← Book details Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 120 OF 269

Sashe 120

Mafari Hargitsin Rayuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Karo na uku yakaka ta ajiye ƴar madaidaiciyar taɓaryar hannun ta da take dakan fura da ita , ta murza tafin hannun ta da suka yi ruwan hoda hoda saboda dakan da basu saba yin irin sa ba ,

   Ta ɗago fuskar ta tana yamutsa ta ,
Ummi wallahi nagaji da dakan nan É—an Allah ummi a min sassauci ki yadda na tafi ko'ina ne cikin garin nan na nemo furar nan nayi sadakar nan da ita , Allah bazan iya yin fura da hannu na ba ,

Malama maryam wacce take zaune daga gefe akan kujerar tsakar gida tana karatun littafin Al'mauduat Al'kubra , ta É—an janye littafin daga fuskar ta

   Fuskar ta babu alamun wasa ta ce ,
   Sai fa kin daka furar nan yakaka kiyi sadaka da abunda kika sha wahala wajen samun sa yafi ɗaukaka darajar sadakar ki a wajen ubangiji , tsawon shekaru biyar kina faɗi tashin neman ilmin nan , a yanzu kin samu kin kai wata gaɓa me kauri ashe baza ki iya dakan fura kaɗai kiyi sadaka domin nuna godiya ga ubangijin ki ba ??

Jikin yakaka a sanyaye ta amsa
   Zan iya ummi ,
To maza kiyi sauri ki gama dan shabiyu ta kusa , kar har  a sauƙo daga juma'ah baki gama ba kin ga kamata yayi a ce ki rabar da ita ga mabaratan da suke bakin masallacin juma'ar unguwar nan kin ji ko ?
  To ummi tace tana saɓar taɓaryar ta fara daka ,
   Lubna wacce take zaune a gefe kusa da ita kan ƴar darduma tana yankar ƙumba , ta ɗago kan ta fuskar ta da murmushi ta sanya hannu cikin faffaɗan kwanon silver da aka ajiye guntun dafaffiyar furar da ba'a kai ga daka ta ba , ta gutsuro wata ƙatuwa ta sake jefawa cikin turmin da yakaka ke daka ,

   Yauwa ƴar ummi yi maza ki daka,  na ɗebo madara na fara damu ni ce ta farkon sanya Albarka a result ɗin nan kin sani ko ?

   Ummi kina ganin ta fa ? Tana ƙara min wata bayan na kusa gama dakan

  Lubna maza ajiye nails clipper nan ki karɓi dakan nan ki taya ta ,
   Ta furta hakan tana gyara zama gilashin idanun tana cigaba da karatun ta .

  Ummiii , dan Allah ni lokacin da nayi nawa dakan futar gama makarantar ta taya ni Haba ummi dan Allah, 

  Wallahi na taya ki kin manta ranar ....

   Yanzu aikin samun ladan kuke yiwa haka ?
   To shikenan duk ku bari ni zan zo na ƙarba nayi tunda da alamu ku lada yayi muku yawan da ya sa har kuka fara gudun sa ,

  Da sauri lubna ta zaburo tana ƙoƙarin karɓe taɓaryar hannun yakaka ita kuma yakakar ta riƙe gam ta hana ta ,

  Dan Allah ki bar ni na taya ki kin ji sahiba ta.
    Tare da marairaice murya

  Naƙi ɗin  , nima zan daka kaya na duk na mulmula na ɗau abuna a kai naje na rabar , kin ji sahiba ta .

Wayar lubna da ta É—au kiÉ—a ita ta raba musu gardama

   Cikin sauri lubna ta ɗau wayar ta ta yi hanyar falo tana satar kallon ummi wacce bata nuna alamun ta san duk abunda suke a wajen ,

  Yakaka ta bi bayan ta da kallo tana murmushi

Ta kai gaf da shiga falon ta É—aga murya tana cewa ,

   A gaishe min da yayan namu da kyau da kyau kin ji sahiba ta ?

Da gudu lubna ta ƙarasa shigewa falon tana dariyar jin kunyar ummi .

Ƙarfe biyu dai-dai da idar da sallar juma'a yakaka da lubna sun kammala ɗaura fura guda uku uku a cikin farar leda tare da kindirmo me ɗan dama shima a ƙulle a leda daban , suka haɗa su suka zuba a ƴar bakar leda daban daban , ba laifi dayawa ,

Yakaka ta jaa hijabinta saka lokacin da ta gama saka socks ɗin ta a kafa ta zura hijabin tana kallon lubna wacce take ƙoƙarin ɗaura niƙaf ɗin ta ,
   Sahiba dan Allah muyi sauri kar mabuƙata su watse ,
    Taku biyu tayi ta ɗauko niƙab ɗin ta ruwan madara , mahaɗin hijabin ta ta  fara ƙoƙarin ɗaurawa a fuskar ta ,

Da sauri lubna ta riƙe niƙaf ɗin ,
  Haba sahiba ta ? Ina mun yi cewa kin daina saka niƙab ɗin nan haka sai bayan kin yi aure ??

Hararar ta tayi
   Shiyasa na ga ai kema yanzu da za ki fita babu naƙib ɗin a fuskar ki , ni dan Allah sakar min mahaɗin kwalliya ta , cikamakon martaba ta ,na sanya abuna ,

   Amma ai ni kin san dai an riga an sanya rana , babu sauran wani ɗa namiji da zai sake cewa yana so na na kula shi ,

   Ok to maza yi min gorin aure sahiba ,
   Ta furta hakan muryar ta babu alamun wasa .

