Sashe 48
Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tsawon dare falmata bata yi wani baccin kirki ba daga ta fara baccin zata ji ƙarar marukan da mutumin nan ya dunga yi mata , cikin ranta tana sake tsorata da mutane gaba ɗaya , abun da ta fahimta a ɗan ƙarancin shekarun ta shine mutane basu da kirki mafi yawan su azzalumai ne tana mace bata huta ba ta zama namiji ma bata tsira ba , sai dai cikin ran ta tayi niyyar boyewa yakaka abun da ya faru da ita domin ta huttashe ta shiga damuwa a dalilin ta , tasan daga lokacin da yakaka ta ji abun da ya faru baza ta sake samun nutsuwa ba har sai ta samo hanyar da take ganin ta bada kariya a gare ta , kwatankwacin wacce ta baro su daga sansanin su , a gare ta samun kwanciyar hankali tare da walwalar da take tsinkayowa daga muryar yakaka yafi mata kome , baza ta so tayi wani abu da zai Wargaza mata farinciki ba , hakan ya sa da a halin yanzun yakaka ta takura ta faɗa mata abun da ya sa ta kuka , taƙi bayyana mata haƙiƙanin gaskiya ta danganta kukan ta da tuno da mahaifan su da tayi ,
Kwanaki biyun da suka biyo baya sun yi su ne cikin takura , ita yakaka al'adar da take yi ita ta hana ta sakewa a matsayin ta na sabon shiga , dan haka duk a takure take jin kan ta gani take kamar kowa ya san halin da take ciki duk kuwa da cewa dai-dai gwargawdo samy baby ta wayar mata da kai tare da saya mata sabbin pad da pants,kuma zuwa yau da take kwanaki biyar da fara yi , ya fara jaa baya, ita kuwa falmata fargabar da take danƙare cikin ran ta akan irin matakin da ɗan liti zai ɗauka akan ta ne a lokacin da mutumin da ya kai ta wajen sa ya tabbatar masa da cewa ita mace ce ,
Sai dai a yau da ake kwana biyar da faruwar lamarin ta É—an samu nutsuwar zuciya ganin har yau bata ji ko ganin wani sauyin da yake nuna mutumin nan ya gayawa É—an liti wani zance ba, dan haka ta sake suka yi hirar su ita da yakaka da yagana waÉ—anda suke É—an zagayowa su taya ta wanke-wanke , walwalar ta ta sauya zuwa taraddadi ne lokacin da ta ji muryar É—an liti yana dannanawa madam saly kira ,
ahayye nanayee madam saly fito, fito , fito ki ji sabon bayani abun mamaki ciyawa da cin doki ,wai kamar mu a garin nan za'a nunawa barikanci , za'a yi mana ungulu da kan zabo ,? Chafɗijam , inji masu iya magana suka ce bar ganin ƙanƙantar allura karfe ce , yekuwa jama'a ku hallaro ku ji abun al'ajabi ango ya kwana da ƙunzugu ,
Da ɗai-ɗaya hankali mutanen wurin ya fara dawowa kan sa saboda tsabar ƙwarmaton sa hatta masu cinikin madam saly da suke cikin rumfa sai da suka ji yo shi wasu ma har suka tsallako suka zo ganin dal ,"
Liti yaya ne ? Yaya ne ?ya da irin wannan kiran haka ? Ta samu ne ? Ko kuwa ta guntso ne zata fesar , ? Kunne na tarwai ina jin ka bamu mu sha ," cewar madam saly wacce take ƙarasowa wurin tare da wasu daga cikin ƴan aikin gidan ,"
To wallahi yaran nan yaks da ƙawar ta tare da munafiki koh munafukar ƙanwar ta zan ce ? Yo abun ne ya sauya , ninke mu baibai suka yi suka buga mana stamp ɗin sakarkaru na gaya miki, "
Wani banzan kallo madam saly take sakar masa kafin ta jaa É—an guntun tsaki ,
Ban gane ba ? Daman akan waÉ—annan yaran kake kwalla wa jama'a kira har da yekuwa ? , kai dai Allah wadaran ka dan liti
Tsiya ta da ke wutar ciki madam saly , toh na rantse da Allah kachalla dai mace ce , macen ma luntsumemiya kuma nunanniya , shine dan iskanci da kuturun munafurci yaran nan suka ce wani wai namiji ne , aradun Allah ma ni ban yadda da su ba idan ba turo su ɗaukar rohoto aka yi ba , atoh ki dai bincika ki kuma san abun da kike ciki kar sai kin baje kafafu ki ji anyi ramm da ke anyi sama da duwaiwan ki atoh , zamanin nan na yanzu ko inuwar ka baka sakankance da ita ba dan zata iya harɗewa ta shige cikin na makiyin ka idan kuka jeru, ji min duniya mai abun mamaki wai ƴan waɗannan ƙuya-ƙuyan yaran sun iya dabo-dabo da rufa-rufa , toh dan uban uban ku yau asirin ku ya tonu ,"
Duk maganganun da yake suna sauka a kunnuwan falmata wacce take duƙe a bakin fanfo da kuma yakaka wacce ta kawo kai domin shigowa ta karbi burkutu ta kaiwa abokan ciniki , dukkanin su tsam suka yi da jin kalaman ɗan liti , wannan fa shi ake kira an yanka ta tashi , take falmata ta fara yin hawaye , yayin da yakaka ta ɗaure ta cije tare da jaan ƙwanjin kare falmata ,"sai dai ayi wacce za'a yi wai bera ya zubda garin ƙyanwa ,"
