉ—arin mota da yayi akan hanyar sa ta komawa daga masallacin juma'ah mintoci arba'in da rabuwar su da Rahima ,
" mutuwar data girgiza zukata da dama , ta kuma bar miƙi a zuciyoyin wasu da dama , Salman Mai Alheri ne , Allah ya gafarta masa ,
Shiru ne ya ratsa tsakanin su saboda kuka haiƙan da Rahima take yi , kukan tasowar tsohon miƙin dake zuciyar ta da ya tarad sabon ciwukan dake cin ranta a kullum kwanan duniya ,
Mutuwar mijinta uban 'ya'yan ta da ta tarar da gawar sa a yashe cikin gona , haka kuma tana ji tana gani ta tsallake shi domin ceton ranta da na 'ya'yan ta ta tafi ta bar gawar sa a daji, tare da ɓacewar manyan 'ya'yan ta da har yau bata da sanin haƙiƙani kan rayuwar ko mutuwar su ta ma fi haƙaƙewa akan Yakaka da Falmata sun mutu kamar yadda harsashi ya samu Baana yayar Bulama ta mutu akan cinyar ta ,
Bakin lafayyar ta Amne ta sanya ta sharewa Rahima hawaye sannan ta cigaba da cewa ,
"Fasalta irin halin da baki É—ayan zuri'ar Dilmari ta samu kanta a ciki bashi yiwuwa ,
 "ai ka san lokacin kana da wayo sosai kana secondary School ,
gyaÉ—a kai Hamza yayi wanda idanun sa suka yi jaa ,
" Rahima ta shiga ɗimuwa marar misali domin har suma ta dunga yi , sai da Maigadin gidan ku na lokacin ya dunga yi mata rubutu , cikin sati guda da mutuwar sa Rahima ta rame tamkar majiyanciya , ni da kaina ƙarfin hali nake yi , nake hana kaina tunani saboda tsohon cikin Rahima ƙarama da nake ɗauke da shi .
"abu mafi muni da ya biyo bayan mutuwar Salman shine takowa da 'yan uwansa suka yi har gida bayan kwana arba'in da mutuwar sa , suka ci mutuncin mu ni da Rahima , a ƙarshe suka danganta mutuwar Salman da cewa ni da Rahima muka lashe masa kurwa muka kashe shi , to waye ya san salsalar asalin mu ??
"Ni kuka Rahima kuka , sannan abun takaicin mahaifinka yana zaune ya gagara hana su ko ɗaukar wani mataki na ba mu kariya , wanda hakan ni kuma ya tunzuro ni , na yunƙuro domin maida musu martani a karon farko bisa duk abubuwan da suke min marasa daɗi ,
"Ga maɗaukakin mamakina sai mahaifinka ya hayyaƙo min ya takore ni daga yin magana har ma yace muddin nace wani abu kome zai iya faruwa ga igiyoyin auren mu ,
"bisa tilas nayi shiru sai hawaye da muke yi ni da Rahima suka gama zage mu tas har da dungurin Rahima da alama ma duka suke da niyyar yi mata sai É—an uwansu ya rarrashe su ,
'tundaga wannan ranar Rahima ta sake yin sanyi duk ta susuce firgici ya bayyana cikin suffar ta bata da aiki sai tunani  ,
"duk da ceqa ina bin duk wasu hanyoyi domin kwantar mata da hankali duk da cewa nima hankalin nawa a tashe yake domin tsakanina da Mahaifinku babu daɗi , nema yake ƙarfi da yaji ya raba Rahima da gidan sa wanda nasan zugar 'yan uwansa ne da ni kuma ko kusa bazan lamunta ba , idan Rahima ta bar wajena ina zata ??
"har zuwa safiyar wata rana da na wayi gari Rahima kin yi gaban kan ki wajen barin Rayuwata , kin tafi kin barni cikin tashin hankalin da ya tunkuɗo min da naƙuda ,
"kika tafi ba tare da kin yi tunanin me hakan zai haifar ba cikin rayuwata ,
"duk wani wajen da nake tunanin zaki je Rahima naje neman ki har ms da wuraren da baza ki ba naje neman ki ,
" a cikin halin nan na matuƙar tashin hankali na haifi jaririyata da tun lokacin da na haife ta na shaidawa mahaifinku sunan ta Rahimatullah .
" da É—anyen jego na dunga fita kusufa-kusufa neman ki da hakan ya tunzuro Al-Mustapha yace muddin na sake fita neman ki da kaina a bakin auren mu ,
" a wannan ranar nima zuciyata a taurare take da zafin rashin ki dan haka nima na taso masa , a take a wajen na nemi da ya sawwaƙe min auren sa tun a nan domin kuwa fita neman ki yanzu na fara har sai ranar da na ganki ,
"shima da alokacin yake ganin zallar laifin ki na cewar ai ke da kan ki kika ga damar tafiya dan haka zaki dawo ,
"a fusace a wajen ya datse igiyar auren mu ba tare da yayi la'akari da irin raunin dake tare da ni ba ,
"Ban kwana a gidan ba na tafi tare da jaririya Rahima , na bar masa Hafsa da Zainab Hamza kuma yana makaranta,
" nayi neman ki Rahimatullah har N'Djamena naje an tabbatar min da baki zo ba ƙarin tashin hankalina shine duk sauran ƙannena a cikin matsanancin talauci suke ,
" Na tattara musu duk wasu 'yan kuÉ—aÉ—en da na tafi da su na basu , na sake dawowa Nigeria , tare da taimakon Æ™awayena biyu Hajiya Hadiza da Hajiya yaana , na sayar da tarin sarÆ™oÆ™i da Æ´an kunnayena zuwa wara-waren zinare da nake da su , na sayi gidannan da muke ciki , na É—ora neman ki daga inda na tsaya saboda na tabbatar kina Nigeria wataÆ™ila gari kika sauya , meyasa kika min haka Rahima ????Â
"aina kika rayu ? Ina mijinki kina da wasu 'ya'ya ne bayan wannan na cinyar ki ? Idan kina da su suna ina ??
