Sashe 166
Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta sake ajiye hannu da zummar miƙewa hannunta taji ya sauƙa akan sandar ta , cikin sauri ta laluba ta ɗau sandar , ta kama hanya fita daga gidan tare da taimakon sandar hannunta,
Bata damu da ta sake É—ora wata rigar sanyi ba illa ta jikinta da take iya guiwar ta sai kuma siririn siket da hular sanyi a kanta ta fice a gidan ba tare da ta san ina ta dosa ba ,
Tsananin sanyin da ya ratsa ƙasusuwan ta lokacin da ta fito waje bai sa ba ta koma illa tafiya da ta cigaba da yi tana laluben hanya da sanda ,
Unguwar da suke shal babu kowa sai tsilla-tsilla motoci ke wucewa haske ya wadaci ko'ina da taimakon fitulun gefen hanya duk kuwa da duhun dare da ya fara mamayar sararin sama.
Tayi tafiya mai nisa lokacin da tsoro ya gama cin galaba akan ta nadamar fitowar ta ya ziyarce ta ,
Matsanancin sanyin da ya fara cin ƙarfin ta sakamakon dusar ƙanƙarar da ya fara sauƙa ya sa ta gaza ci gaba da tafiya gaba ɗaya ji take kamar jinin jikinta ya daskare ,
Durƙushewa tayi a wajen da bata da masaniyar ina ne ?tana jin yadda sanyin wajen da ta zauna yake ratso jikin kayanta yana daskarar da duk wani ruwa na jikinta ,
Idanunta da hancinta suna tsiyaya ta dunƙule jikinta waje guda tana karkarwa ,
A cikin ran ta ta haƙiƙance rayuwar ta ta zo gangara , ashe ita kuma irin tata sanadin mutuwar kenan sanyi ?
****
Biyamuradi Youssouf tunda ya fita saɓe da Mama , yayi ɗan tattaki cike da rashin sani takamaimai ina zasu ??
Ya zaɓi ya fita ne saboda yana da yaƙini zuciyar sa ba zata jure ganin fushin ta ba , da shi kuma a wannan gaɓar bai yarda yayi wani yunƙurin ds zsi fallasa halin da zuciyar sa ke ciki ba a kan ta bai so ta gano lagon sa tunda wuri haka ,
Cigaba yayi da tafiya har ya cimma babban titi , nan ya hango wani shagon sayar da coffee ,
Bayan ya ƙarba musu coffee me zafi ya zaunar da Mama a kujerar da ke fuskantar ta shi ,
Juya ɗan chokalin hannun sa yake yi ya gagara shan coffee ɗin , damuwa tayi masa ƙawanya duk wata walwalarsa ta kau ,
Ko kusa ba zai iya duban ta ya fayyace mata lamuran da suka auku tsakanin sa da 'yar uwar ta ba , yana jin kunya , yana kuma tsoro .
Meyasa ta kasa fahimtar barin abunda ya riga ya wuce a muhallin shuÉ—aÉ—É—an lamari shi yafi alheri fiye da tone-tone . ?
Duban sa ya kai ga Mama wacce tayi shiru ta lanƙwasa kai fuskar ta bayyane da damuwa ,
Tausayin ta ya ji domin ya san damuwar ta ta samo asali ne ga abunda ya faru tsakanin sa da Falmata , da shima zuwa yanzu nadamar ihun da yayi mata yake yi ,
Bai yi hakan da wata manufa ba illa ruɗanin da ya tsinci kan sa a ciki da ya sa bashi da wata hanyar daƙile yunƙurin ta tare da kawo ƙarshen maganar idan ba ta hakan ba .
Tashi yayi ya zagaya ya É—auki Mama suka fito daga Coffee Home É—in ba tare da ya sha coffee da ya saya ba ,
Sake nusawa yayi bakin titi yana tafe sannu kan hankali har ya tadda ɗan wani killacaccen wajen yin sallah , nan yayi sallar la'asar tare da Mama a gefen sa ,
Bayan ya idar hankalin sa ya kai kan wani fili gaban wasu gidaje da matasa da yara suka taru suna wasan ƴar zamiya akan dusar ƙanƙara Tobogganing , kama hannun Mama yayi suka ƙarasa wajen ,
Ya zauna daga gefe kan kujerar gefen hanya tare da É—aura Mama a cinyar sa ,
Sosai wasan ya ɗau hankalin Mama ganin yara ƙanana sa'o'in ta nata faɗuwa da tashi cikin dusar ƙanƙara , nan take ta shagala da kallon su har tana taya su dariya idan wasun su sun faɗi ,
Ganin walwalar Mama ya bashi damar zurfafa a tunani , sashi guda na ran sa na shawartar sa akan idan ya koma gida ya faɗa mata gaskiya ksn abunda take son sani , yayin da sashi mafi rinjaye ke ƙwabar sa tare da tsoratar da shi abunda faɗa mata gaskiyar zai iya haifarwa ,
Abunda ya haƙiƙancewa ba zai iya jurar fushin ta da damuwar ta ba domin kusa take sosai da ruhin sa ,
Bai ankara ba har duhun dare ya fara shigowa , dan haka ya sake komawa wajen da yayi sallah , ya sallaci Magarib ,Â
Yana idarwa ya kamo hanyar gida bayan ya saɓa Mama a bayan sa da tayi laushi tuɓus ,
Ta gaban manyan shagunan sayar da kayan ƙele-ƙele na mata ya zo wucewa , idanun sa suka kai kan wata 'yar kyakkyawar sarƙa da take ɗaukar ido tare da taimakon hasken lantarki da ya haske cikin gilashin da sarƙar take .
