Sashe 164
Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kai tsaye ya doshi sashin , a ƙofar ya tsaya yayi sallama bai ji an amsa ba , baki uku yana sallama ba amsa ,
Cike da nutsuwa ya tura ƙofar da take ta ƙarfe ya shiga faffaɗan filin da yake ɗauke da wasu ɗakuna uku daga kan wata yar baranda ,
Yawata idanun sa yayi a filin wajen , daga gefe ya hangon ta a zaune , tana soka allura da zare a jikin hular da take hannunta tana É—inkawa ,
Yayi mata kallon mintuna biyu masu kyau kafin ya fara taku yana kusantar ta , zuciyar sa cike da yaƙini kan kasancewar ta innar sa ,
Kamar daga sama ya faɗo haka ya gan shi tsil a tsaye a gaban shi yayi banga-banga ya riƙe kunkumi ,
Duban sa ya mayar kan sa yaro ne da bai wuce shekaru takwas ba fari kal da shi irin mamar sa , launin idanun sa yayi masa yanayi sosai da na wata da ya sani da a lokacin baida damar zurfafa tunanin ganota,
Girar sa ya ɗaga yana kallon yadda yaron ya ƙanƙance ido yana wani kumburi kamar mai shirin dambace sa'an sa , ya gane shi sarai yaron nan ne dai da ya bangaje dattijon nan a waje ,
Murmushi yayi tare da miƙa masa hannu ,
"Salamu Alaikum abokina , ni sunana Dr .
 Tsuke baki ya sake yi , kafin ya amsa cikin dakiya
" Ni kuma sunana Bulama , waye kake nema ? Wancen mamata ce sunan ta Mamar Bulama , nan wajen mu ne masu aiki , can babbar ƙofar can nan ne wajen ku 'yan gayu ,
Mayar da hannun sa aljihu yayi ya gyara tsayuwa yana murmushi tare da mayar da hankalin sa kan yaron domin sosai yanayin wayon sa da tsaurin idon sa ya burge shi ,
" wajen Mamata nima na zo ba wajen yan gayu ba ,
 Da sauri Bulama ya katse shi
"waye mamar ka to ?
Da baki Doctor hamza ya cuna masa Mamar Bulama da take nesa da su ta duƙufa ɗinkin ta babu alamun ta san da tsayuwar su a wajen.
' Ga mama ta can ,
Da sauri ya waiga ya dubi Mamar sa , sai kuma ya dawo da ganin sa kan Doctor Hamza .
" Mamata ce Mamar ka ?
Ya furta hakan yana bin shi da kallon mamaki daga sama har ƙasa ,
"unhun ,
Doctor Hamza ya amsa masa yana É—aga kai alamun tabbatarwa
Da gudu ya juya wajen Mamar sa yana dariya ,
 Da murmushi ya bi bayansa zuwa inda takeÂ
Yana zuwa faÉ—awa yayi a kanta , zabura tayi da ya sa allurar da take É—inki da ita ta soki hannun ta ,
Dungure Bulama tayi tana harararsa .
Bata lura da kasancewar sa a wajen ba , sai da ya kamo hannunta da ta riƙe tana duba wajen da allura ta soke ta da har yake jini ,
Da firgici take kallon sa da ya sa É—an hankici yana naÉ—e mata hannun , sannan yana ce da ita ,
"A iya sanina Uwa bata gudun ɗan ta kome muni ko tsananin Lamari , a matsayin da muka ajiye juna tun farkon-fari mun fi shaƙiƙan abokai kusanci , ina zaton kin manta da kika ce ke zaki fara rakani taɗi wajen budurwata ranar da zan fara tsayawa da ita , sai kuma ga shi shekaru sun tafi sun yi nisa cikin wani irin bauɗaɗɗan lamari marar daɗi , da har ɗan nan naki yayi aure baki sani ba , ba kuma kya son sani ,
Ya ɗago kan sa bayan ya gama naɗe mata hannun , ya kalli ƙwarar idanun ta da suke sake bayyana masa tare da tabbatar masa ita ɗin ce dai ,
Da wani irin yanayi yace ,
"khaalty nasan kina ji na , kin kuma gane ni , idan baza ki magantu domi na ba , ki magantu dan Amne Amina , ki dubi girman Allah ki waiwayi 'yar uwarki , ki koma mata ko rayuwar mu zata dai-daita gaba É—aya ,
"kar a tuno da kome da ya riga ya faru ya wuce , yanzu lokaci ne yayi na gyaruwar kome ,
Hawayen da suke sauƙa a idanunta ne suka ɗigo akan bayan hannun sa
Hannun sa É—aya ya kai da nufin goge mata ,
  Bulama wanda idanun sa suka kaɗa suka yi jaa yana daf da fashewa da kukan shima , ya ture hannun Hamza , ya sa 'yan tafukansa biyu ya share mata hawayen , kafin ya waigo gareshi ,
" Kai ba yaron ta bane tunda ga shi ka sa ta kuka ka tashi ka bar gurin mu ,
" ka fita
Ya ce yana tura Doctor Hamza
Doctor hamza ya miƙe a hankali ganin taƙi cewa kome ga kuma hayaniyar Bulama da take ƙara damun sa .
Yayi taku biyu yaji tayi magana da sautin da baya fita mai kyau irin ns bebaye ,
Juyowa yayi sai ya ga ta miƙo masa hannuwanta irin yadda take yi masa tun suna yara ,
Da murmushi a fuskar sa ya koma yana sassarfa ya harɗe yatsun sa cikin nata da zuwa lokacin kuka take haiƙan ,
"la bas , ki daina kuka khaalty ,
Yake cewa ga ita da sigar rarrashi .
