← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 228 OF 269

Sashe 228

Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abun da ya ɗan so tayar masa da hankali bai wuce rashin sanin matsayin sa ba a wajen ta ? sai dai ya yarda da kan sa shi ai Namiji ne zai iya sauya ta zuwa yadda yake so ya koyar da zuciyar ta ƙaunar sa da hakan shi zai samar da nishaɗi a zaman su tare da taimakon sassanyar zuciyar ta mai cike da tausayi da jin ƙai .

Tayar da motar sa yayi yana nufar gida cikin ran sa cike da ƙudirin zuwa Maiduguri a ƙarshen sati mai zuwa ya fara kafa gwamnatin sa tun yanzu kafin nan da ƙanƙanin lokaci da zai dauƙe ta ta dawo kusan sa .

Har zuwa lokacin da ya koma gidan ya tarar da Sofiya yadda ya bar ta , sai daÉ—uwar damuwa da tashin hankalin da yake iya gani akan koÉ—aÉ—É—iyar fuskar ta

Kamar wacce take jiran sa yana zama ta zo ta zauna a ƙafafun sa tana kaɗa ido tace " Doctor na har ka dawo ? .

"Har na dawo Sofi ta daman ai na faÉ—a miki ba zan daÉ—e ba .

Murmushi tayi tana raɓa kan ta a kafadar sa ta cigaba da cewa " Doctor na bayan fitar ka na yi mana wani tunani , akan yarinyar nan ƙanwar mu Yakaka take ko wa ? 

Bata tsaya ba ta cigaba da cewa " me zai hana ta dawo nan gidan ta zauna a ɗakin nan na 'yan aiki kafin a samu wajen da za'a wurga ta tunda kaga fa irin halin ta na cuɗanya da maza ta riga ta saba da 'yan taɓe-taɓe da tsotse-tsotse da kwakule.....

" kin ga bana son shirita ki faÉ—a min magana kai tsaye kawai .

Ya furta hakan a taƙaice fuskar sa na bayyana wani yanayi na daban saɓanin wanda ya shigo da shi '

Ajiyar zuciya tayi shirin da suka haɗa ita da Samy baby yana mata yawo a zuci , sannan makirar zuciyar ta na cigaba da mata huɗhuba tace " ina nufin tunda Yarinyar nan kowa dai ya riga yasan irin rayuwar da take yi kafin a laƙaba maka auren ta dan haka na ga gara ka dawo da ita nan kana lura da ita dan saboda kar ta cigaba da yin ''yan harkokin ta tunda dai mai hali bai fasawa daga haka kuma ta kwaso mana ƙajaga ta shafa mana ko kuwa a maƙalo  baragurbin ƙwai a liƙa maka ya ƙyanƙyashe ya zamar mana bala'i a doron ƙasa ko me ka gani Doctor na ?

Shiru ta ji bayan gama bayanin ta , sai ta É—ago kanta a hankali ta É—aura ganin ta kan fuskar sa .

Yanayin da ta hango akan fuskar sa ya tsinka mata zuciya ta ɗan yi yaƙe sanan ta ce "Docto....

Da hannu ya dakatar da ita wani irin murmushi yake da ya mata wuyar fassara yace , " Sofi kin yi tunani mai kyau , wanda na riga ki yin makamancin sa .
. Ya É—an yi shiru yana kallon yadda faffaÉ—an murmushi ya cinye fiye da rabin fuskar ta , ya cigaba da cewa

" Fitar da nayi a ɗazu gidan da tayi rayuwa tsawon shekarun da tayi bata gida nan naje , kuma Alhamdulillah Amina ta samu shaida saɓanin wanda ni da ke da wasu tsirarun mutane wataƙila ka iya hasashe , Amina ba rayuwar banza tayi ba , asalima yaudarar ta aka yi aka taho da ita Abuja .

" babu wata hujja ɗaya da zata sa a cigaba da yi mata kallon wacce tayi yawon banza, da ya wuce mummunar ƙaddarar da ta faɗa mata da kuma Allah ya iyakance mata shi , dan haka ina so daga yau ke ma ki cire wannan zargin daga ran ki Wafaa nitsattsiyar mace ce wacce ta tafi neman ilmi kuma ta samu dai-dai gwargwado da fatan kin gane ?

Ya ƙarasa zancen yana kallon cikin idanun ta da suka yi wani irin mitsi-mitsi tana kallon sa , bai jira amsar ta ba ya cigaba da cewa
"Amma duk da haka na karɓi shawarar da kika kawo na dawo da ita kusa da mu dan haka ina ga ranar juma'ah zan tafi Maidugurin sai kawai mu zo tare amma ba a ɗakin 'yan aiki zata zauna ba ɗakin 'yan aiki na 'yan aiki ne ita kuma Mata ta ce dan haka zata zauna a ɗakina kafin na samu gida nan kusa da .....

Zuruf! Sofi ta miƙe daga kan ƙafafun sa jikinta har mazari yake ta fara cewa.

" wallahi Hamza baka isa ba , baka isa ka mayar da ni wata wacce bata san kanta ba , dan ka je an faɗa maka ƙarya da gaskiya shine zaka hau kai ka zauna ba bincike ba kome ni nan na san har gidan da tayi rayuwa a ciki tana sheƙe ayar ta a 'yan iskan samarin garin Abuja kaf ɗaya-ɗaya ne basu kwana da ita ba dan haka wallahi ba zan yadda ina zaman-zamana a kwaso min ciwo a yarɓa min ba sai dai ka zaɓa wallahi ko ni ko ita .