Madam saly ce ta juya ga falmata bayan da ta gama jin zantukan É—an liti ,
Kai kachalla zo nan
Sum-sum falmata ta taso tana laluben hanya ta sashin da taji tashin muryar madam saly
Haiyaratataa ni idan ba makantar taki ma ban yadda da ita ba , ni daman kullum ina shakkar waÉ—annan idanun naki da suke wural uwa na mujiya da tsakiyar dare ace wai bakya gani ??? Cewar É—an liti wanda yake jijjiga ya dogare daga gefe ,"
Kai kachallah meye gaskiyar maganar da ɗan liti yake faɗa akan ka ? Tambayar da madam saly ta jefawa falmata wacce take durƙushe a gaban ta kenan , "
Madam karya yake min ni ban san kome akan abun da yake cewa ba ,"
Wata irin zaburowa É—an liti yayi ya dako tsalle ya bangaje Æ´an matan da suke tsaye daga gaban shi ,ya dire a gaban falmata ,"
Dan ubanki Alhaji basko zai miki karya ne ,? Toh idan kin ce karya ne É—aga rigar ki aga kirjin ki , nace É—aga rigar ki mu ga kirjin ki Æ´ar iska jaririyar Æ´ar bariki ,'
Toh kai kachalla ai sai ka cire rigar mu ga kirjin naka domin cire zargi cewar madam saly," sunkuyar da kai falmata tayi tana matsar ƙwalla
Koh kafin su farga É—an liti yayi charaf ya kaiwa gaban rigar falmata chafka , baiyi wani jinkiri ba ya sa karfin tuwo ya balla baturan da suke jere gaban rigar , yana cewa
Dan uwar ki rigar uban waye ya saya miki ba ni ba ?? Yau sai mun ga karshen karya ,"
Da gudu yakaka ta karaso wurin ganin ana neman tozarta ƙanwar ta ayi mata tsirara cikin taron maza da mata ,"
Ƙoƙarin raba hannun ɗan liti da jikin rigar falmatan ta fara , tana cewa
ÆŠan liti ka sake mata riga meye hakan ? Wai ina ruwan ka da harkar mu ,"
Wata dariya ɗan liti ya sake , kin ji koh madam saly nace kin ji koh ? Da bakin ta take ambaton ta a jinsin mata , shegu munafukai , yau me raba ni da ku sai Allah tun da kuka jawo min asara , yana gama faɗin hakan ya ingije yakaka tayi faɗuwar ƴan bori , kafin ta taso , ya sanya dukkanin karfin sa ya jijjiga falmata gami da keta mata riga , ya sanya hannayen sa duk biyu ya cisge tsunman da take ɗaure kirjin da shi ,ya murɗa hannayen ta tare da lanƙwasa su baya ya banƙaro kirjin ta gaba wanda hakan ya bayyana haliltar kirjin ta tsai a tsaye ,"
Wani irin guntun salatin da ba'a ƙarasa shi ba tare da shewa da ihu sune suka cika wajen daga bakunan mata da mazan da ke wajen , cewa suke wallahi chika ce , laaah ,
A toh idan har yanzu ba'a yadda ba sai na ɗaga muku ƙasan shi ma ku gani dan gaba kar a karkace a kuma sharo wata ƙaryar ace mata-maza ce gara a ga ƙarƙashin ,
Nan dai wasu suka fara ihu suna cewa a É—aga su gani a É—aga su gani
Da gudu yakaka ta taso tare da yi wa falmata rumfa da jikin ta idanun ta kuwa tuni suka fara zubar ruwa , cewa take menene hakan ?dan Allah kuyi hakuri ku kƴale ta , ƙanwata miskiniya ce makauniya ce , ni ce da laifi , ni nace ta koma shigar maza , kowanne hukunci zaku yi mata ku min a madadin ta ,' tana faɗin hakan tana warware ɗankwalin kan ta tare da rufawa falmatan da take risgar kuka , cikin tsokar jikin ta take jin idanun jama'ar da suke zagaye da wajen , cikin ran ta tana jin wani irin rauni da bata taɓa jin irin sa ba tabbas an cuce ta an tazorta ta matuƙa an tsaraita ta a gaban jama'a
Yagana ma matsar ƙwallar tausayin falmata take ,
Madam saly kuwa wani malalacin kallo take bin su da shi ,"
Yanzu daman dan uwar ki yaks ƙarya kuke min ? Toh kuwa yau yau ɗin nan zaku bar min gida ƴan iska maƙaryata , da sauri yakaka ta matso gaban saly ta shiga rokon ta akan ta taimaka kar ta kore su domin basu da kowa ,"
Da ƙyar da jibin goshi larki da hema suka sanya baki wurin taya yakaka bawa madam saly hakuri saboda tausayin yaran da ya tsirga musu , bayan sun ƙora ɗan liti wanda ya zama ziga-zigi yana sake tunzura madam saly ta kori su yakaka , ya dage akan cewa turo su C.I.D aka yi wanda hakan ke ruda madam saly , sanin cewa ita ba mutum bace mai gaskiya , sanna a cewar ta kewaye take da makiya ƴan hassadar ta .