Hawayen ta ta goge Bulama yana taya ta kafin ta sunkuya ta share rairayin da yake ƙasa ta rubuta masa da yaren su ,
  kayf hal 'ukhti ? (Ina yar uwa ta ?) kayf tamakanat min aleaysh bidun ily? ( yaya tayi rayuwa bayana ? )
 Kafin ya amsa mata ta sake rubuta masa wata kalma
" aftaqadaha kathirana , ( nayi kewar ta sosai )
A takaice ya bata labarin Amnee da mafi yawa yafi karkata ga halin damuwar da take ciki akan rashinta , ya ɗora da sanar da ita rabuwar auren iyayen sa , da haifar da ruɗani tare da ƙaruwar zubar hawayen ta ,
Ƙarshe ya roƙi da ta zo ya kai ta wajen 'yar uwar ta .
Nan ya ga sabon ɓacin rai akan fuskar ta kafin ta tirje ta nuna ƙin amincewarta da batun ,
Duk yadda yake zaton lamarin zai kasance ya wuce haka , domin kuwa a ƙarshe ta sanar da shi muddin ya matsa kan batun komawar ta gida zata bar inda ya sani ta sake maɓoya ita baza ta taɓa komawa gida ba .
Rochester New York
Cikin kwanakin da suka biyo bayan zuwan Falmata asibiti tare da fara shan maganin ta , sosai aka samu cigaba ga lafiyar idanun ta inda cikin satin ta na biyu da fara shan maganin ya zamana tana iya ganin alamun haske fayau amma bata ganin hoto , hasken ma wasu lokutan yana zama babu ,a wasu lokutan kuma yana mata yawa sosai ta yadda har take gagara buÉ—e idon ,
Hakan ya sa da ta yiwa likitan ƙorafi sai ya bata shawarar ta nemi tabarau da ake amfani da su wajen rage ƙarfin hasken rana , watau tabarau masu duhun launi , bayan haka kuma ya sake shawartar su akan amfani da sandar makafi , ( white cane )
Domin zai taimaka mata wajen gudanar da al'amuranta na yau da kullum a sabbin wuraren da bata kai ga sani ba , zai kuma bata kariya tare da zama garkuwar a gareta .
Dan haka Biyamuradi ya tafi kanti da kan sa ya zaɓo mata tabarau masu kyaun suffa na mata , tare da sayo mata sanduna har guda biyu .
Falmata wacce tun ranar da ta saurari hirar Biyamuradi da Maimounatu duk ta zama wata iri , damuwa tayi mata yawa sannan 'yar sakewar da ta fara yi da shi ma duk ta bi ta daina ta koma takura kan ta kamar farkon auren su .
A hankali ta lura da yawan yin waya da mata biyu da yake yi daga barandar gidan ta waje ,
ta gane su biyu ne ta yadda daga ya gama waya da ɗayar yake ƙiran ɗayar , sai dai ko kusa taƙi yadda ta sake saurarar hirar sa da ta lura shima bai son ta ji tunda fita yake yi idan zai yi wayar sannan ko Mama bai yadda ta bi shi .
A ɓangaren Biyamuradi shima shirun Falmata tare da damuwar da take ciki ya fara damunsa , sai kaffa-kaffa yake yi da ita yana ta bin hanyoyin ganin ya dawo mata da walwalarta kamar farkon zuwan su ,
A yau ma yana zaune tare da su a falo Mama tana wasan ta a gefe da tilin kayan wasan da ya sayo mata su tari guda tarkace iri-iri .
Wayar sa tayi ƙara alamun shigowar ƙira , hannun sa da yake dafe da kan sa da ke ɗan masa ciwo sama-sama ya janye daga kan shi tare da yunƙurawa ya zauna sosai ya ɗau wayar sa ,
Ganin wanda yake ƙiran nasa ya sa shi tattaro duk wata nutsuwar sa ,
" Assalamu Alaikum Maimartaba barka da war haka da fatan alheri .
Daga can Maimartaba ya amsa masa , suka gaisa , kafin ya jefo masa tambaya da ta so ruÉ—a shi da farko
" Youssoufa wake tare da kai nan ƙasar Amurka ? Kacce bisa ga aiki ka tahou nan kou ?
Satar kallon Falmata yayi wacce take zaune daga gefe a ƙasa ,
Sai ya miƙe ya fita
Bata ganin sa amma taji takun barin sa wajen , ajiyar zuciya ta sauƙe tana jin damuwar ta na sabunta ,
" wayar zai je yi da su ,
  Ta aiyana haka a cikin ranta .
"Ranka ya daÉ—e bissa aiki na zou nan kouma tare mukke da abokan aiki na kamar yadda na faÉ—i tun farko ,
Daga ɓangaren Maimartaba sarki Abdoul-Azizou yayi shiru yana nazari , kafin ya amsa
" Madalla Allah shi taimaka yaushe kake dawouwa ?
Cike da jin daÉ—i Youssouf ya amsa da
"ƙasa da watanni huɗu ko biyar ranka shi daɗe ,
"Allah shi dawo da ku lafiya , ka tsayar da gaskiya cikin dukkanin lamuran ka , sannan ka tsananta addu'a .
Ya amsa da
"Â to nagode sosai Ranka shi daÉ—e .