Da sauri ta juya har tana tuntuɓe kome yana shirin kwaɓe mata dole ta yi yunƙurin ɗaukar mataki mafi tsauri da zai kawo mata ƙarshen kome

****

Mutanen Maraɗi sun juya tare da Falmata da Hajja a ƙarƙaahin rakiyar Amnee da zainab  wadanda kwana biyu kawai zasu yi su wuce Chad Amnee zata je yiwa dangin su na can gaisuwar bangajiyar biki tare da godiyar hidindimun da suka yi musu..

Sun samu tarɓa mai kyau daya shafi wajen kwana tare da cimaka masu kyau da kuma tarin girmamawa daga bayu da hadiman gidan sarauta.

Daga Hajiya Umma kuwa babu yabo ba fallasa tun zuwan su sau uku kaÉ—ai ta zauna da su waje É—aya. Ranar farkon zuwan su da kuma washegarin zuwan su da suka je gaishe da Maimartaba sai kuma yau da suke yi mata Bankwana

nan ma kadaran-kadahan suka gaisa Amnee ta É—anka mata amanar Falmata , tana sake jaddawa akan a yi kiwon ta saboda yarintar ta kada a bar ta da kankin kanta .

Amsar da Hajiya Umma ta bayar ya sanyayawa Amnee jiki domin kuwa cewa tayi " ÆŠa ai na kouwa ne itta kouwa É—abi'a ta mai itta ce hali kuma shi ke samar da gurbi .

" Babu Shakka.

Amnee ta amsa mata .

Tafiyar su ta karya zuciyar Falmata yadda bata zata ba , ta dunga kuka tana hangowa kanta rayuwar da zata yi a cikin wannan makeken gidan alhalin shi wanda take zaune domin sa bai ma san da zuwan nata ba.

Tun bayan tafiyar su sai Falmata ta zama shiru koyaushe tana cikin babban É—akin da aka mallaka musu ita da Hajja , wanda yake cikin falo na farko a shiyar , abunda ke fitar da ita gaishe da Hajiya Umma da suke zuwa yi kullum safe ita da Hajja daga sun dawo bata kuma fita sai kuma wata safiyar ,

Bayi biyu da aka ware mata su ke hidimar abincin ta tare da kula da tsaftar É—akin da take , babu abunda take daga zama sai kwanciya , baki É—ayan rayuwar bata mata daÉ—i ga zaton ta idan sun iso zata samu ko da damar da zata dunga yin waya da Biyamuradi Youssouf sai ta tarar da rayuwar masarautar ba yadda ta saba ba , kowa a cikin gidan bisa umarnin na sama da shi yake aiwatar da lamura .

Duk yadda Siyama da Aicha suka so su dunga jaan ta fira zuwa falo taƙi yarda ,dan haka suka ƙyale ta lokaci-lokaci Siyama kan shiga ɗakin su gaisa sannan su ɗan taɓa hira saboda gidan sarauta suke kome kake idanu na kan ka zai iya zama abun magana ko ma gorantawa ace kullum ita ke zaryar shiga wajen Falmata a matsayin ta na kishiyar ta .

ita kuwa Aicha daman bata cika zaman gidan ba saboda tana shirin kammala karatun ta , dan haka Falmata kaÉ—aici ya mata yawa .

har gara Hajja da daman ita bata É—au zaman É—akin ba ficewar ta take can shiyar Bayin gidan su sha hirar su duk da cewa ba wai aiki take yi ba .

Yau tun safe ta tashi da ciwon baya da ƙafafu saboda cikin kwanaki biyun abunda ke cikin ya fara mata nawi ga yawan motsi da yake yi dan haka sai ta gagara ko da zuwa gaishe da Hajiya Umma kamar yadda ta saba tayi kwance lamo tana jin yadda abunda ke cikin ta ya cure gefe ɗaya.

Hajja ita É—aya ta tafi gaishe da Hajiya Umma ita ma ba wani sakar mata fuska Gimbiyar take yi ba "ah to Hajiya Umma ce fa É—iyar Saraki matar Sarki ?

Hajja ta so ta sanar da Hajiya Umma rashin jin daÉ—in da Falmata take fama da shi a yau sai dai yadda tayi wofintar da ita ya sa ta gaza shigar da batun Falmatan, ta ga sai umarni take bayarwa ga bayu ga Alama dai wani shiri na musamman ake yi yau a gidan .

Dan haka sai Hajja ta miƙe jiki a sanyaye ƙasa-ƙasa tace "bana iya ba wannan gurfanon ya na me neman gafara ni ba lafiyar ƙafa na cika ba , a ƙare ƙalau wannan bautar mai ciwo ? ai ni ba sayo ni aka yi ba dan haka ba baiwa bace da za'a isheni da wani ƙaburi, duk na gundura da zaman gidan nan  Babban Soja Allah ya baka lafiya mu samu mu koma gidan mu inda muke a sake ba wata takura .

Bata koma É—akin ba sai ta fita can inda ta saba hira cikin bayu amma yau sai bata same su sun yi sansanin hira ba kamar yadda suka saba , sai shiga da fita kowaccen su take yi akan aiyukan su hankalin su bai kan ta.
Chapter 228 · 0% Book details