Amnee ta ƙarasa bada labarin rayuwarsu da ɗora tambaya ga Khaalty Rahima wacce idanun ta yayi jazir tsabar kuka ,
Tausayin yayarta ya cinye zuciyar ta , ashe haka ta shiga damuwa akan rashin ta ??
ƙasa take son sharewa tayi rubutu ,
Amnee ta miƙe ta kawo mata takarda da biro , ta sanya hannu biyu ta karɓa ,
taƙaitatcen rubutu tayi a jikin takardar ,
"Â tsoron kar na zama sanadin rabuwar auren ku da Yaya mustapha yasa na tafi daga gareku ukhtee Amina ki yafe min , bansan ba zan zama sanadin tarwatsewar jin daÉ—in rayuwar ku .
"Mairambiri shine sunan ƙauyen da na rayu tsawon lokaci a cikin sa kafin zuwan yan tawayen boko haram su tarwatsa garin su kashe mijina da manyan yarana biyu mata da suma nake zaton sun mutu , Amina da Fatima shekaru shida yanzu da mutuwar su .bayan su ina da wata 'ya da ita ma harsashi ya same ta ta mutu , a yanzu Bulama shine kaɗai ɗana .
ASSALAMU ALAIKUM
'Yan uwa ina miƙo saƙon gaisuwata tare da fatan Alheri gare ku baki ɗaya , ina kuma mai yabawa bisa ga yadda kuke nuna ƙaunar ku ga littafin nan ,
nagode .
[11/15, 11:03 PM] +234 806 600 1491: MAFARI
( Hargitsin Rayuwa )
Umm'muaz
39
Duk yadda Falmata take tunanin daÉ—in dake ga mallakar idanu ta tadda shi ya wuce haka , jin kanta take tamkar sabuwar halitta ,
Har bata so bacci ya shiga tsakanin ta da ganin hasken duniya , karambani kuwa babu irin wanda bata yi , har girki take karambanin yi Yousssouf kuwa yana taya ta ,
Shima a ɓangarensa baya gajiya da duk wasu tambayoyi da ko karambanin da zata yi , wani irin son ta yake yana riritata ,
Mama da kanta tasan cewa yanzu Mamarta ta samu waraka saboda wata kulawa na musamman da idanun ta sun hango mata wani É—an datti a jikin kayan Mama zata yi maza ta gyara ta ta sauya mata wani ,
A kullum ta Allah sai ta miƙa godiyar ta ga Youssouf kamar yadda cikin duk wasu sallolinta sai ta ƙara godewa Allah akan wannan babbar kyauta da ya yi mata na dawo mata da ganin ta ,
Godiyar da take yiwa Youssouf ba a fatar baki kaɗai ta tsaya ba , har a aikace take gwada masa ta yadda take nuna masa ƙauna tare da ɗaukar buƙatun sa ba tare da gajiyawa ko ƙorafi ba .
Kamar yadda likita yace tana cigaba da zuwa ana dubata , babu wata sabuwar matsalar da ta ɓullo tunda aka yi mata aiki .
Idan tana da wata damuwa to ta lafiyar Mama ce wacce kwana biyu ciwon ta yake ƙoƙarin tasowa suna danne shi da tarin magunguna gami da ƙara ƙaimi wajen kulawa da ita , amma duk da haka kallo ɗaya za'a mata a iya hango tarin raunin dake tare da ita tun daga cikin raunanan idanunta da suka ɗan sauya launi zuwa ruwan ɗorawa har zuwa ƙafafunta da hannayenta da suka ɗashe suke yawan ɗaukar sanyi ,
Gaba É—aya Falmata da shi kansa Biyamuradi Youssouf basa tare da walwala sosai ,
"Baban Mama ko dai za'a sake komawa asibitin nan ne maganar aikin Mama ,
Youssouf wanda yake shafa kan Mama wacce take kwance cikin jikin sa lamo , ya ɗago kan sa yana duban idanun Falmata da suke nuni ƙarara da damuwar da ruhin ta ke ciki ,
"Fatima duk wassu bayanai da zamu sake samu daga Doctora basu wucce batun baya da sunka faÉ—i muna , wanda kouma mun bar Lamari ga Allah zouwa lokacin da za'a samu damar yin aikin ,
Shiru tayi tana cigaba da kallon sa , cike da damuwa , so take yayi wani yunƙuri kome ƙanƙantar sa ,
Ji yayi gangar jikinsa na karban sakon dake fitowa daga cikin ƙwarar idanunta masu kyaun kallo ,