  A hankali ta sakar mata niƙab ɗin , Allah ya baki haƙuri sahiba ba manufata ba kenan .  Mu tafi .

Yakaka wacce bata furta zancen da wata manufa ta daban ba daga cikin ran ta sai domin ta samu lubna ta sakar mata niƙab ɗin ta da take neman ƙarfi da yaji ta hana ta sawa a cewar ta shi yake hana samari kula yakakar tunda ba ganin fuskar ta suke ba , duk sai ta ji ta ba daɗi da ta ga kamar zancen ta ya sa aminiyar ta a damuwa .

Tafe suke akan hanyar su ta dawowa daga rabar da furar suna tafe suna hirar su hankali kwance irin ta shaƙiƙan ƙawayen da halin su da ra'ayoyin su suka zo ɗaya suke kuma ƙaunar juna domin Allah ,

Motar da take tahowa daga bayan su sannu a hankali saboda ruwan sama  da ya kwanta bisa kan kwaltar , wacce ta fito daga layin gidan su yakaka ,ita ce ta matsa musu hon ,

Su biyun suka haÉ—a ido , yakaka ta janye hannun lubna , da nufin ko Suna bisa hanya ne sun matsa daga hanyar ,

Maza biyu ne a cikin motar wanda kallo guda za'a musu a gane cewa ba ƙananun samari bane , mazaje ne waɗanda suke kan ganiyar shekarun su na 40 cif , wayewa tare da gogewar da ta bayyana kan ta a jikin su ita take nuni da tarin ilmin da yake jibge a ƙwanyar su , ɗaya yana mazaunin direba yayin da ɗayan yake daga gefen sa ,

Na gefen ya kai hannu a karo na biyu da nufin sake danna hon , na gefen nasa ya tare hannun nasa ,

  Suleiman meye hakan kake kuma ?
Yace yana kai kallon sa gare shi ,

   Dan Allah abokina yi parking ka bani mintuna biyu zan fita ,

  Bai ce masa ƙala ba saboda yanayin sa da bai tare da nishaɗi ya sa baya buƙatar doguwar magana , ya gangara daga gefe ya tsayar da motar ,

Da sauri suleiman ya fice daga motar ,

A hankali yayi musu sallama cikin nutsuwar da take halittar sa tun ƙuruciya ,

Tana jin muryar sa ta gane shi , shine dai maƙalemata manne matan da ya liƙe mata tsawon shekaru uku yana bibiyar ta ba tare da ta taɓa saurarar sa ba ,

Matsa hannun lubna da yake cikin nata tayi , ta mata alama da kar ta kula sa , sai dai irin nutsuwa tare da kamala da ƙwarjini na musamman da lubna ta hango a gare shi ya sa ta fahimci ba irin sa ne mazan da mata ke gwatsalewa ba dan haka taƙi amfani da umarnin yakaka ta ja ta tsaya tare da amsa sallamar sa 

Baiwar Allah naji daɗi da ki ka tsaya kika amsa sallama ta domin nasan da ta ƙawar ki ce baza ku tsaya ba , dan kuwa tsawon shekaru kusan uku kenan ina bibiyar ta amma bata taɓa tsayawa ta saurare ni ba,

  Da sauri lubna ta kai kallon ta ga yakaka wacce ta yi gaba kaɗan ta tsaya tare da ɗauke kai daga barin kallon su .

Dan Allah kayi hakuri,

tace da shi , girman sa na sake cika mata idanu

Babu kome duba da cewa a yanzu bisa titi muke ba darajar mu bace yin magana anan dan haka ki sanar da ni adireshin da zan same ki ko kuma number ta wayar ki saboda ina son yin magana da ke game da ƙawar ki idan kin bani dama ,

Da sauri lubna ta ba shi number wayar ta , tana jin farin ciki na ratsa ta , a karon farko yau wani namiji ya nuna yana da ra'ayi akan yakaka , namijin ma gangariya irin wannan ai kuwa yau ummi na da farin labari .

Bayan ya karɓi number yayi mata sallama ya juya wajen motar su , da ƴar dariya a fuskar sa ya dubi abokin sa da hankalin sa ke gefe guda da alama yayi zurfi cikin tunani .

Abokina ka taya ni murna ga alamu na sanya ƙafa a kasancewa mijin mata biyu , ramla ta kusan samun abokiyar zama , tsawon shekara uku da nake bin yarinyar nan tana yin biris da ni , sai yau nayi sa'ar haɗuwa da ƙawar ta ga alamu ita zata min tsani na samun ta , 

na rasa me yake fusgata akan ta alhalin sau biyu kawai na taɓa ganin fuskar ta ,

Da alama akwai rabo ne a tsakanin mu me ƙarfi ,

A hankali ya tada motar ba tare da ya bada muhimmanci a zancen nasa ba ,

To ai sai ka ɗau harama , takaicin matan duniya ne bai ishe ka ba , ko kuwa ma nace har yau baka san wacece mace ba da irin tarin abubuwan ƙi da yake tare da ita da ace ka sani da baza ka yi sha'awar ajiye su har su biyu kamar kayan ado a gidan ka ba ,

Wuce su suka yi a hankali ,
Chapter 120 · 0% Book details