Murmushi yayi lokacin da idanun sa suka hasko masa sarƙar a cikakken wuyan Falmata ,
Da hanzari ya shiga shagon ya sayi sarƙar da take ta farin zinare ƙirar ƙasar Amurka suka zare kuɗin su ta katin sa tare da zura masa akwatin sarkar cikin 'yar jakar da take ɗauke da tambarin Manns jewelry .
Cike da fargaban halin da zai riske ta ciki ya nufo gidan , zuciyar sa na aiyana masa wataƙila tayi ta kuka ,?wataƙila kuma ran ta ya sake ɓaci da shi, koma menene zai bata haƙuri ys rarrashe ta ta bar maganar nan ,
Da Sallama ya tura ƙofar gidan ya shiga ,
Shiru ya ji bata amsa ba ,
Ya lalubi wutar falon ya kunna ,
Idanun sa akan É—an wajen kunna witar É—umama É—akin da har wutar ta mutu , hakan ya sa É—akin ya É—au sanyi
cikin ran sa babu daɗi , Ya zaunar da Mama akan kujera , yayi tsaye yana saƙe-saƙe , jikinsa gaba ɗaya yayi sanyi da barin ta da yayi ita ɗaya ,
Takawa yayi ya ƙarasa bakin ƙofar ɗakin ya ɗan ƙwanƙwasa ,
" Fatima , mun dawo
Ya furta haka da sauƙaƙar murya ,
Shiru ya sake ji babu alamun motsi ,
Sai ya murɗa hannun ƙofar ya shiga ɗakin , cikin 'yan daƙiƙai ya fahimci bata ɗakin , da sauri juyo , kai tsaye ya leƙa cikin ɗaya ɗakin , babu alamarta
Tamkar an safure shi haka ya dunga bin kowanne lungu da saƙo na gidan yana neman ta tare da ƙira sunan ta ,
A ƙarshe ya hiƙanƙancewa kansa tabbas bata gidan , ta fita ne ? Ko an sace ta ? Shikenan shi kam ya shiga ukun sa , ta shi kuma ta same shi .
Da gudu ya sunkuci Mama ya fito , dusar ƙanƙara na sauƙa a kan su yayi tirus a harabar wajen , ina zai fara nufa neman ta ? Wa zai dosa ya tambaya akan ta ?
Gidan da yake maƙwaftan na su ya nufa da sauri ya danna musu ƙararawar neman iznin shiga gidan ,
Zuciyar sa na ayyana masa wataƙila ta shiga gidan ,
Tunanin sa ya katse lokacin da aka buɗo ƙofar wani mutum magidanci yayi tsaye yana kallon sa ,
Da harshen turanci ya gabatar masa da kan sa a gurguje kafin ya É—ora masa tambaya kan ko matar sa ta shigo gidan su ?
Da harshen larabci mutumin ya miƙa tambayar ga matarsa da take daga bayansa a tsaye ,
Nan suka tabbatar masa da babu wacce ta shigo musu ,
Har ya juya sai kuma ya dawo ,
Rokon su yayi akan su taimaka su riƙe masa 'yar sa zai je neman matar sa ,
Basu musa ba suka karɓi Mama da tayi rau-rau da ido tana shirin kuka ganin Babanta zai tafi ya bar ta hannun waɗanda bata kai ga sanin su ba ,
Bai kula ba ya juya da sassarfa mai haɗe da gudu ya kama doguwar hanyar da tayi cikin unguwar sosai yana tafe yana dube-dube da waige-waige , hankalinsa yayi ƙololuwar tashi , maƙogoran sa ya bushe , idanun sa har raɗaɗi suke yi masa ,
"Yaa Allah Fatima ina kike ? Yaya za ki min hakka Fatima , ? Meyasa kika fita ?
Ya furta hakan muryarsa na karkarwa , bayan hannun sa ya sa ya goge fuskar sa da iskar dusar ƙanƙara ta watso masa ,
Ganin har ya kusan ƙure unguwar bai gan ta ba ya sa shi komowa baya , yana cigaba da neman ta , addu'o'i iri-iri yake yi ,
Zai iya cewa tunda yake bai taɓa shiga tashin hankali irin na tsuƙin lokacin nan ba , bai taɓa sanin ita wata kadara ce mai maɗaukakiyar daraja a wajen sa ba sai a wannan gaɓar da yake gaf da rasa ta ,
bazai yafewa mummunar zuciyar sa ba idan har wani abun cutarwa ya same ta ,
Sakin hanya yayi ya nufi wata doguwar hanyar da tayi gefe a tsakankanin dusar ƙanƙara
Fatima , Fatima , Fatima
Yake ƙwala ƙiran sunan ta ,
Ya ƙure hanyar bai ko ga alamun sawun ta ba sai zunzurutun sanyin a yake ratsa sa ,
Dawowa yayi da baya ya sake kama wata hanyar ta daban nan ma yana tafe yana kiran sunan ta ,
Durƙushewa yayi a gefen hanya yana jin tamkar ya ƙwala ihu ko ya ji sauƙin tashin hankalin da yake ciki ,
Kamar a sama ya fara jin amon Murya ta daga nesa , tana ƙiran sa
Da gudu ya nufi inda yake jin tashin sautin ta ,
A gefen hanya zaune cikin dusar ƙanƙara ya hango ta ,
Hannuwan sa duk biyu ya sa ya ɗago ta , ya riƙo kumatun ta dama da hagu ,
"Fatima meyasa kika fito ? Ina za ki je ? Fatima kar ki sake tafiya ki bar mu .
Ta kifta idanun ta da suka bushe ƙemas saboda sanyi tace ,
"Baban Mama ku na fito nema , dan Allah kayi haƙuri kar ka sake tafiya ka bar ni , bazan sake yi ma laifi ba ,
Kamota yayi suka miƙe tsaye , yadda take rawar sanyi ya tashi hankalin sa , "